← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 94

Sashe 72

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda daman abokiyar sheidaniya sheidaniya ce amman kisani wannan shine karo na karshe da zaki yi yunkurin taka min matata idan ba haka ba kika bari na d'aura hanuna ajikinki to fa wallahi kisani mijin ki ma bazaki sake masa amfanin komai ba arayu warsa na kuma sa yaja kunnenki ammn idan kina ganin karya ne babu abinda zai faru dan Allah kiyi kokarin da hannunki zai kai jikin maryama ke har mijinki bazan bari ba sai na d'auki mataki akanku ". "Kai yaya baka san abinda yarinyar nan tayi bane shiyasa kake fad'ar haka ".ko me tayi dan ubanki sai akace ki d'auki mataki akanta ?"baiwar uwar ki ce ko baiwar ubanki ce?" ya fad'a a fusace duk suka zuba masa idanu suna kallonsa har mami wacce jin abinda ya fad'a yasa ta tashi ta bar gurin dan ta fahimci abun nashi ya zarta tunanin ta tunda har ya kai ga zaginta da mijinta ."Adam ya isa haka in sha allahu bazasu sake ba idan kuma har suka sake ni nace ka d'auki mataki akansu amman yanzu kayi hakuri ka yafe masu "ba yafiyata zasu nema ba sun san wacce suka yi wa laifi dan sun d'auki hakinta idan bata yafe masu ba akan zargin karyar da suke mata na tana bin malamai wallahi duk sai Allah ya sakasu a wuta "aunty khadija ta zaro ido tana cewa"what !" Yace "yes wuta duk sai kun shiga "idan Allah bai samu a wuta ba ai sai kazo ka sakamu mara mutunci kawai da bai son ciwon Kansa ba "ya isa khadija duk ku taru kuyi hakuri amman dai ku fita harkar matarsa .sosai baba babba yaja masu kunne ya kuma masu nasiha sukace masa sun ji yayi masu sallama ya mike ya nufi kofar fita adamcy ya biyo shi suka jira suna tautaunawa yana sak bashi hakuri bayan ya dawo aunty khadija taj kallesa a wulakantace tare da tsaki tana cewa "aikin banza kawai malam wallahi kaji kunya ka tsaya kana hauka akan wannan yar iskar shagiyar yarinyar ko da yake an rigada an shayenka tass "wannan kuma babu ruwanki idan an shanyeni bare ni da kaina na kai bakina na sha nonsense kawai karki shiga hankali daidai nake dake "yana gama fad'ar hk ya haye sama ya barsu suna zaginsa ." "Zabiba ta kallesu d'ayan bayan d'aya tana cewa "dan girman Allah for now mu fita tsabgar matarsa kowa yaji abinda ake mata d'auka zaayi saboda ayi mata haka ne yasa mahaifiyrmu tace su tare a gidan nan , ko za'a cigaba da mata to mu bari ta tare a gidansa idan yaso sai ku cigaba ba duk da nifa ina gani mu barsu haka idan namiji ne muna nan zai nuna mata halinsu na maza yanzu duk d'aukita yake nan da kwana biyu ko asiri take masa zai daina aiki "duk shiru sukai suna sauraronta kamar maganar tayi tasiri ajikinsa sai aunty khadija tace "nifa ina zargin baki tare damu zabiba dan duk lokacin da zaayi magana akan yarinyar nan sai kin nemar mata sausauci "haba aunty khadija Ina tare daku mana amman kuma dai mu mata ne babu wacce zata so ta fuskanci irin abinda yarinyar nan take fuskanta daga garemu nan kuma parlour'n ya kaure da hayaniyarsu aunty khadija na nuna cewar idan an sake mata rainasu zatayi ita kuma zabiba ta tsaya akan sam ba haka bane adamcy iske mryama akan daddumar sallah tsaye Dan haka ya fad'a kan katifa yana sauke wani zazzafan numfashi ,tana idar wa ta had'e fuska tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa ta nike daddumar ta ajiye zata bar d'akin yace "ke ina zaki kuma ?" "Cak taja ta tsayawa batare data juyo ba sannan bata fita daga d'akin ba "zo nan !ya fad'a yana sak had'e fuska runtse idanunta tayi domin ji take kamar shine yayi mata cin fuska dan shine silar da'ake ciwa iyayenta mutunci ahankali ya mike ya karaso inda take tsaye ya had'e ta da k'irjinsa "saurin zamewa tayi tana hura masa hanci yayinda fuskarta babu digon annuri ko d'aya ya sake Kai hannu zai kamota ta goce tana d'aga masa hannu "please!" tare da sunkuyar da kanta kasa kankace idanunshi yayi yana kallonta kafin ahankali yace "ni kike d'agawa hannu ?"zan iya yin fiyye da haka akan mutunci iyayena ,zan d'auki komai amman wallahi banda wulaqanta min iyaye ,bare bazan cigaba da zama da mutu min da silarsa za'a dinga aibatan min iyayena ba "ba nace banason jin maganar rabuwar nan ba "dole kaso maganar rabuwa tunda mami bata sona kuma a gabanta ake ci min mutunci tana kallo abun ma kamar dadi yake mata sai kace ba uwa ba laifin me nayi mata data tsaneni ko ni nace karka so zabinta ?duk maganar nan da take idanunta na kasa "ni dai gaskiya na hakura kaje ka dawo da wacce take so ni kuma na k'ara gaba coz I know my right ba zan zauna ana wulaqan tani da iyayena ba dan...." "Enough maryama!" ya fad'a a matukar tsawace yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa jikinta ne ya kama rawa dan tsawa firgitata yake taja baya ahankali ta tsaya tana sak tamke fuska shima ya balain had'e fuska ahankali ya soma takowa zuwa inda take har ya karaso ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa "a natse ya soma magana "wannan matar fa duniya tace duk yadda zaki yi ki zauna lafiya daita kiyi ,daga ranar da kika sa'ba mata da gaske auren nan zai iya mutuwa kuma babu sulhu domin duk duniya bani da kamarta babu wacce ta kaita daraja saboda haka ki kiyaye karki kuskura kiyi sa'insa daita kina matar dana aura gara ki d'aure duk abinda tai miki muna shigowa d'akin ki kwasheni da mari ko ki zageni bama zan tmbyeki menene dalili ba amman akan sweetheart don't try it, haka nake kuma ba lalle ne kowa ya zama kamata ba wannan gurin ba wajen zuwanki ba ba kuma gurin fad'ar maganar da kika ga dama bace amman kinga kannena ko yayena su wad'an nan naja layi babu wani da zai sak rainaki ke kuma baki isa ki rainasu ba kina da daraja suma haka dan hk kowa ya tsaya inda yake da fatan kin gane ?tana jinsa tai masa banza tamkar ba daita yake magana ba ta juya fuskarta wani gefe tana kallon hawaye ya cika idanunta "wato ita nata iyayen ne banza ? ai kuwa wallahi bazai yuwu ba duk wacce ta sak zagin iyayenta sai ta rama uwa bata fi uwa ba haka uba bai fi uba ba ." "ko ban fad'a miki ba kinsan ni fitina ne bare na fad'a miki , ga gagara babu wanda ban yi ba kuma babu wanda ya isa akaina ga rashin ji in takaita miki banji magana ba kwata kwata na bawa mahaifiyata wahala sosai ba zan so na cigaba da bata wahala ba har kema ki shigo ciki ba ki tayani nayi mata biyayya mu rabu lafiya daita ya k'arasa maganar tare da yin shiru yana kallonta tana sheshekan kuka numfashi ya sauke alokcin ta juya ta fice ta bar masa d'akin gabad'a ya tana kuka, ya biyo bayanta ya tsaya daga inda take tsaye ya tsura mata ido yana jin yadda sautin kukanta ke ratsa kunnuwansa ahankali ya cigaba da kallon yadda ta hada kai da gwiwa sai ka ce wacce akayi ma mutuwa ya Kara taku biyu yana mata magana cikin tsigar rarrashi amman taki a haka har barci yayi awon gaba da ita sai da ya bari barcin nata yayi nisa sannan ya d'aukota tare da kwantar da ita akan gado ya shafa fuska rta yana murmushi "drama gril abu ba abu ba kuka, komai na kuka ne a gurinki" bayinta ya shiga yayi alwala yana fitowa ya shimfida sallaya ya fara sallah bayan ya idar ya haye gadon tare da shigewa cikin jikinta." motsawa tai tare da bude ido tana kallon yadda hannayenshi ke saman cikinta shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba jin bai yi yunkurin yi mata wani abu ba yasa ta koma ta cigaba da baccinta sai dai har washegari maryama taki sakar masa fuska ya kwance take akan gado sanye da doguwan riga me hannu shimi wanda bai sauka zuwa gwiwarta ba, gashi kayan sun d'an dame jikinta sun fitar mata da shep dinta, ya turo kofar tare da sallama murya can ciki ta amsa masa tare da 'bata fuska d'auke kanshi yayi ganin yadda take cika tana batsewa wayarshi ya manna a kunne bayan ya zauna akan kujera yana d'an satan kallonta tare da fadin. "taso muje ga umma!" ai da sauri ta wuntsilo har da d'an guduta, ta manta da yanayin da take ciki jin ya ambaci sunan umma wani irin hadiye miyau ya yi yana gyara zama ganin yadda k'irjinta suka motsa ga kayan sun yi bala'in amsar jikinta, gefen shi take shirin bi ta fita ya jawota ta fado jikinshi, ajiye wayar yayi a gefe tare da kura wa kirjinta ido yana sake hadiyan miyau cikin marairaicewa ta fara magana da 'yar siririyar muryanta " kace nataso muje ga umma dan Allah bari naje na ganta ."uhm ashe ba ki da wayo farat daya kin taso kina wani juya min wannan kananun abun .."ta saci kallonsa tana cewa"ni ka barni dan Allah ba na so abinda kake min !" numfashi ya sauke sannan ya d'agata tare da mikar daita ya nufi bayi a lokacin da wayarta ta d'auki kara ta k'arasa ta d'auka subai'a ce aiko murmushi ya bayyana akan fuskarta hira sosai suka yi da subai suna gama magana da ita ta fara neman number hajiya zulfa'u bugu daya ta dauka tace"diyata mara kirki"cikin sakin fuska maryama tace "mumy afuwan!to ya abubuwa ya amarci? Ina fatan ana kula min da dana ?"tace "eh !Juyowa tayi tana satar kallon shi ganin ya fito daure da towel a kugunsa laulausan gashin kirjin nan nashi suna kwance luf luf dasu abun shaawa sai data ji wani abu ya tsarga mata ta d'auke kainta tana fadi cikin rainta "shi dai ba ya gajiya da wanka sai ka ce agwagwa bini-bini yai wanka" Alhamdulillah ya gurinsu mama ki gaishe su"dawa kike waya ?"ta sharesa ta cigaba
Chapter 72 · 0% Book details