Sashe 16
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da maryama zata haifa min "yayi maganar da mur mushi akan fuskarsa,itama tayi murmushi kawai ba wai dan taji dadin maganarsa ba "ai an gama haifata mata jikar da zata so domin bazata ta'ba son maryama ba bare har taso abinda zata haifa masa ." Har yanzu da yake gabanta zuciyarsa cike take tarin damuwa dan bai daina hango damuwa atare da mahaifiyarsa ba, fahimtarsa ta dai barshi yaje yayi aurensa amamn batun son maryama kwata kwata bai ga alamun haka a atattare daita ."adamcy bai bar mami ta huta ba sai daya tabbatar da ta kira baba babba tace suje masa Neman auren maryma, baba babba yace zuwa yaushe kenan ?tace "yau muna litini kuje ranar laraba ,idan yaso banda wannan lahadi lahadi ta sama sai a d'aura auren ,taki bin raayi adamcy dan shi adamcy cewa yayi a aura a wannan lahadin koda yaji abinda tace aransa yace tun dai kin amince Allah ya kai mu" baba babba yace mata "to Allah yasa alkhairi ya kai mu ranar tace "ameen ! atakaice ranta baya mata dadi da auren .adamcy ya mike ya nufi d'akinsa ya zauna shiru tare da kiran layin umma dan aganinsa ita yafi dacewa ya sanarwa ba maryama ba Kira d'aya ana biyu ta d'auka bayan sun gaisa ya sheida mata yanauwnasa zasu zo ranar laraba kuma in sha allahu lahadi ta sama za'a d'aura aure Allah sarki umma nan take ta fad'ada fuskarta da murmushi tana cewa "Allah ya kai mu lokaci Allah kuma yasa albarka Allah ya bamu ikon gani da ranmu da lafiyarmu yace "Ameen ya zarce da cewa umma maryama na kusa ne ?"aa d'azu nan taje gidansu subai'a amman nasan tana kan hanyar dawowa "okay to dan Allah umma Ina neman wata alfarma a wajenki ?tace "kayi maganar adamu !"sai daya sauke numfashi sannan yace "dan Allah karki fad'awa marayma batun zuwan yan'uwana har sai a gama komai "to shikenan an gama to ko wani abu take maka na rashin d'aa ?"yace "no no !! ai yarinyar kirki ce maryama" akwai dai maganar da nake son muyi dake ne kafin tasan komai "umma tai murmushi tace "shikenan sai kazo sukai sallama dashi yayinda fuskar umma ta kasa boye tsantsar farinciki da take ciki ta mike ta fito ta nufi bangaren aunty ." Mmn sudais MAR'ADAMS BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 6 A zaune umma ta iske aunty tana kulla alawar sha ka la'be acikin farar leda ,kallo d'aya aunty tayiwa umma ta fahimci acikin farinciki take haka nan itama taji ta tsinci kanta cikin tayata har sanda umma ta zauna fuskarta cike take da annuri batare da 'bata lokaci ba umma ta shiga karo mata batun zuwan iyayen adamcy "Alhamdu lillah kawai aunty take jerowa ,kamar ta tashi ta taka rawa dan murna haka ta dinga ji saboda farinciki, ba shakka tana mai tabbatarwa kanta Maryamarta tayi kyakkyawan gamo mai d'auke da dumbin alkhairai, umma ta kasa zama waje d'aya tace "bari na shiga na sheidawa gali dan naga kamar yana gida ,daga nan zan je na sheida wa malam mustapha su tarbi bakin dashi ." aunty tai murmushi kawai tana kallon bayanta dan tuni tayi hanyar fita "Allah sarki umma babu abinda zance miki sai dai Allah yasa kiyi kyakya wan k'arshe Allah kuma ya barmu tare da sallama umma ta fad'a bangaren baba gali taci sa'ar samunsa shi kad'ai zaune tsikar gidansa yana jin labarai ."yana ganinta yaji gabansa yayi mummunar fad'uwa dan shi yanzu da ganinta da kiranta ba alkhairi bane a wajensa sai dai ya washe baki yace "aunty da kanki maimakon ki aiko akirani nazo ,sannu da zuwa aunty ga waje ki zauna ya tashi yana kokarin d'auko mata farar kujera umma tace "ka bar shi ba sai na zauna ba nazo na fad'a maka ne jibi idan Allah ya kai mu iyayen yaron nan adamu zasu zo neman auren maryama nan da sati d'aya kuma za'a d'aura aure in sha allahu ". Wani irin yanayi mai wuyar misaltuwa cike da matsanancin tashin hankali baba gali ya tsinci kanshi ciki, inda yaji kanshi yayi masa nauyi kamar an d'aura masa dutse, dishi dishi ya soma ganinta da sauri ya bud'e idanunshi sosai dan muddin yayi sakacin da suka rufe komai zai iya faruwa dashi "gali ina cikin farinciki bari na wuce dan ina son naje na sheidawa malam mustapha sai ku tarbi bakin dashi ,kai ma idan ka samu fita zuwa anjima ko gobe da safe sai kayi masa magana" tana gama fad'ar haka ta juya da sauri ta barshi nan tsaye cikin mutuwar jiki yana kallon bayanta. umma na fita aunty Salma ta fito da sauri ta tsaya a gabansa ganin baya cikin haiyacinsa yasa ta d'an ta'ba shi kadan, ya maida kallonsa gareta tun dazun data tsinci maganar yake mintsininta ,taso ta fito taji sosai "baban Aliyu auren wa za'a d'aura kuma nan da sati d'aya ?"baba gali ya kalleta a sukwane yana jin wani sabon tashin hankali na shigarsa yace "nasan kinji komai amman bari na sake fad'a miki auren maryama za'a d'aura" idanu aunty salma ta ware sosai tana jin wani irin tashin hankali tace "amman dai ba da wannan attijirin mai kudin ba?"da shi kuwa za'a d'aura"ya fad'a mata Kai tsaye gumi na tsatsafo masa nan take jikinta ya kama rawa duk sai ta kasa furta komai,babu abinda ke yawo akanta irin maganar malaminta inda yace mata ba za'a sake tada maganar ba sakamakon aikin da yayi mata a makabarta akaje akayi aikinsa yadda idan mutun ya mutu bazai tashi ba haka baza'a sake tada zance auren maryama da adam ba ". "kin dai ga abinda zai faru acikin gidan nan ko kuma kina raye ba wai kin mutu ba ?"saurin bubbuga gefen kanta tayi da hannunta tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu tace "Kai kuwa ka kwantar da hankalinka har yanzu fa da sauran lokaci tunda ba'a rigada an d'aura auren ba" "baka san wani abu ba shi aikin zai iya tasiri aranar daurin auren ace an fasa "kinga bazan sake kuskurena yarda dake ba domin yarda da nayi dake ne duk yake kokarin janyo ciwon zuciya,ka kwantar da hankalinka bafa za'ayi auren nan ba "dan bakisan me nake ji ba a yanzu haka "bari ina zuwa amman wannan auren kam tabbas baza'a d'aura shi ba sai dai bayan raina sakina da tun fara maganarsu ta fito ta girgiza kai tace "wallahi mama da kin daina wahalar da kanki akan maryama shin dole ne sai mun taka matsayi d'aya daita ?"hannayemu kad'ai sun ishemu misali ,wallahi idan Allah yaga dama sai ya barmu muddin rai babu aure ba ita kuma tayi aurenta kuma ta dangwama cikin jin dadi ." aunty Salma ta juyo a gigice tana dubanta tace idan kika sake fad'a min haka sai na tsine miki "Dan ku fa nake wannna wahalar ko da yake ba laifinki ba aikin dake jikinki ne yake son lalacewa shine kike son ki dawo gidan jiya amman zanyi magani ki "karki sake d'aure min yara "inji cewar baba gali ,aunty salma ta d'auke idanunta akna sakina ta maida kanshi "eh haka na fad'a duk kin birkita min tunanin yara da shegen biye biyen malamanki na banza da wofi "aunty salma bata sake cewa komai ta shiga d'aki ta zari mayafi ta bar gidan ." Adamcy dake zaune a parlour'nsa bayan ya gama waya da umma shiru yayi ,wani irin sanyin dadi ke ratsa ilahirin jikinsa,yanzu hankalinsa ya kanta maryam ba zata dawo rayuwarsa ba ga maryamarsa zai mallaka ,tsadadden murmushin nan nasa ya bayyana akan fuskarsa yana cewa "maryama kin kusa zama tawa ta har abada Allah yasa karki min rowar kanki dan ina tsananin bukatar ki "ya fad'a a fili yana kamo lip's dinsa na k'asa yana cizawa ahankali yana jin nishad'i mara misaltuwa wayarsa dake ajiye a gefensa ta fara ringing ya d'an waigo a natse yana kallon screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya d'aga yana "cewa "hello baba!".daga can bangaren baba babban yace "adam ya kake ?"Alhamdulillah baba barka da yamma ?"barka d'an mamansa ". wani murmushi ya bayyana akan fuskarsa sakamakon jin abinda baba babba ya fad'a " Naji dadi kwarai daka natsu ka shawo hankalin mahaifiyarka akan maganar aurenka ,ya kamata zuwa yanzu ka canza rayuwar da kakeyi. rayuwar da zakayi yanzu ta samu canji kabi mahaifiyarka ku rabu lafiya domin daga lokacin dakayi rakiya aka binneta daga wannan lokacin rayuwarka ta baya data yanzu ta samu canjin zahiri bazan boye maka ba daga wannan lokacin zaka shiga sabuwar rayuwar zaka zamo baka da karfi komai ." "Kuma komai zai iya faruwa da Kai bare Kai da kake tsananin son mahaifiyarka karka d'auka wasa duk wanda ya rasa mahaifiya to fa ya zama abun tausayi ,domin kuwa ya rasa halittar da take son taga rayuwarsa ta samu cigaba kuma ya rasa wacce zata dinga masa adduoin nasara a duk inda take a zaune ko kwance cikin sallah akoda yaushe,dan haka ina shawartarka kabi mahaifi yarka sosai kayi mata duk abinda kasan zatai farinciki Ina maka fatan alkhairi arayuwarka ". "na gode sosai baba in sha allahu zan cigaba akan yadda nake mata ."masha Allah daman Ina son naji a wani estate ko wani guri zamu had'u da iyayen yarinyar dan na kira Zulai tace bata sani ba shine nace bari na kiraka naji dan mu san yadda zamu tsara tafiyar a jibi "?shiru yayi yana tunanin mai zai ce masa Allah yasani shiyasa yaso tuntuni su maryama sun tare a gidan daya basu ba dan komai sai dan samun wata daraja da kima a idanun yanuwansa amman dai zaije suyi magana da umma gobe "adam kana kan layi kuwa ?"numfashi ya sauke ahankali sannan ya soma masa magana a natse "ka bani zuwa gobe zanyi magana da iyayen yarinyar naji a ina zaku had'u baba babba yace "to shikenan Allah ya kai mu goben Allah kuma yasa albarka