Sashe 65
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Page 22 Hankalin mami a matukar tashe ta kafeshi da idanuwanta tana dubansa tana nazarin mgnrsa at the same time kuma tana maimaitawa kanta abinda ya fad'a "ai kuwa mami sai dai kiyi hakuri ki cire wannan tunanin a ranki dan bazan ta'ba iya rabuwa daita ba, maryama ko aljanace ni ita zuciyata ta gani take so."sama da minti goma tana filla filla da maganar kafin daga bisani ta furta "mami !a fili wato sunan daya kirata dashi yanzu "yaushe rabon ya kirata da wannan sunan bama zata iya tuna when last ba.nan take mami ta nemi natsuwarta ta rasa kuma alokci d'aya ta soma jin zuciyarta kamar zata buga sakamakon fad'uwar gaban data risketa tana kallonsa ya runtse idanunshi tare da kai hannunsa zuwa goshinsa ya dafe yana furzar da iska mai zafi bayan kamar second goma ya cire hannunsa a goshinsa yana dubanta a tsanake yana tunanin abinda zai fad'a mata ."muryasa a tsarke yace "dan Allah sweetheart kiyi hakuri amman karki k'ara cewa na rabu da maryama na auro wata ." "shikenan adamcy naji na kuma gode sosai daka nuna min cewar bani da mahimmanci agurinka matarka ta fini dan haka gaka nan gata nan na bar mata kai kaje ku k'arata, kayi duk abinda kaga dama ai duk abinda ido ya gani shi ya jawa kanshi adduar ma idan kaga dama karka yi rayuwarka ce ba tawa ba "tana gama fad'ar haka taja bakinta tai shiru tana kallon wani gefe sai dai idanunwanta sun canza sosai alamun tana cikin tsananin damuwa ."sak runtse idanunshi yayi a karo na biyu yana sak dafe goshinsa "har sai zuwa yaushe zata gane mahimmanci mryama a rayuwarsa,matsayinta dabam haka zalika na maryamarsa dabam bama zai ta'ba had'a matsayinta dana maryama ba haka zalika yafi sonta akan maryama sai dai akan ya rabu da maryama ya auro wata ne a'a!dan duk wacce zai auro bazata ta'ba kai masa kamar maryama ba ."ya cire hannunsa a goshinsa ya dawo kusa daita ya zauna yana kiran sunanta in a low voice sweet heart."! "dakata.."!tai saurin katse masa hanzari ta hanyar fad'ar haka tana waigo da fuskarta ." "shiru yayi yana kallonta kamar yadda itama tai shiru tana dubansa up and down "zai fi kyau ka kirani da mamin daka kirani yanzu ko kuma zulai! "ya salam!"ya furta a saman lip's dinsa yana sauke ajiyar zuciya"sweetheart dan Allah ki fahimceni wallahi maryama dabam ce she's different daga sauran mata,maryama tana sonki kuma zaki ji dadin zama daita akan duk wata macen da zan kawo miki a matsayin matata zata ji mganrki, zata miki biyayya, za kuma ta guji duk wani abinda zai 'bata miki rai yarinya ce mai natsuwa da hankali da sanin ya kamata sannan bata san komai akan abinda kuke tunani akanta ba,totally ma bata san menene rayuwa ba.a yanzu babu abinda tasani sama dani kema kuma kinsan da haka "Idon't know and don't care about all that ni cutarwar da za'a maka kawai nake hango maka amman naga alamar baka cikin haiyacinka an rigada an gama da kai sai yadda akayi da kai." Jin abinda ta fad'a yasa ya mike tsam bai tsaya wani k'arin dogon surutu ba ya nemi hanyar step har ya kure matattakala mami na zaune a inda ya barta tana kallonsa cikin tsananin firgici sai dai shi ko juyowa bai yi ba ya cigaba da taku a natse har ya sauka ya bud'e kofa yana k'ok'arin shiga parlour'nsa yana girgiza kai dan yasan babu abd ke damun mami sai rikicin tsufa da kuma zugan ya'yanta wanda shi kuma bazai ta'ba barin tayi amfanin da zugan ya'yanta ta raba shi da matarsa ba ."a tsaye ya iske maryama tana zariya a cikin parlour'n tana ganinsa ta karaso gurinsa da sauri ta tsaya gabanta na wani irin matsanancin fad'u wa tare da kafesa da shayayyun idanunta masu d'auke da tarin tambayoyi kallo d'aya yayi mata ya d'auke idanunshi yana k'ok'arin wuceta ya shiga bedroom dinsa tayi saurin sha gabansa tana dubansa cikin tsananin tashin hankali dan yadda ya had'e fuska babu sauki ta jima bata ga yayi irin haka ba wanda hakan yasa taji wani irin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinta da zuciyarta dan jin zuciyarta take tamkar ana buga mata guduma ." loakci d'aya ta dinga jin zuciyarta na karkarwa saboda tsananin tashin hankalin da fargaban dake bin jikinta,da kyar take iya janyo numfashi saboda wahalallen yanayin data shiga runtse idanunta tayi da karfi alokacin data ji zuciyarta tana tattarewa waje d'aya acikin ranta take hango girman tashin hankalin dake shirin tun karota cikin wata irin kasalalliyar murya wanda ke fallasa asirin zuciya da gangar jiki take furta kallamar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kafin ahankali ta bud'e idanunta tace "mami tayi fad'a ko !?"ta'be bakinsa yayi yana girgiza mata kai alamun a'a! sannna ya ra'ba ta gefenta ya shige d'akinsa ."bayansa tabi da kallo tana sak jin tashin hankali from know where yana shigarta ahankali ta had'e hannuwanta waje d'aya tana cigaba da kallon kofar d'akinsa hannuwanta ta sauke tana ciza gefen lip's dinta da d'an karfi "yace mami batayi fad'a ba amman mai yasa yanayinsa ya sauya haka ?" tayi wa kanta tmbayr da bata da mai bata amsarta sai shi "lallai wani abu ya faru ko kuma mami ta fad'a masa maganar data 'bata masa rai ya dai boye mata ne "ya Allah ka bani mafuta akan wannan iftila'in dake shirin zama barazana acikin rayuwa r aurena ya Allah ka bani hakuri acikin rayuwar aurena ,ya Allah bazan iya wannan tashin hanka lin ba ka kawo min saukinsa haka tayita tsayuwa a wajen kafin daga baya jiki a sanyaye ta biyosa ta tsaya nesa kad'an dashi tana kallonsa tsaye rike da kugunsa taku uku tayi ta k'araso garesa ta tsaya tana sauke numfashi da karfi tare da kai hannunta tana k'ok'arin kamo hannunsa cikin nata ."ya zame yana furzar da iska mai zafi shiru tayi tana cigaba da dubansa tare da nazarinsa gabad'aya ya sake ba kamar sanda suka shigo gidan ba sai dai tayi tunanin ta barshi tukun nan zuwa wani lokaci amman kuma ta kasa fita daga d'akin ta samu waje ta zauna a bakin gado tana kallonsa ya soma kokarin duba camarorin gidan." a natse yayi komai ya gama tare da yin shr yana kallon saman d'akin batare daya kalli inda take zaune ba ".jikita a sanyaye ta tashi daga inda take ta dawo inda yake ta durkusa a gabansa tana kallonsa magana take son tayi masa amman tsananin tsoron yadda yanayinsa ya canza yasa ta kasa furta komai can bayan kmr minti goma ya sauko da fuskarsa ya kalleta tai masa narai narai da idanu alamun zata iya sakar masa kuka a kowani lokaci ,wani miyo daya tsaya masa a makoshi ya samu ya had'iye da kyar sannan ya mike ya soma cire kayan jikinsa juyowa tayi gabad'aya ta zuba masa ido har ya gama cirewa ya shige bathroom ya d'an jima sannna ya fito fuskarsa still a d'aure tamkar wanda akayi masa mutuwa "Allah kad'ai yasan abinda mami ta fad'a masa wanda yasa yanayinsa ya canza haka cike da sanyin jiki ta mike tsaye tana dubansa kafin ahankali ta soma d'aga kafafunta ta karaso ta tsaya abayansa bata san lokacin data masa kyakkwan runguma ta bayansa ba tana cewa "kayi hakuri dan Allah nasan mami ta maka fad'a ne saboda ni !". ahankali ya juyo tare daita ajikinsa yana sauke numfashi wanda take jin sauakrsa a fuskarta da wuyanta,tana jinsa yasa hannunwansa duka ya zareta ajikinsa still fuskar nan tashi a had'e abd ke sake d'aga mata hankali kenan duk da tasan kusan haka yanayinsa yake amman kasance warsu tare ya rage wasu abubuwa muryarsa a tsarke yace"fad'an me kike tunani zatayi akanki?"ya tambayeta yana tsareta da tsumammun idanunshi masu tsananin kashe mata sansar jiki tace "ban sani ba amman jikina ya bani fad'a ta maka akaina shiyasa yanayinka ya canza zuwa haka "ta fad'a tana sunkuyar da kanta kasa shiru yayi na second biyar kamar bazai yi magana ba dan har ta cire rai da zai sak cewa wani abu ta d'ago ahankali wanda yayi daidai da motsa lip's dinsa ahankali"cewa tayi na rabu dake na auro wata ..ai bai gama rufe bakinsa ba ta sauke wani zazzafan ajiyar zuciya tana furta kalmar inna lillahi wa inna lillahi rajiun a fili hankalinta yayi mugu mugun tashi sai dai tayi k'ok'arin danne hakan acikin zuciyarta ta shige jikinsa tana cewa "mai zai hana ka yiwa mami abinda take so!" idan kuma tana bukatar ka dawo da zabinta ne fine kayi k'ok'arin kayi haka Allah tabbatar mana da alkhairi ". bata gama rufe bakinta ba taji ya zareta ajikjnsa yana mata wani irin mugun kallo mai d'aga hankali da dagula lissafi ."itama cigaba da kallonsa tayi kafin ahankali ta sak shigewa jikinsa sake zareta yayi yace "are you out of your sense ?"ya fad'a yana pointing daidai saitin brain dinsa "I think you don't know what you're talking about,yana gama fad'ar haka ya nufi kofar fita zuwa parlour' ta biyo sa tana kokarin zama kusa dashi yace "don't set beside me please leave my side !"narai narai tayi masa da idanunta zatai magana ya d'aga mata hannu ya mike ya shige d'akinsa ya banko kofar da karfi ya kulle shiru tayi tsaye ."ita kam bata ga abinda ta fad'a wanda yayi zafi haka da har zai sa ya shiga tashin hankali ba "daga tace ya dawo da zabin mahai fiyarsa shine zai d'auki zafi tayi imani mami tana son shi da zabinta fiyye da kowace mace to mai zai hana bazai rayu daita dan ya faranta ranta ba?" kuma hakan da zai yi zai samarwa ita kanta kwanciyar hankali a gurin mami amman da yake shi mutun ne da ba'a saka shi ba'a hanashi bare a bashi shawara yayi aiki dashi gashi nan yayi fushi ." Ta isa jikin kofar ta kai hannu zata bud'e kofar sai kuma ta fasa taga gara kawai ta rabu dashi may be zuwa dare zai sauko sai dai har karfe goma shabiyu na dare idanunta biyu ta kasa runtsawa sakamakon shareta da yayi "k'aramin tsaki taja tana gyara kwanciyarta yayinda wata zuciyar take