← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 94

Sashe 14

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

k'ara masa damuwa akan wanda yake ciki yasa ya share ya d'aura hannu wansa duka a sama cikinsa yana sake zurfafa tunani duk abinda suka tautauna da mami babu abinda bai samu kyakkwan mazauni acikin zuciya da kwakwaluwarsa ba,duka hukuncinta biyu sun yi shock dinsa kuma sun fi tsaya masa arai zaman maryama tare daita da kuma dawowar maryam cikin rayuwarsa a karo na biyu a haka ma har gara zaman maryama akan dawo war maryam ,shi tunda mami ta sako zaman maryma tare daita yasan shirin ya'yanta ne sai dai emran bai fad'a masa akwai wannan shirin ba "to ai kuma ba komai emran zai kwashe ya fad'a maka ba "zuciyarsa ta bashi amsa da haka da kyar ya samu bacci barawo yayi awon gaba dashi a can kusan k'arshen dare." kusan tsawon kwanaki uku kenan mr ata bai fita zuwa koina ba haka zalika bai saka marayma a Idanunshi ba kuma bai nemeta ba sakamakon fushi da yayi daita sosai na rashin nemansa da batayi ba taji dalilin da yasa bai je gurinta ba kamar yadda yace mata zai koma a washegari ". Ita kuwa maryama ko ajikinta sai dai ta cigaba da zuba ido ta ga har zuwa karshen satin idan har bai zo ba tasan mahaifiyrsa taki yarda da batun aurensu ne hakan kuwa zai mata dadi domin zata cigaba da rayuwarta cikin kwanciyar hankali batare da barazana ba." bangaren ya'yan kuwa gabad'aya conference call suka had'a da maryam bayan sun gaisa sukai mata bayanin abinda mami take da bukata "shiru tayi kafin ahankali ta soma magana cike da rauni "gasky aunty shahida bana jin hakan zai yuwu dan bazan so na koma garesa naje na cigaba da zaman bauta ba ,nayi zaman rashin yanci nayi zaman da kullum za'a tashi a fad'a min bakaken maganganu ba ,Allah yasani har zuciyata yanzu bazan iya wannan zaman ba ina bukatar zaman 'yanci kamar kowace mace sai dai Ina masa fatan alkhairi a aurensa da zai yi ,ni da khaira kuma Allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi amman bazan zan sake wanan gangancin ba". "shikenan maryam munji kuma in sha allahu zamuyi mami wannan bayanin "kuyi hakuri idan har na bata maku rai ."to ya zamuyi maryam za dai mu so ki koma din tunda har mami tayi masa magana kuma ya amince da komawarki "inji cewar aunty khadija "aunty khadija ya amince ne saboda bashi da yadda zai yi dan anfi karfinsa ba wai dan son ranshi ba .."tai maganr tana jin kmr suna son dawo mata da abinda take ta kokarin binnewa ne daga cikin shafukan arayuwarta aunty shahida tace "maryam kiyi tunanin akai rayuwar khaira zaki duba a yanzu." shiru maryam tayi taki ce komai ba tabbas rayuwar khaira abar dubawa ce amman baza tayi sakacin da zata koma gurin mutumin da bai sonta bai kaunar ganin ko abinda ta haifa masa ba ,dama yana son khaira ne da sai tace zata ci darajan khaira a wajensa amman sam bata ga alamun haka ba "sister kiyi hakuri ki dawo mana dan akwai shirin da muka shirya akan yaya wannan auren nasa ba dangwamamme bane domin na wuncin gadi ne zasu rabu abinda yarinyar zata masa zai sa yaji ta fita ransa kuma kinga alokacin dole hankalinsa zai dawo gareki da khaira ." Duk sukai shiru suna jiran suji mai maryam din zata ce akan maganr da auta tayi sai dai har kusan minti goma bata ce komai ba akarshe dai zabiba ta tsoma baki dan kar suji haushin bata ce komai ba ta soma mgn wacce ba lallai ne yayi wa yan'uwan dadi ba"ni dai a wata shawarar da ku barta tunda ta nuna bata son komawa gidansa domin kuwa mai daki shi yasan inda yake masa yoyo idan dadi ta ji a gidan yaya tasani idan wahala ta sha ta sani "ni dai har kullum maryam zan baki shawara karki rayu a auren da ba'a san kima da darajarki ba, nmj idan bashi yace yana sonka ba idan duk duniyr zasu taru suna son zamanka dashi na banza ne saboda ba da mutane zakayi rayuwa ba dashi zaka rayu amman dai kiyi tunani kamar yadda suka fad'a Allah ya zaba miki abinda yafi zama alkhairi ".sun dade suna tautaunawa sannna sukai sallama daita aunty shahida tayi kokarin d'auko mami wacce take zaune a parlour'nta tayi tagumi tana tunanin adamcy tunda ya bar gidan bai sake waiwayota ba ,yayinda gefenta mai aikinta tabawa ce zaune tana mata magana cike da girmamawa sai dai zurfin da mami tai cikin tsananin tunani bai sa taji sallmar datai ba bare taji ringing din wayarta sai da tabawa ta d'an ta'bata tare da mika mata wayar ta waigo inda take da hanzari tana kallonta "me ya sameki mami kin dade zaune kina tunani "?ta tambayeta duk dai tasan tunnain ba zai wuce akan tilon d'anta ba dan duk abinda yake faruwa acikin gidan sun sani ." tabawa ta mika ma mami wayarta dake faman ringing numfashi ta sauke tana cewa" babu komai tabawa sannan ta kar'bi wayar ita kuma ta tashi ta bata waje ta amsa wayar idan ta gama ta dawo taji me zasu d'aura ahankali aunty shahida ta soma korowa mami bayanin yadda suaki da maryam "haba mai yasa maryam zatayi min haka ?ko da yake daman zuciyata ta tabbatar min da wahala ta amince, ai naji dadi shine gari a irin wahalar data sha a hannunsa ai bazata so ta sake koma wa gidansa ba ,amman babu komai dani daku bamu isa mu tsara komai ba sai abinda ubangiji ya tsara zamu jira mu bata lokaci ku kirata ku fad'a mata injina nace tayi tunani sosai akai duk abinda ta yanke ta gaugauta sanar maku ." Maryam kam bayan gama wayrta da yan'uwanta d'akinta ta shiga duk ranta babu dadi ta kwanta a kusa da khaira dake bacci ,ta zuba mata ido tana kallon yarinyarta wacce hankalinta ke kwance bata san me ake kira da damuwa ba tunani ne ya rufe zuciyarta"maryam ki duba karancin shekarun diyarki zakiyita zama haka ne har girmanta sannan kiyi aure?" ki yarda kawai ki koma ko babu komai yarinyar ki zata taso tare da mahaifinta sannan zaki zame ma adamcy karfen kafa ,ki koma ki zame masa baraza arayuwarsa yadda bai barki kinji dadin rayuwa ba kema karki bari yayi rayuwa mai dadi tare da matarsa ".wannan ganganci ne maryam karki sake kiyi wannan kuskuren life goes on ki tsira da rayuwarki datayi saura domin ki duba diyarki mikewa tayi ta fad'a bandaki." A kalla sai da mr ata ya d'auki sati guda bai je inda maryama take ba haka ita ma koda wasa bata nemansa ba wannan abu yayi masa ciwo matuka Allah yasani zuciyarsa ta fara jin tsoron kardai marayma ba son shi take ba da gaske dan zatayi auren wuncin gadi ne dashi yasa ta kawo masa kanta, shiru yayi zaune tare da tunani mai zurfi dan yau gabad'aya ko d'an sigarin da yake sha ya ragewa kanshi damuwa bai iya sha ba muryarta kawai yake son ji idan da hali ma ya sanyaya acikin kwayar idanunsa ." Maryama tana zaune suna cin abinci da umma wayarta dake gefen karfata ya fara ringing ganin karshen number ta fahimci mai kiranta wani sanyi taji ya lullubeta dan duk yadda take son ta ciresa aranta ta kasa dauriya kawai take ta d'auki wayar tare da mikewa tsaye umma wacce gabad'a ya hankalinta ke kanta ta d'an tsaida cin abincin dake gabanta tana kallonta ta nufi hanyar d'akinta domin amsa call ."a ranta tace Allah yasa adamu ne ya kira dan ta kula kwana biyu basa waya kuma bai zo ba, kullum addua take akan lamarin su ,idan akwai alkhairi a tsakaninsu Allah ya tabbatar da auren dan bata son mryama tayi biyu babu ba alhji mansor babu adam sai makiya suyi masu dariya daman auren tasan bazai masu dadi ba , kuma da za'a fasa tabbas zasu fi kowa murna ." Maryama tayi shiru bata ce masa komai ba tana sauraron yadda yake sauke numfashi ahankali natsuwa tayi sosai dan tasan tunda yayi shiru haka tabbas akwai mgn a bakinsa dan haka cikin tsigar Jan hankali tace"a koda yaushe idan naji mr ata yayi shiru koda a waya ne nasan akwai wani babban al'amari dake nuna cewar yana cikin damuwa me zai hana ka sanar dani damuwa rka "numfashi ya sauke da kyar sannan ya motsa lip's dinsa yace"maryama kenan a wasu lokutan kina bani mamaki ".shiru tayi bata sake cewa komai ba sai faman juya maganarsa take acikin ranta "tana bashi mamaki kuma ?"to wani mamki take bashi ?"jin shirun yayi yawa ne ya katse shirun ta hanyar cewa "hello kina jina kuwa ?" "Ina jinka yallabai wani mamaki nake baka "kinsan me kikayi ai ?"gasky ban sani ba dan ban san nayi maka wani abu ba"tayi maganr cikin sanyin murya tana jin tashin hankali ."shiru yayi yaki cewa komai domin dai ya fahimci raina masa hankali take son yi taya zata ce masa batasan laifin da tai masa ba "? please let me know ,"yayi shiru kawai yana ciza lip's dinsa ahankali "what did I do to you sir dan gsky ban san nayi maka wani laifi ba kuma bazan ta'ba samun natsuwa ba muddin banji laifina ba ?"".maryama tayi maganar cikin sanyi murya tana mai nuna damuwarta a fili numfashi ya sake saukewa cikin rashin bawa maganrta mahim manci yace "karki damu kanki maryama ki cigaba dama Allah ya baki duk wanda ya samu dama irin taki dole zai yi son ranshi ". Ahankali ta runtse idanunta tana cewa "dan girman Allah ka fad'a min sannan ka fad'a min damuwarka dan muryarka ta nuna kana cikin damuwa "did i toid you something is bothering me "?"no sir amman koda baka fad'a min ba sautin muryarka kad'ai ya isa ya tabbatar min da kana cikin damuwa "wani dogon numfashi ya sauke acikin kunneta har sai data d'an janye wayar a kunnenta sakamakon tsigar jikinta da suka mike yrrrrrrr ."gyara zamansa yayi tare da yin shiru yana kallon makeken tv plazama dake manne a bangon parlour'n yana son sheida mata hukumcin sweetheart yaji mai zatace "zata amince da zamanta tare da mahaifiyarsa ko kuwa?"amman dai sai
Chapter 14 · 0% Book details