Sashe 70
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 3 min read
bayaninsa har ya gama ya riko hannunta suka fito tare zuwa bangaren mami koda suka shiga tana bayi tana wanka wankata kuma yana d'aukar lokaci amman haka ya zauna jiranta ,itama haka ta zauna ya riko hannunta cikin nashi yana murzawa yace "ko dai zan tafi dake ne !"kamar tace masa!eh!sai kuma ta girgiza masa Kai ." "me yasa yanzu bakya son cigaba da zane naga ko a gida bakya yi ?"zan cigaba mana hutun wata nawa aka bani domin nasan ranar komawa aiki ?""ba maganar komawarki aiki nake yi ba ai aiki kin gama dashi har abada sai dai idan ina bukata zaki min a gida"ya fad'a yana kissing din hannunta yana matseta da jikinsa tare da kai bakinsa daidai kunneta tayi saurin zame jikjnta daga nashi "yalla'ba mami fa karta fito ya sake matseta yana harararta yace"ni fitowarta nake so ai "naunauyen ajiyar zuciya ta sauke ita dai Allah ya had'ata da gamonta babu jimawa mami ta fito kafin yayi wani abu ta zame ta durkusa kasa tana gaisheta "ta d'an yi shiru tana dubansu dan ta ga yanayin da suke harara ta buga ma maryama tana nuna mata hanyar waje da hannunta ta d'an yi shiru tana dubanta duk da ta fahimci abinda take nufi .""Sweetheart kina nufi maryama ta fita?" ya tamabyeta yana had'e fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa "idan bata fita ba me zata min ?". "haba sweetheart me yasa ?"idan bata fita ba yanzu zan bar maku d'akin d'an bazan kasance tare da makiyiyata ba domin duk mutumin da yayi silar rabaka da d'anka babban makiyinka ne bakinciki ya kama maryama zuciyarta kamar ta Kama da wuta "bana son gaisuwarta bana buka tar ganinta kai ma idan bazaka zo kai kad'ai ba na yafe amman karka k'ara shigo min da wannan abar tunda bayan asiri data maka yan uwanka ma ka bata damar ta rainasu wai har wannna yarinyar shahida zata gaya ma magana saboda ta samu d'aurin gindi a wajenka taci darajata jiya da jikinta ya gaya mata dan haka iskancita ya tsaya akanka kai da ka kawota amman ni da ya'yana kul .."cike da sanyin jiki maryama tabi ta gefensa ta bar d'akin zuciyarta na zafi bai ce ma mami komai ba shima ya fice ya biyo maryama yana k'ok'arin kamota ta goce tana buge masa hannu ta shige parlour'n ya shigo yana ya sake kai mata hannu ta sak gocewa " gabad'aya ya cakumota yana cewa"ke menene haka ?"kuka ta fashe masa dashi mai tsuma zuciya tana cewa "kwanaki kawai nayi a gidan nan amman Ina Jinsa kamaar shekaru nayi acikin azaba, ni dai dan Allah ka rabani da gidan nan ko kuma ka sauwake min dan bazan iya cigaba da zama acikinsa ana ci min mutunci ana ciwa iyayena ba" ta k'arasa maganr tana kokarin kwace jikinta daga nashi amman ta kasa sakamakon rikon da yayi mata ba wanda zata iya kwacewa bane "ni me nayi wa mami ne data tsa .. ."bata kai ga k'arasa maganrta ba ya rufe mata baki da bakinsa ." Mmn sudais MAR'ADAMS