← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 94

Sashe 6

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

halinsu d'aya mugaye ne masu muguwar zuciya." har ya zauna akan tebirin cin abinci ya juyo ya kalleta bayan ya zauna "Kayan abincin da kika sa a bayan mota nawa ne ko kuwa ?"ta d'auke kanta gefe batare data bashi amsa ba ai yasan nashi ne sarai da zai mata wata irin tambaya ,sosai kwalla ta cika idanunta" ita kam gara duk su taru su kasheta ta huta da wannan duniyar dan sam ba Jin dadin zama acikin duniyr take ba bata an kara ba sai dai kawai ta ganshi a gabanta lokacin har kwallar idanunta sun zubo "yanzu me ye abun kuka "?shiru tayi kawai tana shesheka ya kai hannunsa zai share mata hawaye ta kawar da fuskarta gefe alamun bata so "ki fahimceni ban kawo ki gidan nan dan na sakaki kuka ba ". "Amman me ya kawo wad'an nan maganganun?" "ai kasan dole maganar tasani kuka , ban San dalili da yasa baka son ganina cikin farinciki ". "ni din ?!ta gyad'a masa kai alamun "eh!"tana harararsa "okay zamuyi mgana amamn kiyi min lamani inci abinci tun asuba dana yi training na sha ruwan zafi ban ci komai ba har yanzu kiyi min hakuri in samu na saka wani abu acikina sai mu cigaba da magana." Bata ce masa komai ba illa ta juyo ta kalli agaogon bangon parlour'n karfe tara saura minti shadaya "karki damu zamu gama komai zuwa karfe goma kilama ba zamu Kai ba,still dai shiru tayi masa dan ita tsoronsa ma take ji "me yasa zai bincika mata wayarta?" sannan me ya kawo batun idan tasan dan wani muradi ne zata auresa ta janye, ta aure sa dan Allah ko kuma ta fasa aurensa gabad'aya duk me ya kawo wad'an nan maganganun ?"idan dai abincin da kika dafo min ne a mota in sa a kawo min inci ?"ni kaje kaci abinci kuma ai kasan naka ne tunda Kai ne kace a dafa maka ?"k'aramin bakinta yabi da kallon yadda take motsa shi ahankali kamar bata so ,ko da yake da gani maganar ma a dole take yinta ."wani farin abu ya danna bayan kamar minti biyar akayi knocking ya tashi yaje ya bud'e kofa ,wani yaronsa ne tsaye cike da girmamawa " "umar kaje bayan motar dana shigo dashi yanzu ka d'auko min jakar abinci" da sauri umar ya juya ya barshi tsaye a bakin kofa tsayuwar jiran dawowarsa bai jima ba ya sake dawowa cike da girmamawa ya mika masa ya amshi jakar abinci ya maida kofar ya rufe ya dawo ya zauna akan kujera ya d'aura jakar akan dining table yana dubanta ." "dan Allah kayi sauri kaci muyi maganar da zamu yi dan dare ya fara bana son Ina yin dare a waje "baki yi min yadda zanji dadin cin abinci bane ". ya fad'a tare da mikewa ya karaso inda take zaune ya kamo hannunta tayi hanzarin zata fizge hannunta yace "stop maryama kinsan banason kina hanani ta'ba abinda ya kusan zama halal dina "ai sai ka jira har lokacin yayi tukun bawai ka maidani kamar wata sakariya ba "karki damu lokaci yayi "a ranta tace "idan wannan uwartaka ta bari ba ."wallahi na matsu naji na d'aura miki marata kiji..."ai tun kafin ya k'arasa maganar ta fixge hannunta tana hararrasa ya mike tsaye yana murmushin gefen baki "matsoraciya kawai ." Wata hararar ta buga masa "ki san ban ta'ba biyanki komai ba amman akan kallon nan naki mai sa ki kara min kyau karki sa a yanzu nace zan biya "wata hararar ta sake masa ".okay in zo na biya kenan ?ya fad'a yana tahowa ai ko ta canza fuska zatai masa kukan shagwaba bai san sanda ya sake murmusawa ba "I really like all you maryama ya fad'a yana kashe mata idonsa d'aya sannan ya koma ya zauna kamar yadda yayi d'azu ." A daidai wannan lokacin da mr ata yake zaune yake cin lafiyayyen kuskus din da maryama ta dafa mashi mami na can tare da yaranta suna tautaunawa akan waya "inda aunty khadija tace "mami ki barshi yayi auren sai ki kafa masa duk sharudd'anki idan kina dasu "haka ne khadija maganarki tayi amman ni zan so mami tasa shi ya maida maryam ya had'esu duka "inji cewar aunty shahida "anya shahida kina ganin hakan zai yuwu kuwa ?"mami ta fad'a cike da zullumi "zai yi mana a yadda ya matsu da yarinyar nan ai kina fad'a masa zai amince "to kina ganin ita maryam zata yarda ta koma masa ne dan kwata kwata banga alamun zata koma ba ?"idan dai zan bar shi kawai zan barsa yayi aurensa shikenan yayi galaba akaina "mami ta k'arasa maganar cike da rauni "ai mami halin adamcy ne sai shi inda kika san ba mutun ba "ki bar shi din yayi auren amman karki d'aga masa kafa idan ma da hali yarinyar ta tare agidanki duk abinda zaayi kina gani "kuna ganin haka yayi ace ta tare a cikin gidan nan alhalin akwai tarin gijaje muna dasu ?". "aunty khadija da aunty shahida har ma da auta suka ce "haka ne kawai zai sa ki san halin da suke ciki akan zamansu dan kinsan yaran talakawan da shegen shige shige kar aje a mallake miki d'a abinda ya kamata ko auren zai yi yaje ya nemi yar gidan manyan mutane amman yaje zai kwaso mana jaraba."sarai zabiba ta fahimcesu suna bawa mami shawarar ne dan su samu damar aiwatar da nufinsu akan yarinyar mutane ." mami tace "to shikenan yanzu idan mun gama wayar nan zan kira maryam naji raayinta akan komawar ta "mami da dai kin dakata da kiranta tukun har kuyi magana da shi yaya adamcy kuji me zai ce ,dan a so samuna ne a hakura da auren nan ,kowa yaje yayi rayuwarsa kamar hakan zai fi mana kwanciyar hankali kar a sake komawa gidan jiya "haka ne zabiba kema kinzo da shawara mai kyau zan jirasa har sanda zai sake nemana da maganar dan bazan nemesa ba .""wannan yayi daidai mami karki nemesa ki barshi idan ya gaji zai kawo kansa ne "inji cewar zabiba daga nan ta masu sallama ta sauka ta barsu akan layi itama mami sallama tayi masu ta soma neman layin maryam dan taji lafiyar khaira kira d'aya tai mata ta d'aga tana gaisheta .""maryam ya kuke ya khaira da fatan duk kuna lafiya ?"muna nan lafiya mami ga khaira nan yau ma akayi mata allurar immunization sai rigima take " "Dole tayi rigima yana masu zafi idan anyi masu naga kin d'aura ta a status jiya ta kara girma "wallahi mami nima girman khaira har mamaki yake bani sai kace yar four months haka ma dazu uncle mb da ya kira mu vedio call yace wai ta kara girma "mami tai murmushi cike da jin dadi tace "ayya muhd bello Ai kuwa ya kyauta may be daga nonnki ne dan wani lokacin idan nonon uwa yana da kyau zaki ga kafin wani lokaci ya kar'bi yaro sai kiga yaro yayi saurin girma"to ai mami kamar ma kar mu dawo abuja shikenan khaira ta daina karba nono Madara take sha batason shan nono wallahi,ikon Allah aiko bata biyo babanta ba ,adamcy ya shan nono sosai kuma yayi kulafucin nono dan har na yayesa baya bacci batare da hannunsa yana kan nono ba ,maryam tai shiru batare da tace komai ba "Allah dai ya raya mana ita in sha allahu nima zan shigo abuja nazo na ganku "to mami sai kinzo munyi kewarki sosai "mami tai murmushi tace "baku kai ni ba maryam tafiyarku tamkar kun tafi da komai nawa ne bana jin dadin zaman gidan nan in sha allahu zaku ganni nan kusa suka cigaba da hirarsu." bayan mr ata ya gama cin kuskus zama yayi kusa da maryama kamar d'azu sai dai yanzu lemun gwangwani ne a hannunsa wanda itama tunin ya kawo mata nata gabanta sai dai ita kam ta kasa sha "shawarar me kika yanke ?"ni bani da wata shawara data wuce aurenka zanyi dan..."sai kuma tayi shiru ta kasa k'arasa maganarta" kalleni sosai "ta d'aga kanta fuskarsa a d'aure kamar bashi ya gama murmushi ba ta kallesa kwarjinsa ya mamayeta sosai haka ma kyawunsa ya karu alokcin d'aya wanda yasa taji son shi ya sake dirar mata a zuciyarta tayi saurin kawar da kanta gefe tare da runtse idanunwanta tana sauke numfashi ahankali "me kake son nayi maka adam....."? "ban ta'ba jin wanda ya kira ainihin sunana naji sanyi araina ba sai ke maryama ki d'aure ki aureni saboda da Allah ta bud'e idanuwanta" ai daman saboda Allah zan aureka ta bashi amsa cikin sanyi murya" yayi gyaran murya tare da kawar da idanuwansa daga kallonta idan har na zayyano sharuddana ya zama dole ki zaba biyu aciki Ina tabbatar miki babu fashi ko tausayawa akan kowani sharadi da zaki zaba dole zaki amince tunda na fuskanci bazaki fad'a min gaskiyar da zuciyata take bukata ba " Gabad'aya kasa magana tayi ta bishi da kallon mamaki"sharadina na farko "ki janye muradin aurena dan wata manufa ,sharadi na biyu idan na aureki ya zama dole a ranar zan kusanceki .""ki zaba d'aya idan kuma bazaki zaba ba in fad'a miki d'ayan wanda ya zama dole shi ki zabeshi ." "Wai duk me ya kawo wannan maganar ki zaba idan kinsan babu komai acikin zuciyarki "daman ance maka zan aureka ne dan wata manufa ko me yasa duk kake irin wad'an nan maganganun?"amsa nake bukata kafin lokacin da sharadi na uku zai zo"zan aureka ne dan Allah sai dai batun kusanta wannan ne gaskiya ..."is okay na rigada na gane dan wata manufa kike son aurena "ka shiga zuciyata kasan menene aciki ?"tayi maganar jikinta na rawa "muje sharadin na qarshe,sharadi na karshe tunda baki zabi biyu acikin sharadina ba zan kashe mu nida ke acikin gidan nan ." "Ban fahimci abinda kake nufi ba baki san mutuwa ba kenan ?"nasan mutuwa mana kashemu fa kake nufin zakayi ?"ashe zafin zuciyar ka har ta kai ka iya kisan kai ni dai gsky ban tashi mutuwa ba Ina son na cigaba da rayuwa tare da mahaifiyata ,kai idan ka gaji da duniyar zaka iya kashe kanka amamn bayan na fita a gidan nan "ya isa ya isa !!"shikenan
Chapter 6 · 0% Book details