Sashe 38
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tunda bata yi niyyar gaisheni ba sai da kasata ". Maryama na jin haka ta sunkuyar da kanta kasa ta had'e hannuwanta waje d'aya ta tsarke dan bakaramin taimako hakan zai mata ba a zaune da take ,adamcy ya kai d'ayan hannunsa ya shafa goshinsa na second d'aya sannan ya maida hankalinsa ga mami "sweetheart wannan yarinyar fa matsoraciya ce , ki kalleta da kyau a tsorace take ,hajiya zulfa'u tai murmushi har ta bud'e baki zatai mgn ta tsinkayo maganar mami inda take cewa "wa take jin tsoro a nan ko kuma wake tsoratata?"shiru yayi yana duban mami yana nazarin maganarta ganin tana son juya masa magana .yaji kamar yace mata ya'yanta ke tsoratata sai dai ya danne saboda duk abinda zai fad'a mata a yanzu bayansu zata bi ,tunda yanzu bata son gaskiya ,"anan babu wani abun tsoro sannan babu maye bare taji tsoro ita dai tasan abinda ke tsoratata karka sake zuwa min daita a firgice matukar bazata samu natsuwa ba tai zamanta bana bukatar gaisuwarta ." da sauri hajiya zulfa'u tai masa gargadi da kwayar idanunta alamar kar yace komai nan take ya runtse idanunshi gam yana danne zuciyarsa dake k'ok'arin motsawa bazai so yayi wani abu a gaban maryama ba ,dan bazai d'auki rainin mahaifiyarsa ko yan'uwansa daga gareta ba Maryama kam tashi shiga tashin hankali matuka sai dai tai ta karanto la ila a illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin wanda shi ya ba kwarin gwiwar sake d'agowa ta gaishe da yan'uwansa suka amsa mata da" lafiya !atakaice suna yatsuna fuska kamar sun ga mugun abu zabiba ce kawai ta amsa da kyau kuma ita daman tun farkon ganinta daita tasan suna da bambamci ra'ayin." "ta sake maida kanta ta sunkuyar tana jin mummunar fad'uwar gaba ."yanayin da mami tayi kwata kwata bai ma adamcy dadi ba dan sai wani faman cika take dan haka ya mike tsaye tare da karasowa inda maryama take raku'be ya miko mata hannunsa sai dai taki yarda tayi wannan gangancin, ta yunkura jikinta a sanyaye zuciyarta na wani irin rawa dan itama Allah Allah take ta bar parlour'n idan ma da hali har gidan bata son zama acikinsa". tun kafin yayi gaba ya barta ta nufi kofar fita daga parlour'n ya biyo bayanta a natse suna fita babban parlour'n ya riko laulausan tafin hannun ta cikin nashi yana Jin yadda jikinta yake rawa suka haye sama a parlour'nsa ya tsaya ya janyota zuwa faffad'an k'irjinsa ya manneta tare da zagaye kungunta tana k'okarin zare jikinta ya sake rike kugunta da kyau ya d'aura kanshi a gefen wuyanta "ki rage wannan tsoron idan ba haka ba zai cutar damu." aranta tace "ka barni da tsorona idan ma kasheni zai yi ya kasheni dan muddin Ina cikin gidan nan tare da mahaifiyarka da yan'uwanka zuciyata bazata rabu da tsoroba ." bedroom dinsa ya shige daita yana zare after dres din jikinta dama kayan jikinta ya fara wasa da sansar jikinta ita kam ta yiwa kanta alkawari ko babu sharadin yan'uwansa akanta bazata yarda ta mallaka masa jikinta ba tunda mahai fiyarsa bata sonta bata kaunar ta."acan parlour'n mami kuwa sosai hajiya zulfa'u ta rufe su aunty khadija da fad'a "gaskiya ban ji dadin tarbar da kuka wa yarinyar nan ba ,menene laifinta ?"bafa ita tace ya aureta dole ba shine yayi ra'ayi sannan kusani fa shi fa d'anuwanku ne ita kuma wacce kuke taya kishin cousins ce kuma da ta samu dama a wajensa da zaku ga sa'banin tunaninku ita dai mami bata ce uffan ba dan bata ga laifin da sukai ba ,ta gaishesu kuma sun amsa ai shikenan ." Bangaren adamcy kuwa ahankali ya dinga rud'a jikin maryama da zazzafan romance wani fellings of excitement with love ne ya dinga shiga jikinta ta runtse idanunta gam tana amsar sakoninsa da kyar ta fixgo magana tace "yallabai bacci !"bakinsa ya kai cikin kunneta yayi mata magana cikin rada "kina jin bacci ne ?"ta gyad'a masa kai alamun "eh!"okay kiyi bacci "numfashi ta fixgo da karfi ta sauke dan tasan bazata iya ba idan tana jin tafin hannunsa ajikinta , harshensa ya zira cikin kunnenta ya fara tsotsa cikin wani irin murya tace "wayyo Allah dan Allah ka cire ganin yaki aiki tasa masa kukan shagwaba dole ya bari sai dai bai zareta ajikinsa ba ya rungumeta kawai tunda taji ya bari ta runtse idanunta bata sak budewa ba har bacci ya d'auketa ." ganin haka ya zareta ajikinsa ya janyo wayarsa ya soma neman layin bright yaji dalilin kiran sai dai yaji computer na cewa the number you've calling is switch off ya ajiye wayar ya d'auki nata ya shiga inbox bai ga komai ba , mikewa yayi ya fice daga d'akin ". maryama ta dade tana bacci kafin ta tashi sai dai tayi mamakin ganinta ita kad'ai bata san lokacin da adamcy ya fice ba saukowa tayi daga kan gadon tana duba wayarta karfe uku saura ta shiga bayi ta watsa ruwa ajikinta tai alwala ta fito tana tsaka da goge jikinta taji ana knocking dan hk ta janyo hijab ta zira da sauri ta fito zuwa parlour'n ta bada umarnin shigowa mai aiki ce ta turo kofar ta shigo hannunta rike da tray dake d'auke da manya kuloli ta gaishe daita cike da sakin fuska maryama ta amsa tana kokarin amsar tray hannunta tabawa tace "a'a ranki ya dade ki bar shi !ta fad'a tana k'arasa wa inda zata ajiye tray maryama tai murmushi tace "sannu da kokari na fa gode !"da mamaki tabawa take kallonta domin a gidan babu wanda ya damu da aikinka bare yayi maka sannu cike da girmamawa tace" yauwa na gode zuwana na uku kenan Allah yasa ban takura miki ba ?"maryama ta girgiza mata kai tana murmushi tace "ko d'aya bacci nake lokaci" tabawa tai mata sallama ta fice maryama ta juya ta koma d'akin domin gabatar da sallar azahar ." Bayan ta idar da sallah ta shafa mai ta sauya wasu Kayan ta fito ta bud'e kulat abinci ta farko white rice ce ta biyu kuma stew ne ta d'auki plet ta zuba taci kad'an ta soma tunanin raba d'aki da adamcy dan bazata yarda ya shammaceta ba ." A natse ta mike ta bud'e d'akin dake gefen nashi ta shiga shima kamar nashi ne da gado da wardrobe da komai da sauri ta fito ta koma d'akinsa ta soma janyo akwatunanta d'aya bayan d'aya ta dawo dasu d'akin ta shirya kayanta bayan ta gama ta d'auki wayarta ta kira umma bayan sun gaisa take sake tambayarta bakunta ."tace "umma akwaita fa har da tsoro umma tai murmushi tana cewa "Allah dai ya yaye miki wannan tsoron kinje kin gaishe da mahaifintarsa kuwa ?"naje umma !"ta fad'a jikinta a sanyaye." Umma tace " kiyi hakuri maryama da duk abinda zaki gani ki taya adamu biyayya ga mahaifiyarsa zuwa anjima kad'an ki sake zuwa ki gaisheta ki dinga zuwa safe da yamma duk mugun halin mutun Allah zai taimakeka akanshi kinji karki wani damu da duk abinda zata miki tunda Allah ya rigada ya had'a wata rana zatai hakuri ta rungumeki amatsayin suruka mafi soyuwa a zuciyarta ,ni adduata Allah yasa ki samu ciki da wuri "Kai umma daga aure sai wani ciki ?" "to me ake jira maryama ai haihuwar ce zata sa ta sauko da wuri ta kauna ce ki sun jima suna hira kafin daga bisani sukai sallama ta kira layin aunty suka gaisa itama sun jima suna hira daita har hud'u saura sukai sallama ta mike ta gabatar da laasar dake akwai alwala ajikinta ."bayan ta idar ta fito a natse, tarba mai kyau ta samu daga hajiya zulfa'u cike da girmamawa ta gaishe da mami ta amsa fuska babu tabo babu fallasa ta zauna shiru yayinda suka cigaba da hirarsu ita dai zaune take bata fahimtar maganganunsu saboda hankalinta ya rabu gida biyu, wajensu mami da kuma wasu yara uku da bazasu wuce shera uku da shekara bakwai da kuma shekara biyar ba .masha Allah yaran kyawawa sunyi mata ga wayo hajiya zulfa'u ta juyo zata mata magana sai ta lura da hankalinta gabad'aya yana kan su Amir da mashkur ne ta zuba masu idanu tana murmushi ita dai yarinyar tana burgeta ta d'auke kanta alokcin da adamcy ya shigo hankalinsa a d'an tashe, shima shagala yay a kallon yaran sai faman zuba murmushi take ,da alamun yaran sun tafi da imaninta, naunauyen ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata irin wadatacciyar natsuwa dan lokacin daya hau sama bai ganta ba sannan bai ga kayanta ba ya shiga damuwa waje ya fita yana tambayr masu tsaron kofar shiga gidan mami suka tabbatar masa da tana ciki shima murmusawa yayi yana lasar lips dinsa na kasa kafin ya d'auke kansa ya maida ga mami da suke magana da hajiya zulfa'u." Zuwa can fad'a ya kaure tsakanin yaran d'an shekara biyar din ya fixge jirgin wasan daga hannun mashkur yazo wajen maryama ganin tun d'azu hankalinta na kansu yana tambayarta "aunty see mashkur remove the flight board shima mashkur ya karaso yana huci ya nuna mata game dinsa da amir ya buga da kasa duk da maganar yaron farko bata fito sosai ba amman maryama sarai ta fahimcesa dan haka sai tayi murmushi ta kamosu gabad'aya ta zaunar dasu akan cinyarta tana sake murmusawa, duk abinda ke faruwa akan idanun adamcy da turanci maryama tace " kai gsky mashkur baka kyauta ba amman kayi hakuri kaji murmushi ya mata shima, yace "aunty mashkur mugu ne kullum sai ya bata min kayan wasa "yi hakuri ka daina ce masa mugu ba yayanka bane ?"da sauri ya girgiza mata Kai alamun a'a tace "da gaske?"maryama ta fad'a tana dafa kafad'arsa kansa ya d'aga mata kai mahukr yace "nima ya buga game dina da kasa bazan yarda ba! shima hakuri ta bashi Aunty na koya miki game ?"ta gyad'a masa Kai Amir yayi sauri yace "aa ni ne zan koya miki yadda ake wasa da jingina ko ?" maryama ta d'aga masa kai alamun "eh !tana jin wani farinciki yana shigarta duk suka d'aura mata akan cinyarta alokcin iyayensu dake cikin d'aki suka fito suna kallonsu gabad'aya yaran sun zagayeta tana tambayr sunan mace Amir tace ."rayhana " Murya aunty