← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 94

Sashe 27

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da yayi mata a gaban d'anuwanta ."Jiki a sanyaye adamcy ya fito zuwa parlour'n idanunshi ya sauka akan yan'uwansa suna kallonsa kowace fuskarta a had'e banda zabiba wacce alamunta ya muna tana son masa magana sai dai yanayinta ya nuna masa tana jin tsoro.kallonsu ya cigaba da yi gabad'aya ya kasa samun taya murna daga garesu atakaice dai sun had'e masa kai lallai kuwa zai yi dasu ." "yadda suka nuna masa shima haka zai masu zai ciresu acikin rayuwarsa zai yi rayuwarsa babu su zai yi rayuwarsa daga sweetheart dinsa sai mrym da ya'yan da zata haifa masa daman ba tun yau ya saba da rayuwar rashin d'an uwa namiji ba domin yasan da ace yana da yaya ko kani namiji da bazai ta'ba juya masa baya akan wannan matsalar ba ." shi a yanzu har gara su sultan akan su, domin duk tswon lokacin da'aka d'auka suna nuna masa kiyayya da rashin jituwar dake tsakaninsa da baba karamin yau dasu aka d'aura masa aure ."inda hajiya zulf'au ta kallesa tsanake sannan tace "Adam har ka fito ?"kan shi kawai ya gyad'a mata alamun "eh!" tare da kai hannu yayi baya da hular kanshi ya shafa goshinsa hajiya zulfa'u ta kalli su aunty shahida taga duk sun yi masa dip sunyi wani iri kuma tasan duk wanan shirun bai wuce na auren yayi bane tunda mahai fiyarsu bata so dole suma bazasu so auren ba amman duk da haka bai dace su zare kansu cikin lamarin auren ba ." magana take son tayi dasu gabad'ayansu sai dai taga yanayin adamcy din kamar yana cikin tsananin damuwa tana kallonsa ya fara taku a natse ya nufi kofar fita ta yunkura ta biyosa tare da kiran sunansa ,adaidai bakin kofa yaja ya tsaya batare daya juyo ba yana jin zallar damuwa acikin ranshi ta tsaya a kusa dashi tana cewa "ka natsu ka kwnatar da hankalinka komai mai wuce wa ne ,"bana son ka tsani 'yanuwnaka duk da sunyi maka ba daidai ba, lamarin mahaifiyarka zaka duba su ya'ya mata ne wad'an da a kasani da Taya iyayensu kishi amman da sannu komai zai wuce barin ma idan yarinyar tana da kwantar da kai ".numfashi kawai ya sauke batare da yace uffan ba duk da maganar yake son yi sai dai ya tsinci kanshi da kasa yi ." "zuwa karfe nawa ne zaaje d'auko surukartawa dan ina son na d'an kwanta kad'an kafin lokacin "my aunty ki kwanta abunki ki huta sai zuwa karfe uku saboda minti talatin zuwa awa d'aya zata kai ku "okay shikenan bari naje na d'an kwanta kafin azahar na tashi in sha allahu."tana gama fad'ar haka ta juya shi kuma ya k'arasa fice wa ya koma cikin abokinsa aka cigaba nishadin kowa ka gani fuskarsa cike take da matsanancin farinciki taya adamcy murna ,sai dai shi adamcy karara fuskrsa ta nuna yanayi na damuwa duk da daman kusan yanayin fuskarsa kenan amman kuma duk da haka akwai masu iya ganewa dan kallo d'aya amar yayi masa ya fahimta dan yana hankalce dashi da idanunshi ,ya d'an matso kusa dashi tare da yin kasa da murya ta yadda babu mai jin abinda zai fad'a yace ya kamata ka kawar da duk wata damuwa da kake ciki ka bayyana farincikinka " da kyar ya janyo numfashi ya sauke yana mai runtse idanunshi da karfi alokcin da yake jin tsokar zuciyarsa tana tattarewa waje d'aya ,acikin ranshi yake hango gagarumim bala'i da za'ayi dashi idan wani acikin yan'uwnasa yayi kokarin taka masa mata ko ci mata mutunci." Bayan kamar awa bbiyu ya mike yace yana zuwa ya sake komawa bangaren mami kai tsaye ya haye samansa tare da cire hullar kanshi sannan ya rage kayan jikinsa ya zauna yana neman layin maryama domin yaji lafiyarta ,ya kira layin ya Kai sau uku sai dai ga dukkanin alamun wayar akarshe take dan switch off ake masa ya zauna shiru tare da kamo lip's dinsa yana cizawa ahankali ahankali yana tunanin ko ya kira umma ita dai ya samu kiran ya shiga sai dai bata d'aga ba zame wa yayi yana tunani ,a yau din ya kamata ace yana cikin farinciki sai dai gabad'aya ya rasa meke masa dadi ko dan yanayin da weetheart dinsa ta nuna masa ne bai sani ba duk yadad kiran amar yake shigo wayarsa bai d'aga ba dan yana bukatar zama shiru na wani lokaci ko zai samu kanshi ." Sai bayan azahar ya samu kansa yayi wanka yayi sallah ya shirya kansa cikin wata hadaddiyar shadda milk colour ya d'aura hulla dark blue ya d'aura agaogo a tsintsiyar hannunsa tare da fesa turare ya d'auki wayarsa d'aya,yana k'ok'arin fitowa daga parlour'nsa yaji alamun za'a shigo Dan haka ya d'an ja baya kad'an yana jiran yaga Wanda zai shigo gabad'aya yanuwansa ya gani d'aya bayan d'aya suna shigo da mamaki yake kallonsu ransa a matukar 'bace yace "lafiya me kukeyi anan ?"yayi masu tamabayar yana hura hanci "kayi hakuri da yan'uwnaka adam karka ga laifinsu idan akwai mai lafiya to aunty ce "hajiya zulfa'u ta fad'a tana k'arasa shigowa d'akin ta tsaya a kusa dashi tana dubansa ." "My aunty wad'an nan ba yan'uwana bane suyi rayuwarsu nayi tawa ni tuni na ciresu acikin jerin yan'uwana "ya fad'a yana watsa masu harara tace "aa adam karka ce haka kai dai kayi hakuri kawai komai ya wuce mu dinga yiwa kanmu uzuri duniyar nan ma meye acikinta "?babu komai fa ,dole kowa sai yayiwa d'anuwansa uzuri sannna a zauna lafiya"yaya dan Allah kayi hakuri ka yafe mana munyi kuskuren kuma muna nadamar abinda mukayi kuma muna tayaka murna wannan auren Allah ya sanya alkhairi ya kuma baku zaman lafiya "inji cewar zabiba numfashi ya sauke yana kallonsu d'aya bayan d'aya acikinsu ita kad'ai ce yanayinta ya nuna nadama amamn sauran kana kallonsu kasan dole akayi masu "duk da khadija da shahida su girme maka amman kasancewarsu mata ne dole su kasance a kasanka kayi hakuri komai ya wuce ." Numfashi ya sauke ya so ya fad'a mata duk abinda suka shirya akanshi da maryama amman ya danne domin yana son ganin gudun ruwansu sai da hajiya zulfa'u ta ta'ba aunty khadija sannan tace "Allah yasanya alkhairi ".ta fad'a atakaice taja bakinta ta tsuke ,haka ma aunty shahida sannan nana hauwa'u wacce yake ganin kusan tafi kowa d'aukar zafi a zuwan k'awarta ce maryam yaji kamar ya gaura mata mari sannan yaji baasin kunbure kunburen da take masa "gashin nan gabad'ayansu sun baka hakuri ka yafe masu "shiru yayi yaki cewa uffan dan bai ji zai hakura, kuma Allah yasani bai so zuwansu a yanzu ba domin yana son ya samu damar keta masu rashin mutunci ne dan duk rashin mutuncin da suke ji yafi su iyata "kayi shiru adam suci darajata aunty khadija tayi masa wani irin mummunar kallo tana ayyana irin haukan da zai yi idan maganar rabuwarsa da wacan tsinan niyar yarinyar yazo ." shima nan take ya maida mata da irin kallon da tai masa yana furzar da iska "suci daraajata adamcy muryar hajiya zulfa'u ya sake shiga cikin kunnuwansa "shikenan ya wuce!" to na gode Allah yayi maka albarka Allah kuma ya sanya albarka a aurenka yace "ameen !"adaidai lokacin da aunty khadija ta fice daga parlour'n tana cika tana batsewa tana fita aunty Shahida ta biyo bayanta tare da nana hauwa'u d'akin ya saura daga hajiya zulfa'u sai zabiba da adamcy tsaye parlour'n yayi shiru baka Jin motsin komai sai na ac dake aikin acikinsa ya kalli zabiba dake tsaye yaga duk a tsorace take sai dai bai ce mata komai ba "lokaci na sake karatowa saura awa d'aya bari naje na k'arasa shirina zabiba tace "my aunty zan biku d'auko amarya "to shikenan zabiba hakan ma zai sake goge maku laifinku a wajen adam tayi maganar tana murmushi shi dai bai ce uhm ba bare uhm uhm har suka bar parlour'n." Kai tsaye ya fito ya samu su amar suna zauen ga plate din abinci nan a gabansu kusa da amar ya zauna yana kiran sunan Allah, hannu yasa ya dafe kanshi dashi yana fadin."bahaushe ya ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi"amar yayi murmushi kawai yana kallonsa "wallahi a gajiye nake sosai gashi bana samun bacci isasshe spoon din da ke cike da abinci mb ya kai bakinsa yana taunawa ya furta." Ka kusan sauke gajiyarka dan aikin ne agaban wannan yarinyar sai tayi juriya dan akwai tarin kalubale wanda ba kowa ne zai gane ba sai wanda ya san yadda al'amarin yake ko da yake ai tasan komai bazata baka wahala ba "duk da haka ni dai ina tausaya maryama wallahi dan wannna namjin gaske ne zaki ne akanta idan ya cafketa sai Allah da malaman gari "inji cewar amar aiko suka sa dariya "tsaki adamcy yaja yayi kamar bai san abinda suke nufi ba ." Da misalin karfe uku saura mintuna talatin ya kira layin umma inda yayi sa'ar ta d'aga yake sheida mata wad'an da zasu zo d'aukar maryama zasu taso yanzu sai dai cikin tashin hankali take fad'a masa "jikin maryama ya sake rikicewa sosai yanzu na isketa kwance tana fidda numfashi sama sama amman nasa akira doctor dan babu abinda jikinta yake fitarwa sai hucin zafi ". cikin wata irin wahalalliya murya wanda ke fallasa sirrin zuciya da gangar jiki ya furta" inna lillahi wa inna ilaihi rajiun..!"al'amarin daya janyo hankalinsu amar da mb har ma da sauran abokansa da suke tare dashi kenan suka tsura masa idanu gabad'ayansu suna kallonsa suna jiran suji abinda zai fad'a bayan wannan kalmar sai dai gani sukai ya d'auke kanshi akan su dan baya son suyi masa tamabayar da yake hangowa acikin kwayar idanunsu ." ganin haka yasa suka cigaba da abinda suke shi kuwa acan kasan zuciyarsa babu abinda yake maimaitawa sai "ya Allah ka taimakeni akan yarinyar nan da abinda ke shirin faruwa mikewa tsaye yayi kunnensa manne da wayar ya kasa cirewa yayinda k'irjinsa yayi masa bala'in nauyi yana tsananta bugawa a natse ya cire wayar yana juya ta a tafin hannunsa yana k'okarin nemawa kanshi mafuta akarshe dai ya yanke shawarar zuwa gidan batare da sanin kowa ba ya shiga motarsa baka wacce take da bakin glas ya fita ta kofar baya." Acan
Chapter 27 · 0% Book details