Sashe 76
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
suna shan soyayya ,karfe hud'u daidai ya shiga wanka bayan ya fito ya tsaya kawai yana kallonta "tace me ya faru ?" nothing Ina sonki sosai dadina,gani nake kamar nafi kowani namiji dace dana sameki arayuwata wani irin nishad'i taji ,ranta yayi mata dadi "Ina sonki dayawa uwa uba zanyi kewar kayan marmarina ta d'an harare sa tana cewa "wallahi kafiye rigima"! to ai gaskiya na fad'a zanyi kewarki da abubuwan nan ya fad'a yana kallon k'irjinta sunkuyar da kanta tayi "am saying it rom the bottom of my heart nafi ko wani namiji dacen samunki ya riko hannunta yana tafiya daita acikin d'akin suna manne suna cigaba da soyewa" ita dai cikakken namiji ta aura romantic wanda kowacce mace take da burin aure kasance warsa attajiri bai hanashi jiyar da iyalinsa dadin dake cikin aure ba tare da bata farinciki ba ,abinda batayi tsammanin samu daga garesa ba shi ta iske shiyasa aure dace ne wani lokacin zaka tsammaci jin dadi a gidan aure sai ka iske matsaloli "wallahi duk sai taji bata son yayi tafiyar ya barta." ita shiryasa cikin hadadden sult blue black bayan ya gama shirinsa ya matsota kamar zai maidaita cikinsa "ni zan wuce !"ya fad'a yana kamo kuma tunta tare da sanya kwayar idanunshi cikin nata "Allah ya tsare Allah dawo min da kai lafiya dan Allah karka sha sigari har kaje ka dawo "zan sha kamar sau uku arana"ya fad'a yana had'e bakinsu waje d'aya ya d'auki kusan mintuna shabiyar yana tsotsan bakinta kamar zai cire ya wuce dashi sannan ya zare bakinsa cikin mawuyacin hali yace "muje ko !tare suka fita tana rike da wata yar karamar jakarsa shi kuma yana rike da karamar akwati a parlour'n ya ajiye akwatin hannunsa yace "muje nayi sallama da sweetheart kaje kawai zan jiranta anan bai matsa mata ba ya sa kai ita kuma ta tsaya jiran fitowarsa yayiwa mami sallama tai masa addua sosai da fatan alkhairi kamar babu abinda ke faruwa aparlour'n suka rabu byn yayi hugging dinta ta koma jikin window ta d'an yaye labulen tana kallonsa zagaye da masu tsaronsa idanunta cike da ruwan hawaye kamar ance ya kalli daidai gurin window ya hangota makale tana kallonsa suna had'a ido ta sakar masa murmushi shima murmushi yayi mata yana d'aga mata hannu yana jin kamar ya koma yace ta had'a kayanta su tafi tare itama hannu ta d'aga masa tana tsaye har sai data ga fitar jerin motocinsa sannan ta saki labulen ta koma sama cikin tsananin kewar mijinta ." ****** Wuni ranar shiru tayisa sosai tayi nisa cikin tsananin tunaninsa haka ta dinga lissafa a wanni a cewarsa five hour's zai Kai shi sai gashi har karfe shabiyu saura na dare bata ga shigowar kiransa ba sosai ta damu ta rasa abinda ke mata dadi abinci ma ta kasa ci numfashi kawai take fitarwa tana duba what's app dinta akai akai ko zata gansa online, karfe d'aya daidai sai ga kiran sa video call cike da natsuwa da zumudi ta d'aga muryarta a raunane alamun tayi kuka tai masa sallama " assalamu alaikum!"am sorry dadina !" taji sautin tautausan muryarsa ta doki dodon kunnenta"wani abu taji ya tsarga mata yana bin jijiyon jikinta ya sake kwnatar da muryar "wasu abubuwa ne suka d'an rikeni yasa bana online muryarta a raunane tace "to da fatan ka sauka lafiya?alhamdulillah nayi tunanin ko kinyi bacci?"muryarta cike da sheshekan kuka tace "na kasa bacci ! I really miss you Ina ta jin damuwa rashin ban taho dake ba nasan dole zaki damu bazaki samun natsuwa da kwanciyar hankali ba har sai kinji muryata "babu komai fa kawai dai naji hankalinta ya tashi sakama kon kace 5 hours zai kai ka sai gashi lokaci ya wuce sosai "that's means bakiyi kewata ba ?"nayi mana shiyasa hankalina y tashi "bakya son ki rasani ko ?" ta gyda masa kai tana sunkuyar da kanta." "karki damu bazaki rasani ba Ina sonki sosai "nima haka !ya fahimci abinda nima hakan yake nufi sun dade suna video call sai faman zuba hamma take alamun tana jin baccin amman kuma bata son bacci ya d'auketa yace "kasa da alamun bacci kike ji ta lumshe masa idanunta tana d'an murmushi "ki kwanta mayi waya da safe kwana d'ayan da tayi batare dashi ba taji damuwa mai tsanani Allah bacci ma da kyar take yi sai tayita juyi a gado tana kamka me jikinta domin jikin yayi missing mahadinsa Allah Allah ta dinga yi ya dawo dan d'an kwana biyun da tayi baya nan ji tayi kamar an canzata zuwa wata halitta dabam ."bayan kwana biyu da tafiyarsa maryam ta duro nan da nan gidan ya hargitse ya'yan mami suka cika gidan taja kanta ,sai dai taje tayi mata sannu da zuwa, yadda tayi tunanin zata amasa mata babu yabo babu fallasa hakan ce ta faru sauran kam dama ko amsa gaisuwarta basu yi ba tayita kallon khaira kamar tasa hannu ta d'auketa sai dai ganin yadda maryam din ke kallonta ta kasa d'aukar ta yarinyar ta rarrafo zata zo gurinta maryam tayi saurin ta d'auketa ta riketa a hannu nta ,maryama bata wani damu ba ta share ta koma sama ." Bayan kwana biyu da zuwan maryam mami ta tashi da zazzabi ita bata ma sani ba dan itama kusan zazzabin take ji da yawon tashin zuciya dan tun jiya data sauka bata sak sauka ba sai da mami tayi kwana d'aya da yini sannan tasani shima data sauka ne taji abakin masu aiki aiko bata 'bata lokaci ba ta nufi bangarenta da salla marta ta shiga d'akin mami gabad'aya yaranta suna d'akin sai dai ita mami bacci take tayi jam'i wajen gaishesu zabiba ce kawai ta amsa mata tace "Aunty zabiba ya mai jiki ?"fuskarta a sak tace" Alhamdulillah taji sauki" ta d'an matso zata k'arasa gaban gadon da mami take kwance aunty khadija tace"ke ke menene haka ina zaki ?" jikinta a sanyaye tace "zan duba mami ne" tace miki tana bukatar ki dubata ne wai ke mai uwar miji uwar mijin da batasan da zamanki ba idan baki sani ba zamanki a gidan nan yasa ta kamu da ciwo oya maza maza ki kama hanya ki ficewa mutane mai shegen shishingin tsiya ko dole sai kinyi shishigi ?"wani dan iskan ne ma ya fad'a mata ?"inji cewar aunty shahida maryama dai tayi shiru ta had'e hannuwanta waje d'aya tana sauraronsu sai dai kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana tattare da damuwa "wani d'an iskan ne zai fad'a mata daya wannan kwarton nata ." da sauri maryama ta d'ago ta kalli aunty khadija wacce kalmar ta fito daga bakinta "yanzu dan rashin imani d'anuwanta zata kira da kwarto?" "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "mami tace bata sonki bata son ko kallon fuskarki zaki wuce ne ko kuwa sai na tsinka miki mari?" ta k'arasa maganr tana kai mata duka acikinta ji kake gif wani kara maryama ta saki mai sauti tana dafe cikinta nan da nan idanunta ya cika da kwalla "wallahi kafin na rufe idona na bud'e ki bar d'akin nan shegiyar yarinya duk ma wari take ta fad'a tana toshe hanci maryama ta tsaya sanyin jiki aiko sai tasss taji saukar mari a kuncinta "oya wuce ba'a son ganinki da sauri ta fice daga d'akin tana hawaye ta koma sama tana zama kiran adamcy ya shigo bata d'aga ba har kiran ya katse wani kiran ya sake shigowa tana kokarin goge hawayenta da had'iye kukanta ta d'aga tace "hello !"dad'ina "!ya kirata da wannan sunan tace "na'am!" lafiya me ke damunki meke faruwa !?yayi mata tambayr ajere cikin tsananin tashin hankali tace "babu komai "me ya sameki kike kuka?"babu komai kefa matsalata dake kenan komai kice babu komai alhalin akwai komai ni ba mijinki bane me yasa zan dinga tamabayarki abu ki dinga ce min babu komai ".? tai shiru tana sheshekar kuka "idan ma baki fad'a min ba zan yi bincike na gano komai jin abinda ya fad'a tace "ka dawo pls mami bata da lafiya ta k'arasa maganr tana sheshekan kuka "to kuma shine kike kuka ?"tai shiru ki fad'a me ya faru kike kuka "kawai dai ganin yanayin jikin mami ne ya sani kuka" to karki damu in sha allahu zata samu lafiya ai jikin nata da sauki dan ma munyi waya d'azu da safe tai shiru tana sauraronsa "kenan ma yasan da rashin lafiyarta shine bai fad'a mata ba? kamar ance ta d'ago kanta nana hauwa'u ta gani tsaye ,sai da gabanta yayi wani irin mummunar fad'uwa ta gaugauta masa sallama "zan yi sallah idan na idar zan kiraka yace "okay ki natsu ki kwantar da hankalinki kinji in sha allahu bazan wuce satin nan ba tana sauke wayar taga nana hauwa'u ta k'arasa ta fixge wayar hannunta tana dubawa ta gani ko ta kashe ganin ta kashe ta watsa mata wani kallon banza "bana ji kina waya da yaya kina kuka ba na rantse da huwar rahmanu muddin kika fad'a masa anyi miki wani abu sai kin gwamaci mutuwa da rayuwarki,shegiya dangin mayu dangin matsafa ," "Ni ba shegiya bace da ubana kuma kaf dangina babu mayu babu matsafa ,abinda ya faru kuma ni ban fad'a masa ba amman Allah ya sani kuma Ina son kusani kuma mata ne idan kunyi aure a yanzu kuna ganin kuna cikin kwanciyar hankali kun haifi yaya mata a yanzu ku iyaye ne kuma wata rana zasuyi aure duk abinda kuka yiwa ya'yan wasu kuma zaayiwa naku .."bata gama rufe baki ba nana hauwa'u ta d'aga hannu zata sauke mata mari maryama tayi saurin rike mata hannu "karki soma wannan ganganci dan wallahi zan rama idan yayyenki sunyi min sunci lafiya to na barsu ne darajan sun girme mijina amman ke kam bazan d'auka ba bazan lamunta ba sai dai a mutu ".tana gama fad'ar haka ta sauke hannunta da karfi ta juya ta barta parlour'n tana hucin rashin samun galabar da batayi akan maryama ."maryama na shiga d'akinta ta kulle ta jingina jikinta da kofa ta sulale kasa wani sabon kuka ya kufce mata aiko ta fashe dashi nana hauwa'u ta matso jikin kofar d'akin tana bugawa da karfi" Ashe dai ke karamar mara kunya ce me yasa kika gudu baki tsaya ba,