← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 94

Sashe 20

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

uku acikin takardar bata san sanda hawayen farinciki ya soma gangaro mata ba" yaushe rabon tasa kudin a idanunta ?"bazata manta ba tun zamanin da take cikin gatanta da'ake kwasarsu zuwa England yawon bud'e ido daman zata sake tsintar rayuwarta haka ?"umma ta rungumota ajikinta tana cewa "bazan ce ki daina kuka ba bilkisu domin kuwa nasan na farinciki ne kinga yadda Allah yake ikonsa ko? ".kinga yadda jinkiri ya zame mana alkhairi ko "? naunauyen ajiyar zuciya aunty ta sauke alokcin data tuno matsalar da suke fuskanta a duk lokacin da mgnar auren maryama ya gabato ,muryarta na rawa tace "umma mu daina murnar nan haka mu bari muga d'aurin aure wallahi zuciyata rawa take Ina cike da matsanancin tsoro da farinciki tsorona kar wani abu ya biyo baya duk da na dogara da Allah kuma kullum shi nake kaiwa kukana"ki kwantar da hankalinki bilkisu babu abinda zai faru khairan in sha allahu."aunty ta sake rungume umma ajikinta tana zubar da hawaye umma ta kai hannunta tana shafa bayanta tana rarrashinta tare da fad'a mata kalaima masu kwantar da hankali ,karki karaya da izinin allah aure kam za'ayi sa har ma sai munga jikoki alfarma manzon allah, bilkisu muna da kyakkywan zuciya ba mu kasamce azzalamai ba kuma mun dogara da allah duk wanda yace Allah to wallahi Allah ya isar masa muyi fata alkhairi da addua kawai Allah yasa auren ya zame mana alkhairi duniya da lahira in sha allahu zaayi auren nan ta fad'a tana zareta jikinta ta mika mana kudin ."aunty ta girgiza mata kai tana cewa "aa ki barsu a hannunki ai kudinku ne !"umma tai mur mushi tana dubanta shiyasa a kullum maryama ke sake shiga ranta bayan kyatatawar da maryama take mata aunty ma na mata al kunya akanta tana nuna mata cewar maryama din diyar ce halak malak ." "shikenan Allah yasa albarka ta fad'a tare da fitowa ta nufi bangarenta cike da murna ." Aparlour'n umma ta iske maryama tsaye ta kamota ta rungumeta tsam ajikinta"yar albarka kinyi goshi wahalarki tazo karshe maryama yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa ta zareta ajikinta ta riko hannunta ta zaunar daita tana kallonta kamar wata sabuwar halitta ."maryama tace "umma naji kamr kuna maganr auren ,auren wa kuma za'a d'aura "?umma tace bakiji nace kinyi goshi ba ai aurenki za'a d'aura nan da kwana goma masu zuwa, idanuta ta ware sosai akan umma tace "ni kuma umma da wa kuma za'a d'aura min aure ?"tayi mata tambayr ajere zuciyarta na bugawa da karfin gaske ". "kwantar da hankalinki adamunki zaki aura tun shekaranjiya mukayi waya dashi cewar 'yan'uwansa zasu zo nema masa aurenki yau to Alhamdulillah sun zo har an gama magana"ta bata amsa cike da matsanancin farinciki maryama ta kasa furta komai dan zuciyarta ke wani irin bugawa da mugun karfi babu abinda ke yawo acikin kwakwa luwarta kamar irin halaye da tsare tsaren mr ata yanzu daman duk ya shirya haka shine ya maidaita banza koma ya kirata ya fad'a mata cewar yan'uwansa zasu zo ?" Umma ta riko hannunta cikin nata tasa takardar kudin "kinga kudin da suka kawo kawai na gaisuwar iyaye a zahirin gaskiya maryama adam yana matukar sonki kuma ina fatan zai jiyar dake dadi da farinciki a gidansa "maryama tai shiru tana sauraron umma kawai dan ita kad'ai tasan halin tashin hankali da take tabbas tana tsananin son shi sai dai idan ta tuna tashin hankalin da zata tsinci kanta a gidansa sai taji gabad'aya son ya fita aranta kamar a yadda take ji yanzu dan ji tayi kamar kwanakin mutuwarta ne ya kusantota ahankali ta ajiye takadar kudin akan cinyar umma tana mai sunkuyar da kanta ta dafe ." "Ya naga kamar baki farinciki da faruwar wannan abun alkhairin daya samemu ba ?"still shiru mryama tayi zuciyarta na wani irin tsinkewa tare da bugawa "maryama "!umma ta Kira sunannta "ta d'ago kanta ta kalleta cikin yanayi na damuwa "ki kwantar da hankalinki,ta gyad'a mata kai kawai batare da tace komai ba "yauwa ki saki jikinki,ya kika damu kamar baki son adam bayan nasan kina son shi sosai har ma fiyye da son da yake miki "umma ta karasa maganar cike da zolaya ".nan da nan maryama ta sake canza fuska "Allah umma ki daina cewa haka ni bana wani son shi .""wannan kuma wani zaki fad'a wa bani ba "maryama tai shiru dan umma ta bar zance dan tana mugun sakata jin kunya idan tace tana son mr ata "maryama!"umma ta sake kiran sunanta a karo na biyu." gabad'aya maryama ta tattara hankalinta da natsuwarta gareta dan ta fahimci tana son tayi magana mai mahimanci ne . "ina neman wata alfarma a wajenki maryama "haba umma kiyi maganrki kawai ba sai kin tsaya neman wata alfarma ba umma ta sauke numfashi tace "na gode Allah yayi miki albarka"maryama tace "ameen!"adamu yazo min da wata magana jiya cewar idan an d'aura aurenku a gidansu zaki zauna tare da mahaifiyarsa sai dai na ara bakinki na bashi kwarin gwiwar babu wata matsala zaki zauna daita domin ke din mai biyayya ce agaresa "ai nan take k'irjin maryama ya cigaba da bugawar da yake ta dinga kallon umma cike da matsanancin tsoro da tashin hankali ." Muryarta na rawa tace "umma gidansu kuma ?umma ta gyda mata kai alamun "eh !"haka yace maryama "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "umma mai yasa kika amince masa ?allah bazan iya zama tare da mahaifiyarsa ba wallahi tsoronta nake ji Ina tunanin wahalata ta rag a she wahala basu ragu agareni ba ? ashe akwai wasu sabbin shafukan a gabana ?sai yaushe ne zan daina shan wahala mai dan karen wuya da azabtar da zuciya da gangar jiki "?yaushe ne ruhina zai samu salama ?kiyi hakuri ki yafe min maryama nayi karambani gashi har na bashi kwarin gwaiwa zaki iya zama da mahaifiyarsa ashe ban sani ba cewar bazaki iya ba kiyi hakuri wallahi da nasan bazaki iya ba da ban amince ba nan take umma ta rikice ta soma kuka itama tana bata hakuri ."Allah sarki maryama ganin hawayen umma ya sake rikirkita mata lissafi ta zube gabanta tana kuka tana bata hakuri "dan girman Allah umma kiyi hakuri ki daina kuka ki daina bani haquri naji duk abinda kika fad'a zanyi kece komai nawa, duk yadda kikayi dani daidai ne na na amince na mika wuya zan zauna daita lafiya rokon da nake dashi agareki kiyi min addu'a,ki sani cikin kowacce addu'aki Allah ya bani hakurin zama daita , ya hanani gazawa bare na watsa miki kasa a ido sannna na samu juriya mai yawa" tana kaiwa nan ta kasa cigaba da magana ta fashe da wani irin da kuka mai ta'ba zuciya tana tuna mugun halin yan'uwansa a kullum suke addabarta dashi ,tana son fadawa umma sune silar saceta amman kuma tsananin kaunar data ga umma take ma mr ata yake hanata fad'a mata dan tasan dole kaunar zata juye izuwa mummunar kiyayya mai zafi dan umma bata wasa da duk wani abinda ya shafeta ." "kiyi hakuri da rayuwa maryama in sha allahu babu abinda zai faru sai alkhari "ita dai ta barwa Allah komai duk hukuncin daya yanke akanta mai kyau ne idan zama dashi na har abada idan rabuwa dashi umma ta mikar daita ta zaunar daita a kusa daita ta rungumeta tana rarrshinta kuka take sosai kamar wacce zaayiwa auren dole "maryama ko akwai wani abu ne bayan wannna ki fad'a min dan hankalina ya tashi da kukanki "me zata ce ?"wanda ya wuce babu komai ai kuwa shi din tace mata babu komai ayanzu babu abinda nake bukata sai adduarki ."to ki bar kuka nan haka in sha allahu zamanku alkhairi ne babu abinda zai faru kuma nayi miki alkawarin zan dinga zuwa akai akai ina duba lafiyarki "ni wallahi daman zamu tafi tare gabad'aya umma ." Umma tai murmushi tace"maryama kenan ai gidan miji ba'a bin mutun ,mutun shi kad'ai yake shan gwagwamarya a gidan aurensa duk wanda kika gansa a gidan mijinsa to fa daga shi sai halinsa ne ina miki kyakkywan fatan nasan halinki a duk inda aka kai ki bani da haufi zaki zauna lafiya da kowa sai dai kiyi kokari ki cire tsoron mahaifiyarsa idan adam ya gane kina jin tsoronta bazai ji dadi ba ki tayasa yiwa mahaifiyarsa biyayya kinji diyar albarka "jiki a sanyaye maryama ta gyada mata kai"alamun taji ." "ki s mahaifiyarsa ki kuma so yan'uwansa ki ja kowa nashi ajikinki ki kuma kyautata masu domin zuciya tana son mai kyautata mata ahankali umma ta dinga mata nasiha tana fad'a hanyoyi da zata bi wanda zai kawo mata kwanciyar hankali a gidan mijinta ." Gida ya cika da murna umma aunty banda bangaren baba gali ,habib ma daya dawo gida ya samu labari bakaramin murna yayi ba da gudunsa ya shigo parlour'n umma yana wani irin ihu yana ganinta bai tsaya wata wata ba ya d'agata sama aiko maryama ta fara ihun ya sauketa kar yarda daita amman yaki sai faman juyi yake daita a parlour'n kasancewarsa karfafa dan idan ba sani kayi ba zaka d'auka shine yayanta "wallahi after dad ka saukeni umma kice ya saukeni wallahi juwa nake gani shi kuwa dariya kawai yake yana furta congratulations heartbeat ." Umma tayi murmushi tace "kai ban son iskanci sauke min yarinya tace juwa take gani ahankali ya zaunar daita akan kujera sannan ya zauna gefenta alokacin ta dafe goshinta yace "sorry sorry wallahi na rasa me zanyi ne" ya kai hannu zai ta'bata ta kwace hannunta zata kai masa duka yayi saurin rike mata hannuwanta yana murmushi "umma tace "kinga illar rashin cin abinci ko kalli yadda habib yayi sama dake kamar wata yar kaza "ai gabad'aya suka sa dariya maryama tace "allah umma ko ina cin abinci bazan iya da after dad ba baki ga yanzu karfe yake ci ba "yiwa mutane shiru ko baya cin karfe bazaki iya ba da wannan jikin naki "habib yayi shiru yana kallonsu bayan umma tayi shiru habib yace "yanzu hearbert gabad'aya ATA zaki aura gaskiy am so happy da wannan hadin daman irin wannan kan ya dace dake Allah ni me yasa ba'a d'aura auren ba ?umma tai murmushi tace da yau da kwanakin da
Chapter 20 · 0% Book details