← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 94

Sashe 57

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 2 min read

yi ?"tayi shiru tana kallon yadda ya wani canza ya bar cin abincin da yake cikin tsananin 'bacin rai yake kallonta "me zaki je kiyi gurin muatne da suka zabi farincikin kansu akan naki?"ko kin manta sunce tunda kin zabi mahaifinmu babu su babu ke kuma karki koma inda suke ?""duk da haka habib zuciyata tana tsananin kewarsu zanje na gansu na nemi yafiyarsu." ya tashi daga inda yake ya dawo kusa daita ya zauna yana cewa "ai baki masu laifin komai ba!" "nayi habib!"ta fad'a a d'an fusace tana dubansa "nayi masu laifi domin na zabi hussein akansu wanda nake jin a shekarun da suka zo suka wuce kuskure nayi domin iyaye sun wuce komai sai dai qaddara tasa kayi masu ba daidai ba na sha misalta haka akaina ace maryama ko daya da cikinku yayi min haka ya zanji ?"ko kai zaka iya zabar wata kayi rayuwa daita na tsawon shekaru ka barni ?"tayi masa tamabayar tana zubar da hawaye." Ya kamo hannunta cikin nashi "ki daina misalta haka domin bazan ta'ba yi miki haka ba "to yarda na yiwa iyayena laifi mai girma kuma na cutar dasu na tsawon shekaru, baza kasan na masu cuta mai girma ba sai kasan yadda suke tsananin sona .ta k'arasa maganar kwalla na sak cika idanunta numfashi habib ya sauke kawai yana cigaba da kallonta,ita kad'ai ke bashi tausayi amman shi babu ruwansa da wasu iyayenta mutanen da suka ki mahaifinsa me zai yi dasu tunda ta zabi zuwa bazai hanata ba amman shi har abada bazai taka zuwa inda suke ba "zaka muje tare?"yaji tamabayar on expecting kai tsaye ya girgiza mata kai alamun baza shi ba shiru tayi tana kallonsa saboda tasan dalilinsa nakin zuwa shiyasa tsawon shekaru taki fad'a masu komai akan rayuwarta sai da maryama ta matsa Wanda hakan ne ya zama sanadiyyar da habib ya zafafa kishinsa akan mahaifinsa ."mikewa yayi ya koma ya cigaba da cin abinda a natse ita kuwa shiru tayi tana kallonsa dan zata so suje tare sai dai bazata masa dole dan ita kanta bata san abinda zata tarar ba ." Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 57 · 0% Book details