Sashe 88
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read
fuskarsa ba yayi kokarin ya danne damuwarsa yace mata suje kasa da kyar ta yunkura suka fita inda suka iske gabad'aya yaran mami zaune ban da mutun d'aya zabiba wacce kusan ta rage zuwa gidan yanzu tare suka zauna akan kujera d'aya maryama na kokarin gaishe da mami amman kiri kiri ta d'auke kanta"can kasan makoshinsa yace tashi ki d'auko min khaira ".a d'an rikice ta kallesa gabanta na fad'a uwa da matsanancin karfin gaske "ko baki ji abinda na sakaki bane?"tace uhm amm sai kuma tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta ya d'ago fuskar nan tashi a had'e tamkar an aiko masa da sakon mutuwa da sauri ta mike ta fara taku ahankali tamkar kazar da Kwai ya fashewa aciki cike da sanyi jiki ta k'arasa inda khaira take rarrafenta ta duka ahankali zata d'auketa taji sautin murya biyu ajere "karki sake ki d'aukar min ya !"aiko cak maryama ta tsaya tare da zuba masa idanu tana kallonsa jikinta na rawa shima suna gama rufe baki ya zabura ya mike tsaye yana nuna su da yatsansa."yarki ko tawa!"ya fuskanci maryam yana zaro mata ido dan bashi da lokacin aunty khadija nan take abu biyu ya had'e wa maryam waje d'aya tashin hankalin ganin yanayinsa da kuma farinciki ya furta kalmar 'ya ga khaira daga mami har aunty khadija da maryam da nana hauwa'u zuba masa idanu sukai suna kallonsa irin mugun kallon da yake ma maryam ta fahimci amsarta yake bukata dan har lokacin idanunsa na kanta." muryarta a tsarke tace"yarka ce "!okay tunda har an yarda cewar 'yata ce good ya kalli maryama dake tsaye jikinta na cigaba da bari yace "kina son khaira zaki riketa !"bata da zabin daya wuce ta amincewa hakan , dan haka ta gyda masa kai alamun zata rike "good daga yau ta bar hannun wannan har abada ta dawo hannunki dan haka ki d'auketa na baki ita kyauta kiyi duk yadda kike so daita "ai Maryam na gama Jin haka ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali "ma..mami ki taimakeni ya kyautar min da yarinya bayan duk wahalar dana sha tun kafin haihuwarta har zuwa ranar dana haifeta mami karki bari ya kyautar min da khaira "wannna maganr tasa jikin maryama yayi sanyi dan tayi imani rainon ciki kawai akwai wahala bare haihuwa tana kallonta tana kuka tana rokon mami tasa baki cikin maganar aunty khadija tace "dan Allah kiyi shiru hauka yake a ina ya ta'ba ganin an kyautar da mutun khaira yarki ce idan kuma har ya tabbatar haka walalhi sai munyi sharia dashi mara mutunci kawai da bai san ciwon Kansa ba "kece mara mutunci da bata san ciwon kanta ba ya fad'a yana kallon inda mami take zaune cike da mamakinsa yace "sweetheart kiyi hakuri dan matakin da zan d'auka yau bazai miki dadi ba ke mahaifiyatace duk abinda kika min da maryama kin ci lafiya kuma kinci banza saboda kece kika kawoni duniya ."amman kinga wad'an nan ya'yan naki wallahi bazan sak d'aga masu kafa ba ko duba wata halaka dake tsananimu ,tsakanina dasu back to back ne ya d'auke idanunshi daga kallon mami ya zuba masu "ku kuma muatanen banza zaku gane kurenku a yau ne zaku gane bani da mutunci ya ciro waya ya soma kiran commissione of police yace "police din sun karaso okay shikenan bari nasa a shigo dasu yana gama rufe bakinsa ya juya ya fita cikin tsananin tashin hankali duk suke kallon bayansa maryama kam hannunwanta ta d'ora duka saman kanta ta koma ta jingina bayanta da bango tana karanta" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta kalleta "idan nace aurenki ya zame min alkhairi nayi wa Allah karya kin shigo rayuwarmu kin ruguza komai tsakanina dake Allah ya isa ban yafe miki ba,ai dai ciki gareki ba zaki haifa kuma za ki san me nake ji akan d'ana Ina addua Allah yasa ayi miki irin abinda kika min "maryama ta dukurshe kasa tana jan gwiwowinta tare da had'e hannunta duka tana rokonta "dan girman Allah mami kiyi hakuri ki yafe min wallahi ban rabaki da d'anki ba Allah shine sheidata ." Tana kuka tana rokon mami har ma da aunty khadija tana bata hakuri adamcy ya shigo da polisawa yana nuna masu aunty khadija da nana hauwa'u da maryam,ya kalli auta afusace yana cewa "ina shahida!?bakinta na rawa tace tana d'akin mami tana sallah maza ki shiga ki kirata zan nuna maku tsantsar rashin tausayi ta nufi hanyar da sauri inda take jikin mami ya Kama rawa tana kallon adamcy wanda yaki kallonta dan kallonta zai sa ya kasa aiwatar da komai ."maryama ta ja gwiwowinta zuwa gabansa "ke kuma menene haka please get up? " ya fad'a a tsawace yana jifanta da mugun kallo da sauri ta girgiza masa kai "dan Allah ka duba halin da mami zata shiga akan matakin daka d'auka "kuma menene amfanin wannna matakin ?dan Allah ka janye kudirinka idan dai akaina ne wallahi na yafe masu duk abinda suka min "idan ke baki da hankali ni inda hankalina kuma nasan ciwonki "wai har ita wannna take yunkurin kasheki baki fad'a min ba "ya fad'a yana nuna maryam da d'an yatsansa "well da man kisan kai ba sabon abu bane a gurinta amamn idan ta gwada yi akanki ne zata sheka lahira dan da hannuna zan kasheki."Ya dawo da idanunshi ga maryama data had'a gumi tana rokonsa "ya d'an yi kasa da muryarsa "kima daina wahalar da kanki dan kema baki tsira ba bari na gama dasu zan dawo kanki ne .""Naji ka had'a duka hukuncin kayi min wallahi na yarda kuma na amince mutuncin mami da darajanta zaka duba pls d'auke kanshi yayi yana tura hannuwansa cikin aljihu yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa cikin tsananin tashin hankali auta suka fito tare da aunty shahida ta kallesa tsaye tare da polisawa sannan ta kalli mami dasu aunty khadija tace "meke faruwa !"ta tambaya ."officer's ga cikonsu nan ku tafi dasu" "what !"wallahi adamcy kayi hauka mu zakayi arresting?"bazaki san nayi hauka ba sai mun had'u a kotu cikin muryar kuka maryama ta mike tsaye ta riko hannunsa tana cigaba da rokonsa "kasan Allah muddin ka bari aka tafi dasu sai dai ka sakeni ".: a matukar zuciye taga ya d'aga hannusa sama zai sauke mata mari tai saurin runtse idanunta ko ya tuna tana d'auke da cikinsa ne ya sauke hannunsa shiru bata ji saukar mari ba ta bud'e idanunta fess akan shi gabad'aya yanayinsa ya sauya ya dawo asalin mr ata din data sani yace "bar nan kafin nayi kwallo dake!"officers nace ku wuce dasu aiko suka tasa su gaba suna k'ok'arin fita dasu aunty khadija tace "zan Kira mijina kafin a wuce damu d'aya daga cikin jami'an tsaro yace "babu dama kin kirasa idan munje move"kasan kuwa ko ni din matar waye? karku saurareta sai kunje headquarter ."adamcy ya fad'a yana jifanta da wani mugun kallo ."yana rufe bakinsa maryama ta kwasa da gudu ta hau sama biyu biyu take taka step jini yaga yana bin kafafunta da sauri ya dawo da kallonsa gefensa inda ta tsaya nan ma jini ya gani ahankali ya dinga bin jinin yana kallo cikin tsananin tashin hankali da kad'uwa ya biyo bayanta yana kiran sunanta." Mmn sudais MAR'ADAMS