← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 94

Sashe 13

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ga mace"mikewa yayi jiki a sanyaye yace "ni zan wuce !"ya nufi hanyar fita ammar ma ya mike tare da rusunawa yayi mata sallama mami tace "Allah ya bamu alkhairi." Suna fita mami ta had'a yaranta akan waya ta sheida masu yadda sukai dashi babu wanda bai jinjinawa mami ba acikinsu domin a ganinsu tayi kokarin wajen bashi sharadin "yanzu sauran maryam in sha allahu a daren zan kirata amman kafin na kirata ku fara kiranta kusan halinta itama wani lokacin akwai taurin Kai zata iya cewa a'a ni kuma ba dan wani abu ne nake son ta koma d'akinta ba dan khaira ne banason ta girma a wani waje dabam batare da babanta ba kuma Ina ji ajikina wata rana adamcy zai duba lamarin maryam kodan darajan khaira kowa ya fad'a albarkacin bakinsa amamn banda zabiba wacce tace Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ." Mr ata kuwa zaune kawai yake cikin motar zuciyarsa cike da bakinciki ,yana faman hada numfashi ya kasa cewa "uhm bare uhmmmm amar ya gaji da shirunsa yace "dan Allah ka kwantar da hankakinka ka rage sanyawa ranka damuwa akan wannan yarinyar kalli yadda duk kabi ka dawo cikin kankanin lokaci mr ata ya waigo da kyar yabi shi da kallo sannan ya sauke wani zazzafan huci Idanunshi sun kada sunyi jawur jiyoyin kanshi sun tashi sunyi rudu rudu "amar taya kake exepecting zan iya kwantar da hankalina yau ace ko siyoni sweetheart tayi ya kamata ta bani yancina na sha iska ,yarinyar nan Allah yasani ko nayi rayuwa daita bazan iya mata adalci ba kuma Ina jin tsoron Allah ya kamani "ya karasa maganar yana jan tsaki "kai wannan maryam din na saka mu cikin bala'in "kamar dole "! "amar nace banaso abarni mana akaiwa wani yayi magana a hargitse suna isa gidansa tamkar wani zararrre ya fito daga cikin motar yana cewa "Allah ya tsinewa yayan mami gabad'aya domin duk abinda mami zatayi da shawararsu ne sune sila koma ,hannuwansa duka ya kai ya rufe idanunsa dashi "ya Allah karkasa yarinyar nan ta amince da dawowarta gareni Allah ka min rai ka taimakeni kar ta dawo rayuwata dan wallahi bazan iya adakci a tsakaninsu da maryama ba ." Mmn sudais MAR'ADAMS BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 5 Adamcy yayi shiru zaune bayan ya gama waya da umma,wani irin sanyi ke ratsa ilahirin jikinsa yanzu hankalinsa ya kanta sosai maryam bazata dawo rayuwarsa ba ga kuma maryamarsa zai mallaka tsadadden murmushin nan nasa ya bayyana akan fuskarsa yana cewa "maryama kin kusa zama tawa ta har abada"cike da shaukinta ya kamo lip's dinsa na k'asa yana cizawa ahankali ahankali yana jin nishad'i mara misaltuwa yana shigarsa ,wayarsa dake ajiye a gefensa ta fara ringing ya d'an waigo a natse yana kallon screen din wayar sunan wanda ya gani yasa ya d'aga yana "cewa "hello baba !"daga can bangaren baba babban yace "adam ya kake "Alhamdulillah baba barka da dare?"barka d'an mamansa." Adamcy yayi murmushi jin abind ya fad'a yana sosa keya "naji dadi kwarai da ka natsu ka shawo kan mahaifiyarka akan maganar aurenka ya kamata ka canza rayuwarka,rayuwar da zakayi yanzu ta samu canji kabi mahaifiyarka ahankali ku rabu lafiya domin daga lokacin dakayi rakiya aka binneta daga wannan lokacin rayuwarka ta da data yanzu ta samu canji na zahiri dana boye daga wannan lokacin zaka shiga cikin wata sabuwar rayuwar da zai zamo baka da karfi komai ,kuma komai zai iya faruwa da Kai bare Kai da kake tsananin son mahaifiyarka karka d'auka wasa duk wanda ya rasa mahaifiya kamar ya rasa duk wani jin dadin duniy ne domin kuwa ka rasa halittar da take son taga rayuwarka ta samu cigaba ,kuma ka rasa wacce zata dinga maka adduoin nasara a duk inda take a zaune ko kwance cikin sallah akoyaushe tana cikin adduar yadda saka samu nasara ne dan haka kabi mahaifiyarka sosai kayi mata duk abinda kasan zatai farinciki "Ina maka fatan alkhairi ". "na gode sosai in sha allahu zan cigaba akan yadda nake mata masha Allah daman Ina son naji a wani estate ko a wani guri zamu had'u da su iyayen yarinyar dan na Kira Zulai tace bata san a ina iyayen yarinyar suke ba, shine nace bari na kiraka naji dan in sha allahu gobe nake son mu tsara yadda zuwan namu zai kasance "?adamcy yayi shiru yana tunanin yadda zai kwatatan masu unguwarsu maryama shiyasa yaso su tare a gidan daya basu bai yana kyankyamin gidansu bane a'a saboda irin haka ne yana son ko sun fahimci diyar talakawa ce amman suga girmasu shiyasa yake son yaje yaga umma a gobe duk dai yasan lokaci ya kure masu amman dai zai san abun yi "hello kana layi kuwa adamcy ya sauke wani naunauyen numfashi sannan ya soma masa bayanin a unguwar da maryama take "yarinyar yar agage ce bayan ya gama masa bayani yace zai tura masa number wanda zasu kira idan sunje "baba babba yace "to shikenan Allah yasa albarka bari na kira babanka prof lawan shaaibu ayi tafiyar dashi ko hakan bai yi ba ?"yayi sosai na kuma gode sosai nima nayi tunanin haka Allah yasa yana k'asar "yana nan dan shekaranjiya mun had'u dashi a d'aurin auren diyar senater barau sukai sallam." Bayan da adamcy ya gama magana tsayawa yayi cak dafe da goshinsa yana furzar huci amar ya matso ya tsaya kusa dashi yana dubansa cikin tsananin kad'uwa da tashin hankali dan gabad'aya yanayinsa ya sake canzawa ya dawo tamkar mutun mutumi a tsaye,zai iya cewa wannan shine karo na biyu daya gansa cikin tsananin tashin hankali irin haka kuma duk akan maryam ."cike da tausayawa amar ya dafa kafad'anshi sannan ya soma masa magana a natse"tabbas idan har da had'in bakin 'yan uwanka za'a sake dawo da maryam cikin rayuwarka basu kyauta maka ba amman ka daure adamcy komai zai wuce dan muddin baka daure ba wani sabon tashin hankalin da rikici zaka sake janyowa kanka ." Adamcy ya sauke numfashi da karfin tare da cire hannunsa dake saman goshinsa yana girgiza ma amar kanshi sai dai bai iya cewa komai ba illa ya zuba masa rinannun idanunshi yana kallonsa yana sake jin wani sabon tashin hankali mara iyaka ,shima amar shiru yayi yana kallonsa acikin ransa yace"lallai kuwa za'a sake tafka wani sabon tashin hnkali da adamcy a karo na biyu muddin aka sake dawo masa da yarinyar nan shi kansa bai so mami ta sake saka kanta cikin wannan lamarin ba ,amman babu yadda suka iya daita duk hukuncin data yanke akansu daidai ne ,shi dai zai yi iyakar kokarinsa yaga ya bawa adamcy shawarar yayiwa mahaifiyarsa biyayya su rabu lafiya ,hakan yasa ya cigaba da magana cikin tsigar rarrashi "calm down adamcy ka share komai tunda har ka rigada ka amincewa mami zaka dawo da maryam." Muryarsa a kasalance tamkar mai koyon magana yace "dole ce tasa na amince amar ."tunda ka amince kayi fatan ya zame maka alkhairi arayuwarka da addininka"amman laifin me nayi wa sweetheart haka ?"baka mata laifin komai ba kawai dai ra'ayinta ne haka sai kayi hakuri ka daure kayiwa mahaifiyarka biyayya ku rabu lafiya".ya sake dafe goshinsa zuciyarsa na wani irin tafarfasa "amar ban san me yasa nake Jin bazan iya rayuwa da yarinyar nan ba duk da kuwa akwai wani abu a tsakaninmu,bugu da k'ari Ina ji bazan iya mata adalci ba muddin zan kasance da maryama "ya kake yin abu haka adamcy kamar ba namiji ba ?" "nafa sanka kai din jaruma ne kuma cikakken nmj ne wanda zai iya handling din mata sama da biyar in da ana aurensu bare wasu mata biyu ". shiru adamcy yayi zuciyarsa na wani irin zafi tare da barazanar tarwatsewa ."ahankali amar ya duba wayar hannunsa data fara ringin sunan madam dinsa yaga yana wayo a screen din wayar dan haka yace "adamcy ni zan wuce gida madam tayi kira amman dan Allah ka kwantar da hankalinka in sha allahu ma maryam bazata amince da hukuncin mami ba ."wannan yarinyar tasan kanta ne halan"?yayi maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "mu bari muga mai gobe amman ni Ina ji ajikina bazata amince ba"Allah yasa"!ya fad'a yana ciza lip's dinsa "ameen !"amar ya amsa yana kallonsa da kulawa yana jin kamar kar tafi ya barshi dan Allah yasani yana matukar jin adamcy aransa dan yayi masa komai arayuwarsa shiyasa shima yake tsaye a abayansa a duk halin da zai kasance .da haka sukai sallama da juna ya shiga mota aka jashi ya bar mr ata a wajen tsaye cikin tsananin tashin hankali." da kyar ya shigar da kansa parlour'nsa yana jin wani irin damuwa mara misaltuwa kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya kwanata rigingine akan gado ya d'aga kansa sama yana kallon saman d'akin yana tunanin yadda rayuwarsa ke gudana mai tattare da qalubali iri iri shi ba maraya ba amman bashi da maraba da wanda bashi da uwa sannan cikin yan'uwansa babu wanda zai nuna a yanzu yace wannan d'anuwa ne mai son shi da son farincikinsa domin da yan'uwansa da rashinsu gara babu a wajensa gara ace bashi da su zai fiyye masa samun kwanciyar hankali ." ji yayi komai ya sake dagule masa yaja numfashi ya fesar da kyar yana cewa"maryam a kullum kina cin darajan mami ne a wajena dan saboda ita kad'ai zan iya d'aga miki k'afa har ki sake dawowa kiyi rayuwa dani domin ita ce halitta mafi soyuwa a cikin zuciya ba kuma zan so nayi abinda zatayi Allah wadai dani ba duk runtse zan daure sai dai tabbas an rage min wani jin dadi ne daga cikin jin dadin da zanyi a duniya "ya dade a ringingine yana jin ciwo aransa kafin ahankali ya zame ya kwanta ya cigaba da tunanin a halin da yake ciki babu abinda yake da muradi ji kamar sautin muryar maryama sai dai sanin cewar zai iya kiranta itama ta
Chapter 13 · 0% Book details