Sashe 52
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shahida tace "khadija ya mara akan waccan yar iska kwartuwar yarinyar daya aura "wani irin wulakantaccen kallo yayi mata sai da hantar cikinta ta kad'a cikin rashin Jin tsoro yace "shahida ki saisaita kalamanki akan matata idan ba so kike na miki rashin mutunci ba "ka min shiru ana mara mutunci kawai "mami ta fad'a a fusace tana masa kallon banza " yayayyen naka kake fad'awa haka akan wata macen banza macen da a gobe ma zaka samu wacce ta fita komai ,bari kaji kullum haihu war sababbi kyankyasa ake da zaka wani damu mutane akanta ,menene ka tsinta ajikinta da babu shi ajikin sauran mata "?sarai ya fahimci inda maganar mami ta dosa kuma dan ita uwa ce kawai zai barta ta fad'a son ranta akan maryama amman acikinsu duk wanda yayi gigi zai ga rashin mutunci "nayi amai na zuba a fuskarta ko Karen gidana ka mara akanta bare ka marar min 'ya saboda baka san ciwon kanka ba,wallahi kasa na sake tsanarta akan yadda na tsaneta dan karen gidana ya fiyye min ita albarka kai adamcy am so sorry I'm so sorry for you."ta fad'a tana dafe goshinta." "Haba aunty hakan fa ba daidai bane "kenan daidai ne shi ya d'aga hannu ya mari khadija?"Ta fad'a tana cire hannunta a goshinta ta zubawa hajiya zulfa'u idanunta "khadija ko kwanwarsa ce kinga ya dace ya mareta da aurenta bare yayarsa ce kusan shekara uku zuwa hud'u ta bashi." gasky bai kyuata ba amman kiyi hakuri dan Allah ki koma d'aki karki saka bakinki ciki al'amarin nan kiyi shiru abunki kawai ni zanji da komai "babu inda zani sai naji dalilin da yasa ya mari khadija har yake ikirarin ita ma shahida zai mata rashin mutunci saboda shi bashi da mutunci. "ke dai nace ki wuce zan miki bayani abinda suka aikata masa "babu inda zani sannan ba zan ji bayanin komai ba har sai khadija ta tashi ta rama marin da yayi mata tukuna "to ai sune basu da gaskiya dan sun aikata masa ba daidai ba akan matarsa,kuma idan su aka yiwa haka a gidan aurensu mazajensu bazasu yarda ba ,ki koma d'aki abunki kawai dan idan kikaji abinda suka masa sai kinyi Allah wadai dasu ." "komai ya faru kinga ya kamata ya mareta kuma akan matarsa "?khadija ta shi ki rama marinki ." tai magnar tana bata umarni aiko take aunty khadija ta mike tsaye "hajiya zulfa'u tace a'a gaskiya bazata rama ba ta dai yi hakuri su yafi juna komai ya wuce" ta fad'a tana tsayawa a gaban adamcy wanda yake kallon mami cikin matsanancin 'bacin rai yana jiran aunty khadija ta maresa yayi mata dukan mutuwa sai dai suyi sharia da mijinta " cikin tsananin fushi mami tace "lallai zata rama marinta ko ba yau ba idan kuwa bata rama ba ni zan rama mata "naji jeki zan shigo yanzu na fad'a miki komai mami ta juya ranta a 'bace ta shige d'akinta ".haba khadija wai me yasa kuke yin haka ne ?" "kuyi hakuri mana!"shiru sukai mata har ta gama maganarta tace adamcy ya basu hakuri "Aunty kiyi hakuri bazan iya basu hakuri ba dan bana son wani sulhu a tsakanina dasu kowa yayi rayuwarsa,suyi rayuwarsu kamar basu sani ba Nima nayi tawa da matata that's all "ko baka fad'a ba muma hakan take agaremu ko da Kai ko babu kai zamu cigaba da rayuwarmu ,sai dai ka sani bazaka ta'ba jin dadin auren yarinyar ba da kanta zata bukaci saki dan uwarta inji cewar aunty shahida," wani takaici da bak'in ciki tattare da b'acin rai ne suka taru suka dabaibaye zuciyarsa, alokacin da yake kallon aunty shahida ya dinga Jin wata irin tsanarsu a ransa kamar yasa hannu ya bugeta.daya ga hakan bazai samu ba ya dinga zuba mata harara tare da gintse fuskarsa har girarsa tana alamar tattarewa gefe guda yana ciza leb'ensa al'amari ne da yake nuna ya kai k'ololuwa wajen b'acin rai yace "karku fasa ni kuma zan nuna maku rashin imani "yana gama fad'ar haka ya fice daga parlour'n aunty khadija kam jinjina kai ta dinga yi dan ita kad'ai tasan abinda zata masa dan bazata fasa abinda tayi niyya ba."kai tsaye hajiya zulfa'u d'akin mami ta shiga inda ta isketa tsaye a gaban wardrobe dinta tana cika tana batsewa cikin sauri sauri take mata bayanin abinda ya faru mami ta bar abinda take ta zuba mata ido tana kallonta tana sauraronta cikin tsananin maamkin abinda su shahida suka aikata mata ". "Da fari ke uwa ce kiyi kokarin ki tsawatar masu sun janye kudirinsu dan adamcy ya fisu gasky dan babu wanda za'a wa haka ya d'auka ya ma yi hakuri dan haka kiyi k'ok'arin ki takawa abun burki idan kuma hakan ya gagara babu shakka zaki raba kan ya'yanki ."sai data numfasa kana ta cigaba da magana "maryama bare ce acikinsu ki ajiye tsanar da kikayi mata a gefe ki sulhuta tsakanin yaranki su koma kamar yadda suke kafin abun yafi karfinki dan alamarin ya wuce duk yadda kike tunani adamcy bakar zuciya da taurin kai su kuma taurin kai ,menene ma dalilinsu na shiga rayuwarsa tunda shi ya tabbatar min koda basu kafa mata sharadin aurensa ba zai bi duk hanyar data dace ya aureta" " menene dalilinsu na kin aurensa ko kafa mata sharadin ta auresa ta rabu da shi ?"ki zauna kiyi tunani kwata kwata su shahida basu da gasky kiyi masu magana su bar shi yaji dadin aurensa ta yaya kowacce acikinsu tana zaune a gidan mijinta lafiya tana jin dadin rayuwarta zasu damu rayuwarsa su barshi ya huta pls ."idan ba haka ba ran kowa ne zai baci dan gabadansu babu wanda bai san halinsa ba ni zan wuce saduwar alkhairi ."tana gama fad'ar haka ta juya ta fice daga d'akin ta bar mami tsaye cikin tsananin mamakin yaranta "daman sune silar da adamcy ya auri maryama ai kuwa idan haka ne sun cuceta sun Ci amanarta dan babu yadda batayi dashi ba akan ya fito ya fad'a mata yana sonta ya kasa har ma tace ya kawo mata ita ta fad'a mata yaki ." A tsaye adamcy ya iske maryama tana zariya a parlour'n tana ganinsa ta tsaya cak tana dubansa cikin tsananin tashin hankali gabad'aya yanayin ta ya sake sauyawa kana kallonta zaka fahimci bata cikin kwanciyar hankali a natse yake daga kafafunsa har ya isa inda take tsaye yana kare mata kallo itama kallonsa take zuciyarta na wani bugawa da sauri sauri kamar zata fasa k'irjinta ta fito yayinda kwalla ta cika idanunta ya kai hannu ya janyota jikinsa gaba d'aya ya rungumeta tare da matseta a faffad'an k'irjinsa nan take tsigar jikinta suka mike hatta numfashinta sai daya nemi ya d'auke sakamakon irin rungumar da yayi mata kuka ta fashe masa dashi tace"dan girman Allah yalla'ba ka sakeni bazan iya zama da yan' uwanka da mahaifiyarka ba"ya sake matseta sosai yace "bazan iya rabuwa dake ba da kinsan adadin son da nake miki da duk tsanani baza kice na rabu dake ba"ahankali ya soma tafiya daita tana rungume ajikjnsa tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki har suka shiga d'akin zanensa a tsakiyar d'akin suka tsaya yace wannan d'akin kika shigo a daren ranar da aka kawoki gidan nan muje ciki kiga abinda zai tabbatar miki da irin son da nake miki ya bud'e wani d'akin dake manne aciki, da mamaki take kallonsa har suka shiga d'akin duhu ya sak manneta ajikinsa had'e da lalubo wayarsa ya haska ya kunna wutar d'akin." Nan take haske ya haskaka koina a d'akin taga abun mamaki domin kuwa duk bangon d'akin frem din zanenta ne tun tana karama har zuwa girmanta wasu da kaya sanye ajikinta wasu kuma daga ita sai pant and bra ya kamo fuskarta ya had'e da nashi yana shakar numfashinta"kece mafarkina maryama. kece wace nake gani acikin duniyar mafarkina tun shekarun da suka gabata yanuwana kaf da mahaifi yata da abokana ke duk wani wanda yake tare dani yasan dake acikin duniyata kece wace zuciyata take da muradi kasancewa tare daita har karshen rayu wata ."Kinga gabadaya d'akin nan hotunan zanen ki ne da nake zanawa a duk lokacin da nayi mafarki dake ,kowa kallon taba'b'be dakiki mara hankali yake min abaya ,nima kaina tun ina ganin cewar ke din gaskiya ce har na dawo na fara tunanin mafarki na karya ne sai dai zuciyata ta kasa yarda da hakan kullum gani nake zaki bayyana a gareni adalilinki na fad'a rayuwa kala kala." "Adalilin tunaninki na fad'a rayuwar shan sigari adalinki na sha giya ,adalinki sweetheart ta min auren da bana so ta aura cousin dina nayi rayuwar daita batare da na ta'ba jin sonta ba acikin rayuwar da mukayi daita ta haifi khaira tunda k'aramin cikin khaira muka rabu daita wanda ya zamo silar da mahaifiyata da 'yan uwana suke jin haushina ,fansa su khadija suke son d'auka akaina,ki taimaki rayu wata ki zauna dani dan zan iya rasa raina akanki matukar kika yi kuskuren butulcewa rayuwa dani ya kamo hannuta zuwa faffad'an kirjinsa dake matsana ncin bugawa da karfi "ta'ba kiji yadda zuciyata ke beating akanki " wallahi mutuwa zanyi akanki muddin kika barni . idan kuma kinyi kuskuren guje min tabbas mutuwata zata kasance atafin hannunki dan kece rayuwata, kece faricikina kece jigon jin dadi rayuwata "yayi maganar yana sak manneta da jikinsa ."jikinta ne yayi sanyi tamkar anyi mata wanka da ruwan sanyi lallai ta jima tana wannan tunanin aranta fansa suke son d'auka akansa ya zareta ajikinsa ya tsura mata ido ." Itama kallonsa take kamar yau ta fara ganinsa tana mamaki irin girman son da yake mata kuma ta hanayr mafarki "yanzu kin yarda da irin son da nake miki ?"shiru tayi kawai tana cigaba da kallonsa "sonki daga Allah ne ban ta'ba ganinki akoina ba sai a mafarkina soyayyar ki a kullum bin jinina take tare da bugar min da zuciya a iya son da nake miki ya wuce so ruhinki nake so ba wani abu naki ba ,Ina sonki ko kina da komai ajikinki ko baki dashi ko kina da lafiya ko baki da lafiya ko kina da hankali ko baki dashi ina sonki koda zaki kasance acikin kabari zan cigaba da sonki ".hannunta ta zare