← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 94

Sashe 19

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aure wata hargi tsatsiyar unguwa,mai cike da adarawa kala kala da 'yan cirani iri iri da 'yan sikiraf, shi kam prof lawan kasa hakuri yayi yace "kaddara aure kenan babu inda bata kai bawa,shi kuma adamcy duk tarin ya'yan manya mutane dake cikin kasar nan birjiki bai ga wacce tayi masa ba sai anan kaddararsa take ?" numfashi baba babba ya sauke kawai dan bai san ma me zai ce ba sai dai ya shiga cikin wani yanayi mai tsarkakkiya babu abinda yazo zuciyarsa kamar nuzlarsa yadda tai kulafucin son shi haka ma hindu wacce har yauzu tana mutuwar son shi dan ko bayan fitowarta daga kurku sai data samesa da maganar ya shiga cikin lamarin sai dai hakuri ya bata tare da bata misali da nuzla da yana da wannna karfin ikon to tabbas da tun lokacin da nuzla ta haukace akanshi ya dace ya bashi umarnin ya aureta .""ubangiji yasa albarka "!prof lawan ya fad'a yana jinjina kai baba babba ya amsa da"ameen !"daga haka bai k'ara cewa komai ba ya kai hannunsa baki yana shafa farin gemunsa batare da 'bata lokaci ba baba gali ya turo ataho dasu suka fito a natse kowannensu cikin shiga ta alfarma suna taku ahankali kallo d'aya zaka masu ka tabbatar da cewa wad'an din manya mutane ne ." baba gali dake tsaye a bakin massalaci cikin tsananin tashin hankali da firgici tsayuwar jiran karasowarsu tun daga nesa yake kallonsu tare da yaron daya tura idanunshi ya zuba masu gaba d'aya kwakwaluwarsa motsin kirki bayayi tun kafin su Kai ga karasowa inda yake ya tabbatar da lallai ba komai yasa maryama tayi wannan babban kumun ba sai hasaadar da suke mata hawaye ne ya cika idanunshi yayi saurin daukewa ahankali suka karaso yayinda jami'an tsaron ke biye dasu ." a mutunce ya kar'besu yana cewa "sannuku da zuwa ku biyuni ya fad'a yana juyawa da sauri sauran kad'an yayi tuntu'be dan jikinsa har rawa yake suka biyo bayansa a natse Inda kowannen su ganin yake kamar a mafarki ne wai auren adam shararren d'an kasuwan nan da kasa da duniya tasan da zamansa ne suka zo nema acikin unguwr irin nan kuma a massalaci irin wannan abun kamar almara , amman lamarin ubangiji kenan yafi gaban haka waje suka samu suka zauna ,doguwar gaisuwa suka yi fuskar malam mustapha cike da annuri yayinda fuskar baba gali take cike da matsanancin tashin hankali haka ma baba k'aramin zuciyarsa kuna take ganin Inda adamcy ya kawosu bayan sun gama gaisawa suka fara da abinda ya kawosu wato nemawa d'ansu auren diyarsu maryama "baba gali ya fara magana "ni yayan mahaifinta ne uwa d'aya uba d'aya na baku auren maryma sai dai wani hanzari ba guda ba maryama fa ta ta'ba aure kuna ganin babu wata matsala "eh to mu bamu san da wannan zance ba amman bari mu kira shi yaron muji ko yasan da zaman haka ."baba babba ya fad'a tare da ciro wayarsa ya soma kokarin Neman number adamcy kira d'aya ya d'aga yana gaishesa baba babba ya amsa sannan ya saka wayar a handsfree ta yadda kowa zai ji "adam gamu mun samu karasowa, gamu tare da yayan mahaifinta sai dai yayi wata magana ko kasan da zaman yarinyar ta ta'ba aure ?"adamcy yayi shiru zuciyarsa na dokawa da sauri sauri sai dai yayi matukar mamakin jin abinda yayan mahaifin maryama yayi to ma me kawo wannan maganar,?"adam kana jin kuwa ?"ina jinka baba maryama ko aure dubu tayi ina son aurenta haka "." Mmn sudais MAR'ADAMS BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 7 baba babba yana gama jin abinda adamcy ya fad'a ya dubi baba gali a tsanake sannan ya maida hankalin sa ga wayar da yake yace"shikenan idan mun gama zan kiraka" adamcy yace "tom!"ka ji abinda yaro yace da alamun yasan da zaman komai sai muyi fatan Allah yasa albarka, ai auren bazawara ba wani abun aibu bane yana daga cikin baiwa ta mussaman matukar zata tsare mutuncinta tasan ciwon kanta ai shikenan ." "wannan haka ne maryama kam yarinyar kirki ce wacce ta tsare mutuncin kanta ga hankali ." "Dan tana da hankalin da wata budurwa bata dashi nasan shi d'an naku shi yasan abinda ya gani atattare daita da har ya zabeta ta zamo abokiyar rayuwarsa ."inji cewar malam mustapha ." murmushi baba babba yayi" yadda kuke da tabbas akan yarinyarku haka d'anmu adam yake domin kuwa Allah yayi masa baiwa iri iri cikin farinciki sukai murmushi hannuyensu damke da juna da malam mustapha baba gali kam zuciyarsa kamar ta buga tsabar bakinciki yaso ne lokacin daya fad'a masu ta ta'ba aure daga nan komai ya rushe sai gashi abun yazo masa da bazata "ganin baba gali bai da niyyar basu ruwan sha yasa malam mustapha ya janyo katon din ruwan roba ya soma zarowa yana ajiye ma kowa a gabansa." Baba babba yace "mun gode idan zai yuwu yaron yana son a d'aura auren a lahadi ta sama "ji baba gali yayi kamar ya mutu a gurin domin kuwa da zarar an d'aura auren shikenan ta faru ta kare basu da wani sauran dabara amman dai zai nemi su d'an daga masu kafa ko nan da wata biyu ne masu zuwa alabashi kafin zuwa wannna lokacin salma tayi nasarar ruguza komai sai dai kafin yayi hanzarin yin magana ya tsinkayo dariyar malam mustapha tare da cewa "ai tunda mun bada auren maryama ga adam aure kam za'a d'aura shi in sha allahu Allah ya kai mu lahadi ta sama ,Allah kuma ya tabbatar mana da alkhairi yasa muna raye za'ayi wannan auren Allah yasa auren ya zamo abun alfahari da farinciki wa zuriarku ".Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun baba gali ya shiga furtawa daga zaunen da yake ."amman dai malam mustapha da karambani tsiya yake wannan zakewa haka kamar shine shakikinta?" maimakon ya zuba ido ya barshi yayi magana akan komai amman sai wani zakewa yake yana bare bare da rawar kai ."ameen ya hayyu ya qayyum cikin farinciki mutane dake zaune a wajen suke amsawa sannan suka ajiye wata takarda mai ruwan kasa a gabansu ". baba babba tsaf ya fahimci baba gali kamar akwai hassada atare dashi dan a zahiri ake iya hango tarin bakincikinsa wanda Ke nuna alamun bai so faruwar wannan abun alkhairin ba ."a natse suka mikawa juna hannu sukai musabaha sannan sukai sallama baba babba ya kai hannu ya d'auki roban ruwan da'aka ajiye masa wanda hakan yasa suma sauran suka d'auka suka rike har bakin inda motocinsu suke pake suka rakasu ."fuskar baba gali babu yabo babu fallasa ya kalli malam mustapha dake tsaye kusa dashi yace "kai malam mustapha haka akeyi ?"da mamaki malam mustapha ya tsaya yana kallonsa "kasani ko mu a shirye muke daga jin sunce a d'aura aure ranar lahadi ta sama sai kayi tsigil ka amince halan kai zaka yi mata kayan d'aki da sauran abubuwa ?"da wani sabon mamaki malam mustapha yake dubansa sai dai yace "ayya kayi hakuri malam gali na maka shishshigi ashe ?sai dai ina mai baka hakuri tare da neman yafiya amman na d'auka kai ma hajiya tai maka bayanin komai akan batun zuwansu da kuma bukatarsu kamar yadda ta min amman dai kayi ..."fuuuuuu baba gali ya wucesa tare da karya kwana ya nufi hanyar gida hankalinsa a matukar tashe batare daya tsaya ya karasa jin abinda malam mustapha zai fad'a ba " . Tafiya kawai yake yana surutu "ko ya salma zata yi da rayuwarta dan tun shekaranjiya da taji batun auren nan bata sake kwantar da hankalinta ba ."?yanzu haka bata gida tun safe data fita bata dawo ba bai san inda ta nufa ba ."cike da matsanancin tashin hankali ya shigo gidan kai tsaye bangaren umma ya shiga ya samu waje ya zauna akan kujera yana mata bayanin yadda sukai da iyayen adam sannan ya mika mata takarda da suka kawo yace "kudin wata kasa ne masu yawa sosai sai dai ban san ko na wace kasa bane ga shin nan na gaisuwar iyaye ne "umma tasa ta kar'ba ta d'an bud'e ciki tace "masha Allah lallai maryama tayi kai kudi ne kuwa masu yawa nima ban san ko kudin wace kasa bane hakika yau muna cikin tsananin farinciki domin kuwa abun farinciki ya samemu Alhamdulillah Alhamdulillah umma ke jerowa tana taka rawa gabad'aya ta kasa zama waje d'aya saboda tsananin farinciki." maryma kinyi hakuri kin sha wuya yau ga irin kyakkwan sakayyar da Allah yayi miki ,gali bari naje gurin auntynta kai ma dan Allah ka kira 'yan'uwanka ka sanar masu abun alkhairin daya same mu ."maryama dake zauen a d'akinta tun awanin biyu tana zaune tana zana fuskar mr ata da shigar da ya zo daita jiya ta jiyo maganar umma komai data fad'a ya samu kyakkwan mazauni acikin kwakwaluwarta"maryma kinyi hakuri kin sha wuya yau ga irin kyakkwan sakayyar da Allah yayi miki ta sake maimaitawa kanta maganr "to me hakan yake nufi ?"meke faruwa a gidan nan nasu ?" Ta yunkura ta mike tsaye ta yaye labulen d'akinta ta fito zuwa parlour'n adaidai lokacin da baba gali ya mike tsaye jiki a sanyaye ya nufi kofar fita itama umma ta biyo bayansa tare da janyo kofa maryama tayi turus tana kallon parlour'n tare da kamo yatsun hannunta tana murzawa tana tunanin abinda ya faru da har taji umma tana magana cikin tsananin murna da farinciki ,ahankali ta kai hannunta ta d'an tsutsa gefen kanta hakan nan ta tsinci kanta da jin fad'uwar gaba mai tsanani ,ta zauna akan hannun kujera tana cigaba da jin bugun zuciyarta."kusan tare umma suka jera da baba gali ya shige part dinsa ita kuma ta shiga wajen aunty fuskarta cike da tsananin farinciki mara misaltuwa ta bud'e takardar da kudin suke ciki ta nunawa aunty "ga kudin da iyayen adam suka kawo na gaisuwar iyaye ".shiru aunty tayi tana kallon kudin domin kuwa bandir din pound's ne har guda
Chapter 19 · 0% Book details