← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 94

Sashe 68

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

junansu na sak mamaye zuciyarsu ji suke tamkar su had'e guri d'aya ."fad'a me kike son na mallaki?ya tambayeta yana kamo ha'barta yana kallon face dinta "ai na rigada na fad'a maka tunda ka soni a matsayin da nake ka gama min komai sukai shiru suna kallon kwayar idanun juna so take tai masa magana akan shan sigari duk da kwana biyu taga baya sha amman tana jin tsoron zai iya canzawa daga farinciki da yake ciki zuwa damuwa dan haka zata bari sai zuwa wani lokaci." ahankali ta zare jikinta tana duba agogo "yalla'ba ya kamata ka shiga wanka ka fito lokacin na tafiya kuma nasan taru takardu na can na jiranka shima agogo ya kalla sannna ya nufi hanyar bathroom yasa hannu ya bud'e sannna ya juyo tana tsaye tana kallonshi "bana tsamanin zamu wuce wata biyu a kasar nan dole idan zanje england dake zani kiyi renon ciki acan". yana k'arasa magana ya fad'a bathroom har ta bud'e baki zata masa tuni da adduar shiga ban d'akin sai taji mgnr daya sakar mata shi kuma har ya rufo kofar abun shi ta girgiza kai kawai tana kallon kanta "wani irin ciki kuma ana zaman kalau duka yaushe akayi auren ?."sak girgiza Kai tayi tace "yalla'ba kenan Allah ya bar min kai Allah ya kara maka lafiya yasa kayi tsawon rai mai albarka tana zaune tana tunnain irin soyayyar dake wakana a tsakaninsu dashi a kullum .a dan lokacin da sukai tare jinsa take kamar sun d'auki tsawon shekaru tare dan ya iya soyayya ." bata ankara ba sai ganinsa tayi akanta ya fito daga wanka lallai tayi nitso cikin tsananin tunaninsa mai tarin yawa, ahankali ta d'ago ta kallesa domin tasan yana nan ya tsareta da wad'an nan tsumammun idanun nan shi masu karyar mata da zuciya, gabanta ne ya shiga fad'uwa ganin launin yanayin su ya sauya kamar ba daga wanka ya fito ba gabad'aya hankalinta a tashe yake kar yace zai yi wani abu daita gani tayi yanayin fusakrsa ta gauraye da murmushi wanda bai bayyana akan fuskashi sosai ba amman ita ta fahimci murmushi ne." tafiya yayi da baya da baya yana kokarin sakin towel din dake d'aure a kugunsa tai saurin sunkuyar da kanta kasa tana jin fad'uwar gaba mai tsanani ."har ya gama shirinsa bata d'ago ta kallesa ba kamshin turarensa ne da ya doki hancinta yasa ta d'an d'ago kanta taga ya shirya cikin wasu hadaddun kananan kaya yana tsaye ya zuba mata idanunshi yana kallonta kamar wani maye kafin ahankali ya tako ya zauna kusa daita batare daya d'auke idanunshi akanta ba ita kam tuni kanta yayi kasa tana kallon kasan kafet ". "har ka gama shiri ?"ta fad'a tana cigaba da kallon kasa bai amsa mata ba yace "ki taso ki shirya mijinki shima ya zama abun kunya a wajenki ?ta d'ago a natse ta kallesa da shayayyun idanunta "yaushe nace abun kunya ne ?"ta fad'a tana masa wasa da idanunta ya d'an yi murmu shin gefen baki "idan ba haka bane mai zasa da zan shirya kikayi saurin yin kasa da kanki?"Tayi shiru kawai domin ganin ya ranfota bata da ta cewa dan gaskiya tana jin kunyarsa sosai "me zai sa ki dinga jin kunya ta haka nifa mijinki ne bai kamata ki dinga jin kunya ta haka ba komai kikayi min daidai ne haka nima komai na miki ke din tawa ce bata kowa ba still dai bata ce masa komai ba sai dai ta aro murmushi tace "nifa ba kunyar ka nake ji ba kawai abun nan ne nake jin..."sai tayi shiru ta kasa k'arasa maganrta tana jin wani irin fad'uwar gaba "wani Abu kenan ?". tai shiru tana kawar da fuskarta gefe aranta tace "wannan maganar tafi karfin bakina "Ina jinki!"allah ya gani bazan iya fad'a ba"ya jinjina kai yana dubanta "look at me !ya fad'a cikin wata irin murya mai kashe sansar jiki da kyar ta waigo ta zuba masa idanunta kamar yadda shima yake kallonta "Ina bukatar acire kunyar nan a dinga kula dani yadda ya kamata ." "kayi hakuri wata rana zan daina "ya gyara zamansa ya matso sosai kusa daita hakan yasa ta sak sunkuyar da kanta hannunta ya kamo ya rike ya had'e da nashi "idan ina kallonki bana iya rike kaina Ina son naga kin cire kunyar nan ya fad'a yana k'ok'arin had'e fuskokin su kafin tayi wani abu har lip's dinsa sun sauka akan nata tana kallonsa ya fara tsotsan lip's dinta lumshe idanun ta tayi tana kallon cikin kwayar idanunshi sai daya tsostsa son ranshi sannna ya tashi makale daita a parlour'n ta zame hannunta cikin nashi tana masa fatan alkhairi da dawowa lafiya "ban gane nufinki ba !"sarai ta fahimcesa dan haka tace "kayi hakuri anan zan tsaya ". yace saboda me !? "Ka fahimta mana"! tayi maganr cike da shagwa 'ba ya dawo kad'an ya janyota jikinsa "ban gane ba ki ganar dani na fahimta ,fuskarta ta manna a k'irjinsa tana boye fuskarta ."ya fahimceta sarai saboda yanayin tafiyar ne "idan saboda tafiyrki ce zuwa anjima zaki dawo normal ta d'ago ta kallesa tana hura masa hanci batare da tace masa uffan ba ," muje kici wani abu "ta girgiza masa kai" for now bana jin cin komai idan ina bukatar wani abu zan sauka "duk yadda yaso tabisa taki binsa anan sukai sallama ya kamo bakinta yana tsotsa da kyar ta samu ta cire bakinta acikin nashi ya tsaya yana dubanta tare da kai hannunsa ya kamo kuncinta yana kashe mata idonsa d'aya kamar wata sokuwa haka ta tsaya tana kallonsa ya kai bakinsa daidai kunnenta ya sakar mata zazzafan kiss, saurin d'auke numfashi tayi tana lumshe idanunta bata san tsawon minti nawa ya d'auka kafin ya cire bakinsa ba sai ji tayi ya fice ." Tunda ya fita suna makale a waya ko kiransa akayi zai ce ta rike wayar da zai shiga metting ne yace ta shiga d'akinsa ta duba durowa da system dinsa take kai zata ga wani book ta d'auka ta karanta kafin ya fito tace "okay tare da mikewa ta shige d'akinsa ta d'auko ta fito zuwa parlour tana zaune tayi zurfi sosai cikin karatun book din soyayya ne sai ga tabawa tana nemi izinin shigowa. bayan ta shigo ta gaidaita cike da girmama wa tace "hajiya tace kizo !" tai tsam da ranta tana tunanin kafin ahankali tace mata "okqy ganin nan zuwa "tabawa ta juya ta fice bayan fitar tabawa ta mike ahankali tana jin fad'uwar gaba dan bata san dalilin kiran ba kuma jikinta tuni ya bata kiran bana alkhairi bane ".ahankali ta koma d'akinta ta d'auko hijab ta sanya ta fito tana taku a natse har ta sauko babban parlour'n gidan sai dai bata ganta a parlour'n ba ta tsaya shiru tana tunanin shiga parlour'nta na biyu dan haka ta samu waje ta zauna akan kujera tare da had'e hannuwanta tana wasa dasu bata jima da zama ba sai ga tabawa ta fito daga hanyar parlour'n mami ,d'an murmushi tayi tace "ranki ya dade ai hajiya tana wan can parlour'n ki k'arasa can ."tana gama fad'ar haka ta shige kitchen." jikin maryama da muryarta a sayayye ta nufi hanyar parlour'n gabanta na matsanancin fad'uwa da karfin gaske ,aiko tana gama shiga parlour'n tayi mugun gani domin kuwa aunty khadija,aunty shahida zabiba da auta ne zaune sai mami dake zaune a tsakiyarsu suna tautauna wa ,nan take jikinta yayi sanyi haka gabanta ya cigaba da fad'uwa da yake bata san lokacin data soma karanto adduar da zata kare mutun daga duk wani abinda ya tunkarosa( allahumma inna na'uzubika min jadil bala'i wadarki shaka'i wasu 'il kad'a'i wa shamatatil ahda'i ) da kyar ta dinga d'aga kafafunta tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki ta cigaba taku inda gabad'aya suka zuba mata idanu suna mata kallo mai d'auke da tsana da kaskanci ,bata tsaya akoina ba sai a gaban mami ta durkusa har kasa ta gaisheta a tsorace "mami ina yini "!?da kyar mami ta bud'e baki ta amsa mata da "lafiya !"atakaice sannan ta juya ta gaishe da yayyen mijinta da zabiba batare data gaishe da nana hauwa'u ba zabiba ce kawai ta amsa mata gaisuwarta itama babu wani sakin fuska ,ta maida hankalinta ga mami tace "mami gani !" Kafin mami tayi yunkyrin yin magana aunty shahida tace "ita nana hauwa'u sa'arki ce da ba zaki gaishe daita ba ko kuwa rashin mutuncin da kike wa shi wancan shayayyen sokon mijin naki zaki kawo ma mutane ?"maryama tai shiru tana dukar da kanta kasa azahirin gasky taso ta gaishe daita amman ganin yanayin yadda take jifanta da mummunar kallo yasa taki gaisheta"idan shi kin shanyesa kin gama dashi mu baki isa ki gama damu ba, idan ma ba shi ba me ne ne abun so a wajenki ?"wallahi idan na kalleki kullum dariya nake fashe wa dashi saboda ba inda ya kamata soyayyarsa ta kare ba kenan amman munyi masa uzuri tunda ba haka aka barshi ba an rigada an dabaibayesa da mugayen asiri wallahi rayuwarsa is so pity kin d'auki kaya kin d'aurawa kanki kiji tsoron Allah abinda kikayi kika rufe wa d'an uwamu ido dashi ki kwancensa"ke da iyayenki kunyi shirka kun mallake sa idan ba haka ba ina shi ina ke bare wannna tsinanniyar unguwar taku da ko masu aiki a karkashinaa bazasu zauna acikinta ba bare macen da yake aure ."ahankali maryama ta d'ago kanta tana kallon aunty shahida dake magana cikin nuna isa da mata kaskanci ." "Wallahi ina namiji bazan ta'ba had'a iri dake ba ko ba dan komai ko dan zuriar da zan had'a dake na kaicewa aurenki wai fa ashe ubanta d'an giya ne kuma acikin giyar ya mutu uwarta kuma sai da suka gama hole warsu da ubanta akayi auren wallahi tur da aurenki "aunty shahida ta k'arasa maganar tana zabga mata harara"inna lillahi wa inna ilaihi rajiun maryama ta dinga furtawa tana runtse idanunta tana danne damuwarta da hawa yen daya cika idanunta dan karsu ga raunita bayan aunty shahida tayi shiru itama aunty khadija ta Kama hakan yasa mami ta mike ta shige d'akinta tana goge hawayen bakinciki abinda adamcy yayi mata uba dan gida uwa karuwa wani irin zuriar zata hanfo masa tashin
Chapter 68 · 0% Book details