Sashe 69
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mami ya bawa maryama kwarin gwaiwar yin magana ".tace kuyi hakuri duk abinda zakuyi ya tsaya iya kaina amman karku ta'ba min mutuncin iyayena sai maganar asiri da kuke ta faman mgan akai kusani ni ba jahila bace inada ilimi bazan yiwa namiji asiri dan ya soni ba dan banga ribar me zan samu akan haka ba"yanzu ku amatsayin ku na iyaye iyaye wad'an da suke da ya'ya mata ..""ke dan ubanki waye sa'anki anan nana hauwa'u ta fad'a tana katse maryama ta hanyar fad'ar haka ." wani kallo maryama ta d'auketa dashi wanda hakan yasa nana hauwa'u ta mike tsaye tana k'okarin rufeta da duka maryama tayi sauri ta mike ta nufi kofar fita da sauri nana hauwa'u tana biye daita tana zaginta sauran taku uku tsakaninsu ta cafko maryama ta shige ta banko kofar da karfi kofar ta rufe kanta aiko tayi tayi ta bud'e kofar ta kasa dan haka tsaya a bakin kofar tana buga kofar da karfi "wato ke gaki yar iska yau sai dai karki fito yunwar cikinki ma kad'ai ta isheki amman muddin kika fito sai kin ci ubanki "maryama dake tsaye a tsakiyar parlour hawaye take zubar wa jikina na rawa " wai ke har kin isa aunty shahida tana fad'a kina fad'a wai gaki shegiya zaki fito ne yar gidan matsiyata matsefa" can sai ga aunty khadija tace "auta kofar a rufe take ne ?"shegiya matsiyaciyar yarinya ta rufe kofar amman zata ci uwarta sai dai karta fito "wallahi zaki sani tunda kika yi silar rabamu da d'anuwanmu kema zaman gidan nan sai yayi miki zafi zamuyi addua kam ya dawo haiyacinsa amman kema zaki ci ubanki ".inji cewar aunty ." khadija." Aunty khadija ta numfasa tace "auta na baki wannan aikin ki tabbatar kin lakadawa wannan yar gidan matsiyatan mugun duka "ai karki damu aunty bani kad'ai zanyi wannna aikin ba tare da sister zamu ci ubanta ai wallahi adamcy ya cucemu daya auro mana wannan yarinyar aunty khadija taja hannun nana hauwa'u suka sauka suka koma parlour'n mami alokcin mami ta fito tana cewa "ai ni ba aurenta bane damuwata a yanzu kamar yadda kuka ce ubanta d'an giya ne uwarta kuma karuwa ce wallahi wannna shine babban tashin hankalina "asalinta kenan sai dai mu d'age da addua kuma muyi maganinta Allah sarki maryama kam tana can ciki tsananin tashin hankali hannunta rike da waya tana son ta kira adamcy tana jin tsoron abinda zai biyo baya jin sun wuce yasa ta sauke naunauyen ajiyar zuciya."Duk wuni ranar a storace maryama tayi sa acikin d'akin da ta d'an ji motsi jikinta zai Kama rawa har most especially kasan mararta ta kai hannu ta dafe kasan mararta da take wani irin karkarwa shiyasa bata sauka dan karta had'u dasu daga d'akinta sai parlour'n ko abu take bukata hakura take har sanda zai dawo ta kwanta flat akan kujera dafe da mararta tana zubar da hawayen cin mutuncin iyayenta da sukai ." Karfe biyar daidai ya dawo gidan kallo d'aya yayi mata ya fahimci akwai abinda ke damunta dan ko kusa dashi bata zo ba yayi mata tambayr duniya tace babu komai kanta ke ciwo "shine ba zaki kira ki fad'a min ba?" ya fad'a yana janyota ya had'eta da jikinsa ya kai hannunsa daidai kanta normal yaji kanta sannan ya zarce da hannunsa kasan mararta yana shafawa ahankali "me kika bawa baby nah yaci ?"tai masa narai narai da idanun tana had'e fuska "nifa bana da komai "ai bazaki san kina da ba amman ni naji alamun kina da akan jijiyata "Allah bani da komai karki min mutsu mana dan rashin wayonki bazai bari ki fahimta ba, ya kai bakinsa yana tsotsa karan hancinta ta zare jikinta ta koma can nesa dashi ta tsaya ."ahankali ya taka ya sake janyota jikinsa gabad'aya ya rungumeta tare da matseta gam ajikinsa wani iri taji ajikinta nan take gabad'a ya tsigar jikinta suka mike hatta numfashinta sai daya nemi ya d'auke sakamakon irin rungumar da yayi mata "Ina son ki haifa min yara da wuri." "Bayan kana da wata !"naki nafi so !ya fad'a yana shafa mata sansar jiki "bari na baki maganin ciwon kai kafin lokacin sallah yayi wani kallo tayi masa tana shagwabe masa fuska "naki wayon tunda ka fita kaina da marata ciwo suke "yarin yar nan fa na gano ki babu abinda ke damunki so kike ki doje min kuma baki isa ba haka yayita jagwalgwalata har sai da yaji kiran sallah daga massalaci dake cikin estate din sannna ya barta ya shiga bayi ."da daddare da misalin karfe goma adamcy na zaune akan sofa ya d'aura k'afafunsa saman teble yana latsa laptop, yayinda maryma ke zaune a tsakkiyar gado ta cigaba da karatun novel din d'azu , madadin tayi murmushi saboda kashi hamsin na damuwarta ta kau amman taki sakin fuska yanzu ma tana karatun ne dan samun sausaucin abinda ke damunta sai tayi kamar ta fad'a masa sai ta danne ."shi kuwa lokaci lokaci ya kan d'ago idanunshi ya kalleta saboda gaba d'aya hankalinsa yana kanta ." shiru yayi na second biyar yana kallonta cikin rigar bacci fara sol iya gwiwarta ahankali ya d'auke idanunshi ya maida kansa ya cigaba da aikinsa da yakeyi ,sai dai kasa cigaba da aikin yayi ya taso daga shi har laptop d'in da coffee d'insa ya hawo gadon inda take rigingine itama sai ta tashi zaune sosai tana kallonsa ya zauna a gefenta tare da ajiye mug d'in hannunsa akan bed side d'in, laptop d'in kuma a saman gadon d'ayan gefensa. hannusa ya miko mata alamar tazo garesa .bata musa masa ba ta matso ya janyota gabad'aya ya had'e ta da jikinsa tare da makaleta a tsakkiyar k'afafunsa.ahankali ta zame ta kwanta ta d'ora kaina a cinyarsa daman wajen da ya fi son ta kasance kenan ya kar'bi book d'in hannuna ya ajiye a gefe, ya d'ora hannusa a saman cikinta yana sak maimaita tambayarta damuwarta "wai meke damunki ne ?"cike da sanyin jiki ta shafa sajensa shi kuma ya d'an ciza lips dinsa na kasa "miyasa wataran kike da miskilanci ne ?"tace "ni d'in?". 'ta fad'a tana nuna kainta da kallonsa'.sai wani basar dani kike inata tambayrki meke damunki ?".. "Me ka gani ne kake ta faman tambayata?" yace "abubuwa dayawa"tace to babu komai kasan wani lokaci yanayin mutun yana canzawa haka dai na yini yau ban sani ba ko dan kaina da marata dake ciwo ne "ta fad'a tana gyara kwan ciyarta ajikinsa wanda yasa shi Lumshe idanun shi , ya duk'o a hankali ya manna mata kiss mai kyau a goshinta .sannan ya dauko novel d'in yana duba shafin da take kallon kasan ido yayi mata sunkuyar da kanta tayi tare da kai hannu ta Shafa sumar kanta ta kai hannu zata kar'bi book din ya hanata yana furta sunan book din how I love to be loved,a lokuta dadama waanan book din ke debe min kewarki most especially wannan page din ya damk'a mata book din a hannu yana shafa sumar kanta aranta tace dole kaso page din tunda iskanci ne zalla amman a zahiri murmushi ta sakar masa very interesting novel "wow!"ya fad'a da d'age mata girarsa d'aya bakinta ta turo masa tana girgiza masa Kai yace kina son ki tashi kaina kenan ?"ta sake girgiza masa kai tana mur mushi shi din ma fuskarsa a sake take ta fahimci sai lokacin ya samu natsuwa , ya jawo lap top d'insa ya cigaba da aikinsa ita kuma ta zuba masa ido yana cigaba da aikinsa batare da ya kalleta ba, idonsa na kan system d'insa yace, "kallon fa ko kina bukatata ne ?" ahankali ta d'auke idanunta tana tabe baki a ranta tace "aikin ka kenan!"shima ta'be baki yayi alamar me yayi . karatu ta cigaba shima ya cigaba da aikinsa yana shan coffee time to time yayi aiki mai tsawo kafin ya saki wani ajiyar zuciya, ya kalli maryama da barci ya kwasheta hannunta rike da novel fuskarta ya shafa yana sake sakin ajiyar zuciya bayan ya gama ya duba camerorin gidan shiru yayi tare da kai yatsan hannunsa kan hakorinsa ahankali yaga duk abinda ya faru a gidan mamaki ya cika zuciyarsa hankalinsa yayi matukar tashi ganin irin gudun da maryama tayi domin ceton kanta daga nana hauwa'u ya ALLAH wannan irin tashin hankali ne haka ?"ya furta a fili yana kallonta baiwar Allah shiyasa yanayinta ya sauya zuwa damuwa amman kuma taki fad'a masa abinda aka mata "nan take zuciyarsa ta dinga masa tuttukin bakinciki ya duba agogon wayarsa karfe d'aya da wasu mintuna ta wuce Amman bazai iya hakuri har garin Allah ya waye ba number mijin aunty shahida ya kira kiran na shiga ba'a d'aga ba haka zalika ta mijin aunty khadija kira uku yayi ana na hud'u ne ya d'aga cikin bacci yace "adamcyn .."adamcy ya katse shi da sauri ta hanyar furta sunansa "kabir!wanda aka kira da haka ya mike zaune yana damke wayar hannunsa da kyau "kabir!! sau nawa na kiraka ?" yace sau biyu "ka jawa matarka kunne ta fita a hanyar matata idan ba haka ba zan d'auki mummunar mataki akanta yana gama fad'ar haka ya katse kiran ya kira hisham shima cikin sa'a ya d'aga abinda ya fad'a wa kabir shi ya fad'awa hisham ya katse wayarsa yana dafe goshinsa yana furzar da iska mai zafi ." Ya d'auki kusan mintuna talatin yana dafe da goshinsa sannan ya cire hannusa yana ciza lip's dinsa ahankali ya soma motsa bakinsa "idan kunsan wata baku san wata ba idan na daukeki muka bar kasar gabad'a ya zan ga yadda zakuyi ya k'arasa maganar yana sumbatar goshin maryama,kwanciya ya gyara mata ya ja bargo ya lullu'ba mata sannan yaje bayi ya d'auro alwala kamar yadda ya sabar ma Kansa kafin ya kwanta sai yayi alwala bayan ya fito ya kwanta a gefenta zuciyarsa na cike da tausayinta addu'a ya musu sannan yasata a jikinsa yana shafa jikinta tana jin motsinsa a jikinta ta share ta cigaba da baccint"Washegari bai nuna mata yasan komai daya faru ba sai dai bayan yayi breakfast ya gargad'eta da karta sake ta fita duk abinda take so da zarar ta danna bell masu aiki zasu zo su kawo mata ." tai shiru tana jin