← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 94

Sashe 29

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

haka protein yana da nashi amafani nifa bazaki yi rayuwa tare dani da yunwa ba dole kici abinci enough kuma sau uku arana "ta yatsuna face dinta kamar zatayi masa kuka "my princess you must eat well kalli yadda mararki ta shafe ."? "to ai Ina cin abinci sai dai ba koda yaushe ba tayi maganar tana shagwabe masa fuska alamun zatayi kuka "kina son ki kasa d'aukarta ciki da wuri ne "? "me kuma ya kawo wannan maganar ?"ta fad'a tana had'e fuska a dole karya kawo mata maganar lumshe idanunta tayi tace "wai dan Allah kai baka jin kunya ne "?kunya for where ?" "dole fa zaayi maganar ciki tunda dole .."dan girman Allah karka k'arasa maganar ." Shiru yayi tare da kamo laulausan tafin hannunta cikin nashi yana murzawa hannunta da jikinta tamkar ba diyar talakawa ba ,yan'uwanta suka shigo dakin tai saurin zare hannunta cikin nashi dan muddin tayi sakaci to kuwa ita zai barwa abun kunya umma subai'a har ma da yusura suka dinga jero mata sannu.byn sun fita ne taji tamkar kar su fita dan bata son abarta daga ita sai shi a d'akin hakan na sake frigita zuciyarta dan zan tutt'ukansa babu sauki komai nashi dabam salon soyayyarsa mai matukar tafiyar da kuzari da ruhi ne sai data shanye tea tas sannan ya soma bata abinci kad'an taci tace "ta koshi bai wani takurata ba tunda ta sha tea sosai ya ballo magani ya mika mata, ba musu tasa hannu ta kar'ba ta sha dan tasan halinsa ciwonta ba zai hanashi matseta ya bata ba ko dagula mata lissafi ba har sai yaga ta sha dan gabadaya a tsorace take dashi ." sosai Idanunshi ke cikin nata yayinda hannunsa ke tsarke cikin nata "ki tashi daga wannnan ciwon naki domin a samu damar kawo min ke pls nan take ta had'e fuska "kinsan Allah idan na bar gidan nan kuma kikayi abinda yasa ba'a kawo min ke ba a yau ba bazaki sake ganin kafafuwana a inda kike ba "sai me ai na ma huta da takura." "tayi maganar acikin ranta k'aramin bakinta yake kallo yana son ya Karanci abinda ke ranta itama shiru tayi tana tunani bata ankara ba taji ya kamota ya sanyata ajikinsa yana shafata cikin wani yanayi na tsananin sha'awrta "ni zan wuce amman masu zuwa d'aukar ki suna zuwa ni wallahi da umma zata barni dana wuce dake an hutar da kowa kwace jikinta tayi tana masa wani kallo "sai kace wata yar kaza zaka ce zaka wuce Dani kamar bani da galihu "meye marabanku." Tai shiru tana kallon kafin ahankali tace "bani da maraba da kaza kake nufi ?"yes gabad'aya jikinta babu kwari kamar pepper Allah kina shigowa hannuna double abinci zan dinga tura miki ga abinci ga spam dan kiyi saurin .."saurin kai hannunta bakinsa tayi ta toshe tana kallon cikin kwayar idanunshi shima cikin idanunta yake kallo cike da matsanancin shaawarta kallon juna suke kamar zasu cinye juna" Ina sonki s sai bazan ta'ba son wata halitta sama dake ba."yayi maganar acikin ransa sake had'ata yayi da jikinsa yayi runguma mai kyau sannan ya zareta yana duba agogon hannunsa" nan da wasu yan mintuna zasu karaso har juya ya sake dawowa yayi kissing din foreign head dinta lumshe idanunta tayi batasan lokacin daya fice ba sai bud'e idanunta tayi taga wayam baya d'akin." a parlour'n kuwa adamcy yayi wa umma sallma yana k'ok'arin fita ta biyo bayansa tana masa magana ya tsaya cak ."adamu kana ganin bazaku dade a gidan mahaifitarka ba?"shiru yayi kawai yana kallonta "wai saboda Kayan amfanin maryama ne "umma sau nawa zamuyi mganar nan gidan da zata zauna babu abinda babu acikinsa amman tunda kuna raayi zaku iya kai wa zan turo zuwa jibi akai ku gidan sai ku Kai mata." ya fad'a haka ne saboda baya son suga ya raina matsayinsu "to shikenan hakan yayi ya sake yi mata sallama ya fice yana kiran direbansa yaji ko Sun taho "alright!"kawai ya fad'a atakaice Karfe biyar daidai umma da subai'a tare da kawayen aunty suka shirya maryama cikin wata hadadiyar atamfar super exclusive puppy toch of white and black ajiki ,dinki riga fitet da zani ne aka mata duk da tafi son dinkin doguwar riga amman dinki ya kar'bi jikinta sosai tare da lullubeta da lifaya shima fari toch of pupply sukai mata wanka da ruwan turare kala kala suka fito da ita umma tace akaita gurin aunty suyi sallama sannan idan an fito daita akaita wajen baba gali shima tai masa sallama ." Allah sarki maryama durkushewa tayi a gaban umma sai kuka ya kufce mata tana kiran umma !!"shine kawai abinda bakinta yake iya furtawa itama umma hawaye ne ya cika mata ido ta goge da sauri tana cewa "ki daina kuka kin dai san baki da lafiya Allah yasa kin shiga a sa'a Allah yayi miki albarka Allah yasa wannan gida da zaki shiga ya zamo silar samun kwanciyar hankalinki Ina miki fatan alkhairi arayuwarki aurenki tashi kinji lokaci na tafiya ta mikar da ita tsaye tana kuka umma na kuka dan zatayi kewar diyarta aka nufi bangaren aunty daita itama dai da kuka suka rabu tana sa mata albarka tare da fatan alkhairi sannan suka shiga bangaren baba gali shima dai babu yabo babu fallasa yayi mata addua da fatan alkhairi suna fito iyayen adamcy na shigowa mutun uku ne kawai suka zo d'aukarta hajiya zulfa'u da matar baba babba sai zabiba sun baro matar baba k'aramin da matar uncle jay a gidan mami da sauran jamaa batare da 'bata lokaci ba aka shedawa umma zuwansu ." inda tace subaia tayi maza ta fito da akwatin data shiryawa maryama na kayanta na sakawa guda uku mutun biyar ne ta bangaren maryama zasuyi mata rakiya umma,da kawayenta aunty guda biyu sai aunty fatima da aunty hassana sai kuma kawayenta mutun uku a natse umma ta fitar da maryama daga lungunsu tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya tuni fuskarta ta sake canzawa aka sakata motar da hajiya zulfa'u take ciki gefenta umma ce sauran mutane suka shiga mota suka bar unguwar ,cikin mintuna talatin da wani abu suka k'arasa abdullahi estate Kai tsaye bangaren mami aka nufa daita alokcin duk suna zaune a babban parlour'n har mami dan tun kafin su karaso hajiya zulfa'u tayi wa aunty shahida text message akan lallai suyi kokari mami ta zauna a parlour'n dake sun san shiru su akan maryama batare da bata lokaci ba suka bukaci mami ta dawo parlour'n tace "me zanyi bayan gasu zulfa'u dasu hajiya baseera da kyar dai suka lallabata ta fito cikin wani hadadden lace red toch of gold haka mayafin data lullube jikinta dashi da talkami duk gold ne ga wasu awarwaron zinariya a hannunta haka ma wuyanta sarkar gold ne ." kana kallonta kasa tun asalinta ba daga gidan babu ta fito ba daman kuma ga kyau ga jiki mai kyau Allah ya bata bazaka ce itace ta haifesu ba hajiya zulfa'u rike da hannun maryama bata tsaya a koina Ina ba sai a gaban mami fuskar d'auke da murmushi tace "Aunty ga surukarmu maryama ta kamo hannunta ta sanya maryama ai maryama na Jin hannunta cikin nata jikinta ya Kama rawa sai dai cike da girmamawa da ladabi maryama ta zube a gabanta kanta na sunkuye a kasa cikin tsananin jin kunya da fargaba dan har lokacin kuka take mai ban tausayi tunda mami ta rike hannunta taji komai ya sauya agareta wani irin tsanarta kawai take ji yana bin jinin jikinta cikin sakonnin da basu wuce goma ba ta saki hannunta tana kirkiro murmushin dole inda zabiba ta karaso gaban maryama ta soma k'ok'arin bud'e mata fuska cak mami ta dakatar daita ta hanyar take mata kafa ." muna sai da ingantaccen maganin mallaka sai dai baa bawa mai kishiya saboda karfinsa ga masu bukata zasu iya tuntubata ta wannan number 09136918331 ." Mmn Sudais MAR'ADAMS
Chapter 29 · 0% Book details