Sashe 89
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BOOK 4 AYSHA A BAGUDO WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Page 29 "Ahankali ya kutsa kai ya shiga parlour'n bai ganta ba ,sai dai idanuwanshi suna cigaba da kallon kasa ,sosai hankalinsa ya k'ara tashi sakamakon ganin yadda jinin d'anshi ko 'yarshi dake malale a kasa ,ji yayi kwalkwaluwarsa ta soma juyawa tmkr zata tarwatse tsabar tashin hankali,take launin idanunshi suka sake kad'awa ga wani irin zafi da kirjinsa ke masa tamkar zuciyarsa zata buga ."kai tsaye d'akinta ya shiga inda ya isketa tsaye a gaban wardrobe tana fito da kayanta, cikin tsananin tashin hankali ya soma mata magana cikin d'aga murya "maryama jini ne fa ke zuba ajikinki ". ya fad'a yana huci tamkar wani zaki ,sai dai ko kallonsa bata yi ba duk da tasani ,dan tana jin dumin fitarsa ,sai dai ta cigaba da abinda take ,ta juyo ahankali ta ra'ba ta gefensa ta shigesa ta barshi nan tsaye cikin tsananin tashin hankali."ta isa inda ta ajiye karamar akwati akan gado ta zuba kayan data d'ibo tana jin wani sabon tashin hankali na shigarta ". "maryama !" ya sake kiran sunanta still bata amsa ba haka zalika bata d'ago ta kallesa ba "karki kuskura wani abu ya samu cikin jikinki ."me ye amfanin cikin da'aka tsine masa ai gara ma ya zube nima na huta,ya riko hannunta cikin nashi tayi hanzarin fixge hannunta tana cewa"bana so kaje ka cigaba da rashin mutun cinka tunda kai babu wanda ya isa yace ka bar abu ka barshi sai abinda zuciyarka ta kitsa maka amman kasani ni mryma a yau zan bar gidan nan kuma har abada na bar shi kenan bazan dawo cikinsa ba idan yaso hankalin kowa ya kwanta tunda daman nice matsalarku to zan barku ku cigaba da rayuwar ku . ya had'e fuska sosai yana cewa "wai Ina ruwanki da hukuncin dana yanke ?ina ruwana fa kace ?ta tambayesa tana tsaida abinda take ta zuba masa idanu cikin tsananin damuwa ". "Kullum kuka ake yi dani gashi yau akaina ka zartar wa yan'uwanka hukunci mai tsauri ga.." "babu ruwanki da hukuncin dana yankewa 'yanuwana yayi saurin katseta ta hanyar fad'ar haka "yanuwana ne ba naki ba dan haka babu ruwanki "okay kaga gara na bar gidan gabad'aya kuma gara cikin ya zube ba sai na koma gidanmu dashi ba dan bazan cigaba da zama da mutumin da baya d'aukar shawara yana jin haka ya zaro mata tsumammun idanunshi cikin kar karwa"wallahi wallahi kikayi gigi wani abu ya samu cikin nan zan bala'i canza miki maryama zan miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba ."ya k'ar asa maganr yana mata gargadi da yatsan hannunsa daga haka bai sak cewa komai ba ya juya fuuuuu ya bar d'akin kunnensa manne da waya."jikinta ne ya d'auki rawa sai dai bata fasa had'a kayanta ba .parlour'n ya koma yana cigaba da kiran number likita mutun d'aya daga cikin polisawan yace"yalla'ba zamu wuce. ku wuce dasu ."ya fad'a atakaice yana cigaba da neman doctor aiko suka tasasu gaba suna basu umarni ". aunty shahida tace"ita mryam shayarwa take a barta a gida mu zamu biku .adamcy najin haka ya d'ago da sauri yace"karku saurarawa kowa acikinsu ku wuce har daita"wai adamcy ko dai kaje kayi shaye shayen ka da kasa ba?ba shaye shaye nayi ba wuta na sha na rantse da Allah tunda kuka gwada min rashin imani nima zanyi daku zaku sha mamakina aiko polisawa suka soma kokarin fita dasu khaira na ganin mamar ta zata fita tasa kuka tare da rarrafawa ta biyosu aiko kukan maryam ya k'aru tana tafiya tana waigenta adamcy yasa hannu ya d'auki khaira ya rungumeta a kafadansa."mami dake zaune tana kallon sarautar Allah an tattara mata ya'ya gabad'aya an wuce dasu "ta mike tsaye tana zaro idanu waje tare da fasa ihu muryarta a tsarke tace "meye haka zan gani yau ni zulai ?"yanzu adamcy abinda zaka min kenan?"ta fad'a tana kallon inda yake tsaye yana huci gashi gabadaya jikinsa rawa yake itama mami jikinta ya d'auki rawa da sauri takarasa kusa dashi tana kallon sa da idanuwanta cike da ruwan hawaye. "yanzu sakayar dazaka min kenan adamcy ?ka rasa hukuncin da zaka d'auka sai wannan?"Sweetheart kiyi hakuri hukuncin da yakamacesu kenan kuma na d'auka kina zaune acikin gidan fa suke wulakanta min mata, baiwarsu ce ko kashe min ita zasuyi ?ya k'arasa maganr adaidai lokacin da likita ta d'aga kiransa cikin gaugauwa ya bata umarnin tazo yanzu yanzu yana katse kiran mami tace wai ma me aka mata daka damu mutane ?"kuma ko me aka mata a ganinka ya kamata kayi masu irin wannan tozarcin da auren su fa ?"ko rikonsu nake a tunanina bazaka masu haka ba bare ya'yan cikina." Adamcy dake tsaye sai faman huci yake yana fidda numfashi sai dai ya kasa cewa maminsa komai ya barta tana fad'ar duk abinda taga dama dan wallahi yasan yana bud'e bakinsa bakar mgn zai furta mata a yadda zuciya take cinsa kuma bazai so faruwar haka ba ,dan zata sak d'aukar wutar tsanar maryama ne ta k'arawa zuciyarta ta kuma ce ya zageta saboda matarsa .dan haka ya kiyin magana, hakan yasa mami ta sake Jin haushi ta d'aukesa da mari tana kwace khaira a hannunsa tace "maza maza kasa a dawo min dasu kuma a yanzu idan ba haka ba sai dai nima ka sameni a police station din ".ya zuba mata tsumammun idanunshi da suka rigada suka rine sai dai bai ce mata uffan ba kuma baya ji zai ce din kma bazai sa a dawo dasu ba sai ya nuna masu iyakarsu cikin tsananin fushi mami ta shige bangarenta rike da khaira tana shiga d'akinta ta soma neman layin baba babba ta fad'a masa abinda ya faru kai tsaye yace babu ruwansa ." bayan maryama ta gama had'a kayanta ne fa ta fara jin ciwo na ratsa mararta sosai dan haka ta shiga bayi nan fa hankalinta yayi mugun mugun tashi ganin yadda jini ke fita daga jikinta har da guda guda wani rikitaccen kuka ta fashe dashi tana d'aura hannuwanta duka a saman kanta "shi kenan na rasa cikina gashi kuma tasan tunda ya furta sai ya mata rashin mutunci tabbas bazai barta ba sai ya ci kani yarta,wani irin murd'awa mararta tayi da sauri ta kai hannuwanta duka ta dafe cikinta tana murkususun ciwon mara,rarrafe ta fara acikin bayin tana tunanin yadda zatayi ta gudu ta bar gidan kafin ya dawo ya sameta ."da kyar ta mike ta dafe bangon bayin ta dinga jan jiki ga jinin na tsiyaya ajikinta hankalinta ya sake tashi gabad'aya ta kasa amfani da komai domin tare jinin sai dai hannuta na dafe da mararta dake mata wani irin azababen ciwo .da kyar ta samu ta fito daga bayin,ta zube kasan d'akin tana sakin numfashin wahala,har lokacin jinin dake zuba a jikinta bai tsaya ba tana kuka tana kiran wayyohhl Allah cikina zan mutu muryarta da gangar jikinta duk rawa suke cikin haka ya shigo d'akin ya isketa kwance cikin jini dafe da cikinta da kyar ya iya furta sunanta da karfi. "maryama "! "meyasa kika min haka?" nace me yasa kika min haka? me yasa kika sa bakinki ?ita kuwa kuka take sosai tana jujjuya kai, yayinda hannuta duka ke kan cikinta tana murkususu ciwo kmr ranta zai fita jini kuwa sai malala yake ta kasanta bai san sanda ya buga mata tsawa yana sake furta me yasa zaki min haka maryama ?tamkar zaki ya' karaso gareta ya d'agata tsaye zai kai mata gigitaccen mari". tace dan Allah karka mareni ka barni da azabar da nake ji wani iri yaji a gabad'a ya ilahirin jikinsa wanda yasa yaji ya kasa marinta .yayinda rashin kwarin da babu ajikinta yasa tayi kasa ta zube cikin matsanancin ciwon mara da sauri ya durkusa a gabanta ya kai hannunwansa duka ya tarairayota ya manneta ajikinsa ya zuba mata idanunshi kamar zai yi kuka dishi dishi take kallonsa da idanunta da suka gama canzawa tsabar azaba."a haka doctor ta shigo ta samesu. Ahankali ta karasa gabansu tana kallonsu a fusace yace"kin ja kin tsaya,I think abd ya kawoki kenan ki duba min ita ?tace "sorry sir dama nake jira abani, a zafafe yace" ki duba min ita nasan halin da take ciki ta d'an tsugunna tare da daga hannuta tana jin yanayin numfashnta sannan ta fito da kayan aiki cikin kwarewa da iyawa gurin aikinta.ahankali tasoma hada allurar da zata mata da kyar doctor ta somu jinin dake siyaya ajikin ya tsaya ."idanun maryama a rufe suke sai dai tana jin duk taimakon da doctor take mata da maganar da adamcy yake furtawa " meyasa zaki bari damuwarki ta zubar min da ciki na ? yayinda ita kuma take furta "wayyo Allah cikina mutuwa zanyi ka tamakamin " ji yayi kamar ya zuba mata lafiyayyun marukan ko zai samu sau sauci luuuf idanunta suka rufe tana sakin numfashin sama sama ga azabar ciwon dake nukurkusanta ga azabar tashin hankalin da kalaman adamcy ke sak jefata ciki tunda take bata ta'ba ganinsa cikin yanayi makamancin na yau ba.idanunshi sun kada sunyi jawur gabadaya jikinsa babu inda baya kirma tsabar tashin hankali da yake ciki muryarsa na rawa yace" doctor cikin ya fita ko "?ya fad'a yana kai tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa." "bazan tabbatar da haka a yanzu ba sai mun dangana daita hospital zamu tabbatar da komai ta hanayr duba mahaifarta duk da ita a tunaninta a yanayin yadda ta zubar da jinin cikin ya fita sai dai wani ikon Allah,da kyar ya iya cire tafin hannushi yana kallon fuskarta hawaye ne kwance acikin kwayar idanunshi ya d'agata ya rungumeta ajikinsa muryasa na rawa yace" maryama me yasa zaki min haka ? yana tafiya yana kallon face dinta ya nufi kofar fita daita ." Suna isa hospital likita ta soma aikinta sai dai cikin kankanin lokaci ta gano cikin jikinta ya fita ta dawo d'akin da take kwance bata ga adamcy ba ta tsaya akanta tana kallonta kwance tana sauke numfashi ahankali "wasu matan dai suna da sa'a a rayuwarsu. karamar yarinyar daita amman kuga yadda tayi saa shahararren d'an kasuwar nan ke ji daita kallo d'aya zaka masa ka fahimci zallar son da yake mata tsagwaron so ne wanda babu cutarwa acikinsa