← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 94

Sashe 18

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na dawo "a dawo lafiya !" ta fad'a ataikaice fuskarta a d'aure babu annuri bare ta tambayesa inda zashi da kuma abincin da zai bukata idan ya dawo da alamun ma yau haka zata barshi ya kwana da yunwa numfashi ya sauke sannan ya fito zuwa haraban gidansu ya soma taku zuwa massalaci dake cikin estate dinsu bayan ya idar da sallah kai tsaye ATA company direbansa da masu tsaronsa suka nufa dashi bisa umarninsa ." Tun daga haraban ma'aikata yake samun gaisuwar mutane, wasu ya amsa wasu kuma ya d'aga hannu ,wasu kuma ya share a haka har ya kusan karasowa inda sagir pA dinsa yake zaune yana ganinsa ya mike tsaye da sauri yana cewa "good morning sir !?morning !"ya amsa atakaice ya shige office dinsa ya zauna yana kallon makeken table din gabansa kusan minti goma yana zaune sannan sagir yayi knocking tare da Neman izini shigo "may I coming sir ?"bayan kamar minti biyar yace "coming !"ya bashi izini ya shigo ,a natse sagir ya shiga ya tsaya a gabansa cike da girmamawa yana sake gaishesa mr ata bai d'ago ba ,bayan kamar minti goma sagir yace " sir "!mr ata ya d'ago ya kallesa a d'age alokcin da yake kokarin ajiye wani file a gabansa "sir ana bukatar saka hannuka anan." ya fad'a yana nuna masa inda zai saka hannu "mr ata bai ce komai ba ya d'auki biro yayi masa singn da zanen fuskarsa cike da girmamawa ya d'auki file din yana cewa"sir akwai wasu mutane da suke son ganawa da kai kusan kwana uku kenan suna zuwa basa samun ganinka "me yasa baka bari nasan da zaman haka ba tun kafin yau ?"im sorry sir naga kwanakin nan ne baka samun zama amman dai yanzu haka suna kasa shiru yayi na wasu mintuna har sagir ya fidda rai da zai yi magana dan har yana kokarin juyawa yaji sautin muryarsa a kasan makoshi "kace masu su dawo gobe dan yau banzo da shirin ganinsu ba akwai wanda zan gani ."okay sir ya juya da sauri ya fita kmr zai tuntsura." Karfe biyar na yammacin ranar a gidansu maryama tayi masa yana zaune a parlour tare da umma wacce farincikinta ya kasa boyuwa Allah ya sani tana tsananin kaunarsa ko d'an cikinta sai haka bata sani ba ko dan ta fahimci maryamarta na son shi ne bayan sun gaisa daita ya soma da tambayar maryama umma tace bata nan yayi shiru sai dai acikin ransa ya fara fad'a yau ma kamar jiya fita tayi to Ina take zuwa haka ?"wato ma zata iya fita yawonta zuwa Office ne bazata yi ba bare ya samu ya dinga ganinta akan time ?"kamar umma tasan abinda yake cin ransa tace "bata dade da fita ba taje nan bayan layinmu ne akwai wata yar makarantar islamiyarsu da zatai aure acikin satin nan dake tana cikin kawaye ai naso tun jiya na hanata kanwance duk da dai ba wai tana ra'ayin yi bane ita firdausi ce ta matsa mata da magiya amman bazata wani jima ba zata dawo ko a kirata ne ? ."a natse yace "a'a ki barta kawai ya fad'a tare da yin shiru umma ta mike domin kawo masa abun sha bata wani jima ba ta dawo hannunta rike da karamin tray dake d'auke da cincin da drinks, ta aje mashi akan table din gabansa tace "adamu ga cincin kaci ni nayi da kaina yayi d'an yi murmushi kana yace "na gode umma !"bayan second biyu yayi gyaran murya sannan ya soma magana "umma naso ace kun tare a gidanku kafin zuwan wannan lokacin dasu baba zasu zo amman ban sani ko kuna da dalilin ku na rashin son tarewa ba ko kuma maryama ce ke hanaku ?". umma tayi murmushi irin nasu na manya tace "sam ba maryama bace munyi magana da auntynta itace dai tace abari har ayi auren tukun shiyasa kaji mun yi maka shiru amman ba wani abu bane. numfashi ya sauke da kyar shi dai gasky ya so ace sun tare amman bashi da yadda zai yi dasu kar ya matsa su d'auka ko yana kyamkyaminsu ne ko kuma ya raina muhallinsu ne ,muryarsa a sanyaye yace "shikenan umma Allah ya nuna mana lokacin sai magana ta gaba wacce kusan itace musababin zuwana "umma tace ina sauraronka ya d'an ciza lip's dinsa na kasa yace "mahifiyata tace maryama a gidanta zata zauna amman nasan zaman na wani lokaci ne in sha allahu" umma tayi shiru tana sauraronsa domin gasky abun bai mata dadi ba zaman maryama tare da mahaifiyarsa kasancewar bata sonta amman babu yadda suka iya shi shaani aure sai anyi hakuri kuma ahankali komai zai wuce bare tasan hali maryama bada mutun ba ko da aljanu ne zata iya zama dasu "karka wani samu damuwa wannan abu ne mai kyau Allah yasa hakan ya zama alkhairi maryama bazata ki zama tare da mahaifiyarka ba ." Yaji dadi sosai daman kuma yayi masu kyakkwan zato yasan bazasu ce a'a ba "cikin 'ya'yan gidan nan kaf Allah yayiwa mryama baiwar hakuri kuma yayi mata baiwar ilimi da hankali da nutsuwa, zakayi mamaki yadda zata zauna lafiya da mahaifiyarka ,da ba dan kar na baka labarin irin rayuwar data fuskanta da irin qaddarorin da suka fuskanceta cikin ikon Allah ta cinye jarrabawarta ba ,to zaka d'auka ko dan maryama tana tawa ce yasa haka, amman gashi tsananin hakurin datayi yasa taga karshen komai wa ma zai ce ta taba fuskantar matsi da Kunci maka mancin wanda ta tsinci kanta "basani ba kota fad'a maka wanda ta fara aure ?mr ata yayi shiru yana dubanta a tsanake yana saurronta "d'an cikina maryama ta aura ?"kana ganin idan bansan nagartata ba duk yadda suke dashi zan yarda ne ?"amman hasalima nice da kaina na had'a auren saboda kyawawan hala iyanta amman dake auren ba mai daurewa bane Allah ya kar'bi abunsa dubanta kawai yake kafin ahankali yace "Allah ya jikinsa !"ya fad'a a fili yayinda a boye yace "ai mutuwarsa Itace alkhairi arayuwata daman sai wani ya rasa wani yake samu ." "ameen !"umma ta amsa tana sauke numfashi ." Suna zaune suna tautauna yadda zuwansu baba babba zai kasance a gobe maryama ta shigo sanye cikin dogon hijab har kasa kawai taga mutun zaune ,ta tsura masa ido tana kallonsa da mamaki akan fuskarta ,yayi kyau sosai cikin shigar da yayi ,shima ya d'ago ya kalleta sai daya ji wani abu ya caki zuciyarsa ,ahankali ta d'auke idanunta akanshi tana gaishesa"yallabai barka da zuwa" mr ata yana jinta yayi mata banza ."ta d'an juyo ta kallesa jin bai amsa ba taga idanunshi baya kanta yana kallon wayarsa ne yayinda fuskarsa a d'aure, maryama ta d'an tsorata amman ta danne tsoron da taji ta kalli umma "sannu da gida umma!" yauwa maryama sannu da zuwa ya firddausi take ?"tana lafiya tace a gaisheki ,ina amsawa firdausi amarya maryama ta d'an ja tsaki tana cewa "nifa umma ina ganin bazan iya kwawance nan ba dan bazan iya fita kullum ba ,gashi wai sai anje wajen agwane a ajibose bazan iya ba gsky ba ." umma tai murmushi tana duban adamcy dake zaune yana sauraronsu dan tasan za'a rina karshe bazata yi ba ."sai dai bata ce mata komai ba ." "Ina yini yallabai ?"ta sake gaishesa "lafiya !"ya amsa atakaice maryama tayi shiru tana tunanin laifin me kuma tayi masa daya canza mata ya wani had'e rai kamar yaga mutuwarsa har ma zai zo gidansu batare daya kirata ya sanar daita zai zo ba sannan yazo yana wani cika yana batsewa ". umma dai bata ce komai ba ta zuba masu ido sai dai ta lura yanayin maryama kamar bata so zuwansa ba,shima kuma yayinsa ya nuna bai ji dadin fitar da tayi ba ,jiki a sanyaye ta nufi d'akinta ."ahankali ta cire hijab dinta ta ninke ta zauna abakin gado tai shiru idanunta na kokarin zubar da hawaye tayi saurin gogewa ita kam wannan halin nasa yana matukar damunta dan dai Allah yasa tana da dauriya ne, data yarda ta bayyana masa yadda take son shi da bata san irin wulakancin da zata sha a hannunsa ba a yanzu ma da shine yake bukatarta yana mata iskancin daya ga dama Ina ga ita ke bibiyarsa ."shi kam mr ata bayan ya kar'bi number baba gali tashi yayi bai nemi maryama ba yyiwa umma sallama ya wuce .sosai maryama taso tasan me ya kawosa dan har dare tana tunanin umma zata yi mata magana akan zuwan shi amman ta share ta kasa hakuri ta tambayeta "umma wai zuwan me mr ata yayi d'azu?" umma tace" babu komai zuwa yayi mu gaisa "gaisawa kuma umma "?eh mana ko akwai wani laifi ne ?"aa "!maryama ta fad'a tana girgiza mata kai sai dai tai tsai da ranta tana tunani dan a lissafinta ya kwana biyu bai kirata ba gashi yau yazo yayi mata banza "to ke me zai dameki tunda Allah ya saukaka miki idan ma fasa aurenki yayi ai kin huta ,amman kuma ya zakiyi da son shi da sharadin yan'uwansa har washegari ranar laraba mr ata bai nemeta ba canji da mr ata yayi mata shi ya kara d'aga mata hankali ya kusan haukatata dan gabad'aya ta gama amincewa zuciyarta ta rasa shi ." ****** A yau ne su baba babba zasu samu ganawa da baba gali tare da malam mustapha a babban masallacin malam mustapha dake kan sabon titin agege had'add'un motoci jeep guda biyu tare da motocin masu tsaronsu guda hud'u wad'an da daman sun san unguwarsu maryama mr ata ya had'asu dasu ,karfe d'aya daidai suka baro estate dinsu mota d'aya baba babba ne tare prof lawan shu'aib aminin mahaifin mr ata yayinda d'ayar motar baba k'aramin ne tare da uncle jay zaune aciki sai motocin masu tsaro biyu a gaba biyu abayan da jiniya suka karaso unguwar diribobin suka yi parking a gafen titi inda mutanen unguwar suka zubawa motaocin ido suna kallon jami'an tsaronsa dake cike da kowannesu rike da bindiga .kai tsaye baba babba ya soma neman number baba gali, daga baba k'aramin har baba babba da uncle jay har ma prof lawan zance zuci suke acikin ransu da mamakin a irin unguwar da adamcy ya kawosu nema masa
Chapter 18 · 0% Book details