← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 94

Sashe 12

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace mata "mr ata ne yazo umma tace tun yaushe dan kin dade da barin d'akin nan ?eh ya d'an jima da zuwa amman yanzu ya wuce yama ce zai zai je suyi magana da mahaifiyarsa zuwa gobe zai dawo "to Allah yasa muji alkhairi ,maryama ki rike mutuncinki karki sake ki bari so ya yaudareki duk da gabad'ayanku Ina maku kyakkwan zato amamn dai ki sake rike mutuncinki "tana gama fad'ar haka ta mike ta nufi bayinta itama haka ta mike jikinta a sanyaye tana tunnain maganar umma ruwa baya tsami banza ko dai umma taga wani abu ne "?inna lillahi ta fad'a cikin tsananin damuwa tare da shigewa nata d'akin." ******** karfe tara daidai a gidan mami tayi ma mr ata da amar adaidai lokacin mami na zaune a babban parlour'nta tana vedio call dasu khaira kawai taga shigowarsu bakinsu d'auke da sallama "assalamu alaikum."a hankali mami ta bu e idanuna sosai akansu tana jin wani sanyin dadi na ratsata alokacin da idanunwanta sukai tozali da adamcy nta sanye cikin wasu hadaddun kanana Kaya Wando da riga ash colour kanshi rufe da facing cap nan take parlour'n ya sauya da kamshin turarensu ta amsa da" walaikumssalam tare da d'auke kanta dan kar ya gane tayi farinciki da ganinsa, amar ya gaishesa cike da girmamawa ta amsa masa fuskarta babu yabo babu fallasa sannan ya samu waje ya zauna shi kuwa mr ata kujerar da take zaune ya nufa ya zauna a kusa daita yana kamota hannuwanta cikin nashi tana kokarin zare hannunta ya ake riko hannun yana cewa "I'm very sorry sweetheart I don't mean to hurt you my world best nayi nadama abinda nayi kiyi hakuri ki yafe ma adamcynki"shiru mami tayi tana cigaba da kallon fuskar khaira ta cikin wayar inda adamcy ya kar'bi wayar hannunta bata hanashi ba fuskar khaira yayi tozali daita tana murmushi "yaushe rabon ya ganta bama zai iya tunawa ba haka nan yaji wani sanyi ya ratsashi ya kalli mami "sweetheart khaira ce haka ?"ta gyda masa kai kawai "gsky ta girma "ya fad'a yana kashe wayar ya ajiye a gafenta ". Ya zaka kashe min waya bayan wayar nan tafi min ganinka mahimmanci murmushi mr ata yayi yace "haba dai sweetheart saboda ni fa kike son khaira "waye kai a wajenta da zan sota saboda kai?"kasani ba dan kai nake sonta ba maryam jinina ce kuma kasan ko wani ta haifawa diya dole zan sota Ina son khaira ne saboda diyar maryam ce yace "shikenan naji Sweetheart mu bar wannan maganar muyi maganar data kawo ni "ai dole kace abari tunda ba imani dake kai ba sai da yayi daya sanin kar'ba wayar da yayi "ina jinka Allah yasa maganar data kawoka ba shirme bace ?"ta fad'a tana karkada kafa ya numfasa yace "nazo ne na baki hakuri akan abinda ya faru kiyi hakuri ki yafe min kiyi min lamani na auri maryama"ya fad'a tare da yin shiru yana jiran yaji me zata ce masa "sai dai har tsawon minti goma bata ce komai ba ya kalli amar yayi masa alamar ya sake bata hakuri "sweetheart dan Allah kiyi hakuri ki duba lamarina "na duba lamarinka akan yarinyar daka nuna tafini daraja ". "haba sweetheart me yasa zaki fad'a haka kema kinsan babu wata mace da zata kai darajarki ?" matsayinki dabam nata dabam" banga alamun haka ba tunda har zaka iya kaurace min amman ita kana zuwa wjenta kuyi iskancin da kuka ga dama ai d'auka zaka aureta ne a boye batare da izinina ba wallahi da kayi dana sanin cewar ni uwar aka ce "ta fad'a tana zare hannunta dake cikin nashi ."shiru yayi yana kallonta inda amar yayi gyaran murya ya soma magana "mami kiyi hakuri dan Allah adamcy bazai ta'ba auren yarinyar nan ba muddin bada izininki ba kuma kinsan da zai aikata hakan da yayi amman tsananin son da yake miki ya kasa samun sukuni kuma ya kasa biye wa zuciyarsa bare ya aureta a boye ,shiyasa ma yace na rakosa ya baki hakuri ki lamince masa,a yadda yayi nadama ko cewa kikayi ya hakura daita ina mai tabbatar miki zai hakura daita domin farinciki "haka yace maka zai iya hakura daita ?"mami ta tambayesa tana kallonsa zaune shiru yayi ya kasa bata amsa "nifa na haifa adamcy kuma duk duniya nafi kowa sanin halinsa zan amince yayi auren ne tare da sharadi idan har ya amince yaje yayi Allah ya bada sa'a ". "Sharadi kuma sweetheart ?"ya fad'a tare da sake kamo hannunta "eh sharadi kafin kayi auren nan idan ka amince na fad'a kaje kayi aurenka idan kuma baka amince ba shima kaje kayi aurenka sai dai babu hannuna kuma babu ni babu kai har abada ,kallonta ya cigaba da yi zuciyarsa na wani irin tsalle hakan nan yaji sharadin mmai masu wuyar aiwatar wa ne agaresa amamn dai zai bita ahankali yaji sharadin nata Allah dai yasa masu sausauci ne "muryarsa a kasalance yace "Ina jinki sweetheart ki fad'a min ni mai biyayya ne agareki "wacce ni agareka da matsayina "?ke mahifiyata ce kuma duniyata ba kuma zan iya fadar matsayinki a zuciyata ba dan duk yadda zan fad'a kin wuce haka acikin zuciyata "da kyau da kasan haka ,sharadina guda uku ne da zan fad'a maka kuma acikisu sai kayi duka idan kaga zaka iya to". ta fad'a tana sake had'e fuska shiru yayi yana kallonta yana Jin zallar damuwa Allah yasa babu sharadin maida wannan duwaf din yarinyar cikin rayuwarsa "a matsayina na mahaifiyar Ina son ka kar'bi khaira har acikin zuciyaka ka janye kalmar ba yarka bace "sweetheart wannan ai tun tuni na kar'bi khairat Allah shine sheida ta tunda na d'aura kwayar idanuna akanta na tabbatar da jini ce ban kuma isa nayi wa Allah wayo ba ." Wani sanyayyayen ajiyar zuciya mami ta sauke tana godewa Allah sannan ta cigaba da magana sharadi na biyu "idan ka auri ita wannan yar gwal din da kake so a gidan nan zaku zauna "gidan nan kuma !?"ya furta hakan a fili ko bazakayi ba ne ?"ya kalli amar inda ya gyad'a masa kai alamun ya amince "numfashi ya sauke yace "shikenan sweetheart wannan ai ba wata matsalar bace."tayi shiru tana tunanin sharadinta na uku wanda itama sai da taji bugun zuciyarta a fili "sharadi na uku Ina son ka maida maryam kafin ka auri wancan yarinya". da wani irin sauri yace"sweetheart wace maryam kuma ?"wace maryam ka sani ?"maryam dai tawa wacce ta haifa maka diya ita nake nufi nan take kansa yayi wani irin mugun sara ya ajiye wayar hannunsa akan a gefensa tare da cire hullar kanshi ya ajiye yasa hannuwansa gabadaya ya dafe kanshi dashi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa bashi ba hatta amar ya shiga damuwa sai dai maganarsu ce bai isa ya saka bakinsa ba muddin ba izini aka bashi ba ." bayan kmr second biyu ya d'ago yana duban mami kmr zai yi kuka yace "why sweetheart "?ban maka dole ba idan kana bukatar aurenka ga abinda nake so sharadina guda uku kuma dole ayi min su a qalla ya kusan minti talatin zaune cikin tashin hankali yana girgiza kafafunshi batare da yayi magana ba yana tunanin sabon tashin hankalin da mahaifiyarsa take son kunno masa jikinsa sai tsatsafo da zufa yake ahankali nasihar maryama ta dinga masa yawo acikin brain dinsa"su iyaye suna da darajar da zasu ce ka bar abu ka barshi duk kuwa da tsananin son da kake wa abu ,haka zalika idan sunce kayi abu to ka hanzarta yinsa duk kinka da abu domin kuwa da zarar sun mutu shikenan anan duniya kad'ai muke da damar kyautata masu domin mu samu aljanna barin ma Kai da kake matsayin namiji wanda Allah yace aljanarku tana tafin kafafun iyayenku "mami tai shiru tana dubansa ganin kamar maganarta ta shigesa sai dai zuciyarta rawa take kar yace mata bazai yi ba ." d'ago Idanunshi ya dubi agogon dake manne a bangon parlour'n yaga goma da wasu 'yan mintina sun wuce da kamar yace mata bai amince ba da sharadinta na uku ba amman hakan nan maganar maryama taki barin zuciya da kwakwaluwarsa ta huta kuma tabbas yasan gaskiya ta fad'a masa duk da alokcin ya dakatar daita da Zara mami ta bar duniya duk son da yake mata shikenan kuma duk yadda yake son ya kyautata mata babu halin yin haka gara ya kyautata mata tun tana raye sai dai abinda take so din ne yana da daci a zuciyarsa ahankali ya motsa lips dinsa yace "shikenan sweetheart na amince ."a natse ta kallesa tana jin wani irin sanyi zuciyarta "ba wai ka kar'beta da wata manufa acikin zuciyarka ba ?"ko d'aya sweetheart zanyi komai matukar zai faranta ranki ." ai nan da nan mami ta saki fuska ta soma saka masa albarka ta kalli inda amar yake yana murmushi "amar kaji abinda adamcy ya fad'a ka zama sheida babu wulakacin babu tozarci dan bazan d'auki cin kashin da yayi mata a baya ba dan ko yanzu hukuncina ne ita kanta maryam batasan da zaman maganar ba amman tunda ya amince da umarnina zan fad'a mata kuma nasan maryam bazata bani kunya ba "." "Allah ya basu zaman lafiya "inji cewar amar wani kallo adamcy yayiwa amar mai had'e da harara mami tace bangane wannan kallon da kake masa ba ?nifa banyi maka dole ba abu kake so nima kuma nace ga abinda nake so "sweet heart abar maganar dan Allah tunda dai na amince kiyi ma bab babba magana suje gobe gidansu maryama ayi abinda zaayi idan ma ta kama a d'auran ayi "gobe goben nan kake nufi ?"ya gyad'a mata kai dan gabad'aya bai son dogon magana "ba dai gobe nan ba sai dai lahadi ta sama , idan mun gama magana da maryam ta amince sai maida aurenku wannan lahadin "inna lillahi mami dai ta rantse sai taga karshen sa, shi sharadinta na maida maryam kwata kwata bai masa dadi ba, Allah yasani mami ta sake shiga rayuwarsa dan bai ji aransa ko darajar diyar da mrym ta haifa masa zata ci a wajensa kamar dole sai tayu dashi shifa wannan nacin yana cikin abinda yasa sam baya jinta aransa dan arayuwarsa ya tsani naci bare
Chapter 12 · 0% Book details