Sashe 22
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iya zuwa makabarta ta ciro kwanya kan mamaci to za'a iya mata aikin da za'a fasa yanzu zaman datayi tunanin mafuta take tunda da sauran lokaci ." "manya mata guda goma daga cikin family's aka zaba domin sukai lefe koda suka isa sun sha mamaki ganin irin gidan da adamcy yazo neman aure sai dai kowannensu ya danne mamakinsa domin suyi abinda ya kai su ,an masu tarba na arziki kuma an basu tukuici mai kyau da kayayyinki snaks da'aka saba bisa alada suka juyo suka dawo gida ai kuwa ranar estate din ya d'auka ya rikice da magana ." kusan mata ba kamar maza ba dan lokacin da maza suka kawo kudin auren babu wanda yaji komai babu wanda bai tofa albarkacin bakinsa ba wasu suyi wa mami Allah ya kara ai taki ya aura cikin danginsa ta nace sai a daginta gashin bai zauna da zabinta ba kuma bai aura acikin daginsa ba, yaje waje ya kwaso talaka futuk wasu kuma shi suke wa allah ya kara ai damn karshen ruwan ido kenan ." mahaifiyar nuzlah kam kiri kiri ta fitowa mami ta fad'a mata son ranta "kin hana a auri namu gashi kina ji kina ganin an kwaso miki irin tsiya" mami dai tai shiru tayi kamar bata jita ba dan tasan gsky ta fad'a dan da tasan karshe abinda zai faru kenan da duk tasa ya auri hindu da nuzla da sultana ya rufe kofa ."ranar lahadi wanda yayi daidai ga bakwai ga October 2020 yan'uwa da abokan arziki suka hallara a babban masallaci malama mustapha dake sabon titin unguwar agege domin sheida daurin auren ADAM TARIQ ABDULLAH da MARYAMA HASSEIN akan sadaki 30 million pounds wanda ya kama thirty-eight million thirty thousand four hundred take gurin ya karad'e da lasfika domin sheidawa jama'a da suka hallara sosai wajen ya hargitse da lissafin mutane ." Mmn sudai MAR'ADAMS BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 8 Ai tun daga cikin massalacin har zuwa haraban waje inda mutane suke cike makil lasfika ya kai wa kunnuwansu shelan zunzurutun kudin sadakin da aka bayar na maryama shela tare da addua ne ya biyo bayan an gama d'aurin aure."ranar dai sabon titi wanda ada aka fi saninsa da unguwar gwagulori tasan ta kar'bi bakuntan manya manya mutane,tun daga kan 'yan kasuwa har zuwa kusoshin gwanati,'many 'yan siyasa wanda kusan gayyar ta baba babba da prof lawan shaaibu ne da uncle jay dan tun ana sauran kwana hud'u d'aurin aure prof lawan ya buga iv ya fara aikawa abokan arziki sakamakon wancan auren da'akayi baya kasar yana k'asar waje jinya haka ta bangaren baba babba da uncle jay da sauran yan'uwan adamcy maza da abokansa dan suma ba'a barsu abaya ba ,shiyasa d'aurin aure ya samu hallarta manya mutane dabam dabam wasu ma sai dai ka gansu a tv ko a jarida amman idanunka basu isa su gansu a zahiri ba ." Ahankali ango ya fito daga cikin massalaci sanye cikin fararen kaya babbar riga da yar ciki yayi kyau sosai ,yayinda abokansa ke take masa baya suka fito ,ganin fitowarsa yasa mutane suka shiga mika masa hannu domin tayasa murna sannan aka fara d'aukar hotuna ta bangarensa da kuma bangaren yan'uwan maryama,habib shine kan gaba shima ya sha fararen kaya babbar riga da yar ciki da hula fari wanda akayi mix da baki yayi kyau kamar wani ango ,sosai fuskarsa ta nuna ainihin farinciki da yake ciki shi ya dinga nuna wa adamcy sauran yan'uwa akayi hotuna sannan abokan adamcy suka biyosa aka rankayo zuwa gida inda maryama take domin ayi hotuna bisa ga al'adar mutanen lagos daga nan kuma sai su k'arasa gida inda zasu gabatar da walima tunda yace babu biki, abokansa ne suka shirya masa walima acikin estate dinsu ." kwance maryama take a cikin d'akin yaya sadam sanye cikin wani had'add'en lace fari haka komai dake sanye ajikinta fari ne tare da babbar k'awarta subai'a sai dai kallo d'aya zaka mata ka fahimci tana cikin tsananin tashin hankali sakamakon abubuwan da suka had'e mata waje d'aya ciki kuwa har da hayaniyar mutanen da suka cika gida dan ita mutunce da bata fiyye son hayaniyar mutane ba shiyasa da matukar wahala ka ganta a wajen biki ko suna yanzu ma hayani yar ce tasa ta baro sauran kawayenta dake d'akinta ta gudo d'akin yaya sadam ta kwanta ." ganin yanayinta yasa subai'a ta biyota dan tun jiya take fama da zazzafan zazzabi mai rikitarwa har sai akayi mata allura dan lalle ma da kyar aka samu akayi mata sai da subai'a ta riketa dan zazzabin ya hanata zama gurin kwanciya kawai take nema ." yau kuwa zazzabin dake jikinta ya karu duk wannan zazzabin da tashin hankali da take ciki na fargaban hayaniyar mutane ce da kuma fargaban zama cikin ahlain adamcy ne dan tasan yau ko gobe dole zata dangana da inda suke "ya rab ga baiwarka nan Allah ka taimakeni kada ka basu ikon cutar dani ."tayi mganr acikin ranta tana jin tsinkewar zuciya subai'a dake zaune kusa daita ta kai hannu ta dafa kanta wani irin zafi taji ya ratsa tafin hannunta da sauri tace "maryama wai meke faruwa ne haka ?"ji yadda kika dawo cikin kankanin lokaci kamar wacce za'ayiwa auren dole kin ki kwantar da hankalinki ko bakya son mr ata ne ?" Shiru maryama tayi tana zance zuci "subaia bazaki ta'ba gane halin da nake ciki ba da kuma halin da zan tsinci kaina ba ." dan Allah ki d'an tashi ki zauna kinsan fa yanzu angwane zasu shigo tunda gasu baba gali can da malam mustapha a parlour sun shigo kawo sadakinki."duk maganar da subai'a take mata tana fahimta daga kwance da take haka ne ma yasa ta zurma cikin duniyar tunani kala kala acikin zuciyarta tace "waye zai zo!?" ba dai wannan mai bakar zuciyar bane zai zo inda take dan tasan ma bazai zo ba dan yau kusan tsawon kwana shabiyu kenan rabon data saka shi a Idanunta fushi sosai ya d'auka daita wanda ta rasa dalilin na meye ta zuba masa ido taga iyakar gudun ruwan sa gashi har yau d'aurin aurensu bai kirata ba bama zai barta taji da damuwarta ba har sai ya Kara mata da fushinsa." "Kinji yadda jikinki yayi zafi kuwa?"subaia tayi maganar idanunta na kan fuskarta dake d'auke da tsananin damuwa ta kamo hannunta cikin nata "maryama ki fad'a min meke damunki aranki haka daya haifar miki da irin wannan damuwar? duk Wanda aka ce yau ne d'aurin aurensa muddin ba auren dole bane dole zaka ga alamun farinciki atattare dashi amman ke sam babu sai tarin damuwa? "tai maganar tana tsareta da idanuta yadda bazata iya mata karya ba ,gabanta dake fad'uwa ne ya cigaba da fad'uwa da yake ta runtse idanunta da karfi "har ga Allah bata son zama tare da mahaifiyar mr ata bare yan'uwansa da bata marmarin sake d'aura kwayar idanunta akansu ,ba dan komai ba sai dan ta horu a hannunsu tana jin tsoron sake faruwar wani abu Ina ma zai Kai ta can wani waje dabam suyi rayuwarsu daga shi sai ita dan zamanta tare da mahaifiyarsa lallai wasu abubuwan zasu faru bayan yarjejeniyar dake tsakaninta da yanuwnasa wanda bata fatan shi ." "Allah yasani tana son zama dashi ta karar da dukkanin rayuwarta dashi amman tasan hakan ba abu ne mai yuwuwa ba dole tana ji tana gani zata sake dawowa wata karamar bazawarar a shekarunta da basu wuce a shirin da uku a duniya ba ."sake runtse idanunta tayi tana jin kaunar subai'a har cikin ranta, ji take kamar ta fad'a mata halin da take ciki amman kuma bazata iya yin haka ba dan ta rigada ta saba rike sirrinta bayan umma da aunty babu mai jin damuwarta suma a haka wani lokacin bata barin su san halin da take ciki .tana tsaka da wannan tunanin taji ruwan hawaye suna zubowa daga cikin kwarnin idanunta tai saurin jan farin mayafin dake jikinta ta rufe fuskarta sosai dan kar subai'a ta ga zubar hawayenta "muryarta na rawa tace "subai'a babu komai ko me kike tunani akaina "?ina tunnain kamar bakya son auren nan tillasataki akayi ". "ko d'aya subai'a Ina so kawai dai tunani da faragaban barin gida ne ke damuna zanje na fara wata sabuwar rayuwa da wasu mutanen dabam da ban saba dasu ba kinga dole naji damuwa ."tsura mata idanu subai'a tayi sannan ta jinjina Kai still tana kallon fuskarta cikin wani bakon yanayi wanda maryama ta kasa fassarashi cikin sauki "hawaye kike gogewa maryama"maryama tai shiru tana kokarin danne kukanta ".ba wai ban yarda dake ba amman wannan maganar da kikayi sam bata gamsar dani ba dan kwayar idanunki kad'ai ta bayana min ainihin abinda ke zuciyarki cewar kina cikin damuwa mai girman gaske sai dai kisa aranki ba'a maganin matsala da sanya damuwa a rai dan haka kan iya haifar miki da wata gagarumar matsalar ta bangaren lafiyarki wanda ni kuma bazan iya jurar ganin haka ba." ta k'arasa maganar tana sake damke hannunta dake cikin nata ."jikin maryama yayi sanyi da maganganunta dan haka tai shiru ta kasa cewa komai sai dai subai'a ta cigaba da magana cikin tsigar rarrashi domin dai so take maryama ta fad'a mata damuwarta ko zata iya taimaka mata ." A natse adacmy da abokansa suka shigo cikin haraban gidan tare da habib wanda yayi gaba da sauri domin yayi masu iso zuwa bangaren umma shigowarsu ya bawa jama'ar dake tsaye a haraban gidan damar tsura masu ido cikin tsananin farin ciki yayinda wata mata dake tsaye take tamabay ta gefenta "waye angon maryama ne acikinsu dan gabad'ayansu masha Allah kusan kowa yayi Kama da ango "da alamun wancan na tsakiyar ne dan shigarsa tafi ta sauran d'aukar hankali suna tsaye baba gali da malam mustapha suka fito daga bangaren umma suna musabaha da juna adamcy kallo d'aya yayiwa baba gali ya d'auke kanshi dan babu wani girmansa da