Sashe 2
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
so yake ki nemishi ki biye masa . Ai mami ki barmu dashi kawai muddin ya auri yarinyar nan sai munci uwarta tana son zaman gidansa zata barshi inji cewar aunty khadija duk maganar da suke ita dai zabiba kallonsu kawai take domin sun fara bata tsoro kuma bata ta ba tunanin zasu iya aikata abinda suke aikata a yanzu ba ,dan ataikaice dai sun zama masu fuska biyu a boye suna son ya aure yarinyar a fili kuma suna ki ita kam ta rasa meke damun tunanin su . Ni wallahi mamaki bani , idan ma ba an asirce mutun ba me kamar marym me zai yi da wannan yarinyar Aunty shahida ta fad a tana kallonsu zabiba ta gyra zama tace ai kuwa yarinyar bata da laifi ko bata fi maryam ba bazaa kirata da mummunar ba to sarkin yan iya tsara magana ai daman ba son maryam kike yi ba dole kiyi side din bare akanta aunty khadija ta fad a tana harararta ,ai in sha Allahu Allah zai biya sister da mafaficin alkhairi dan tayi hakuri a gidan aure bari auta duk iskancin nan nashi baki ga yadda tayita bani hakuri na barshi yayi auren nan ba mami tai maganar tana had e hannunwanta waje d aya ,Allah zai d aga darajanta a idanun duniya sai Allah ya bata wanda ya fishi nana hauwa u ta fad a idanunta na ciccikowa da kwalla wanda yasa duk jikinsu yayi sanyi hawayen nana hauwa u yasa gabad aya sai da idanunsu ya kawo kwalla sai bayan laasar sannan suka bar gidan ******* Ranar da abun ya cika kwana biyar ya bud aya daga cikin wayoyinsa domin kiran wani abokin kasuwancisa sai dai kiran amar ya shigo baya ya d aga ko gaisa wa basu yi ba ya hau shi da fad kai malam Ina ka shige ne duk ka daga hankalin mutane hankalin suwa na d aga ? wallahi mami ta shiga damuwar rashinka wai meke faruwa me ? .okay bata fad a maka abinda ya faru ba ? wallahi bata fad a ba , ka fad a min meke faruwa ? sai da ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan yayi masa bayanin komai daya faru subhanallah me yasa mami zatayi haka ? gaskiya zanje na sameta a yau din nan tayi hakuri ta barka kayi aurenka bayan sun gama waya da amar ya kira layin maryama kira d aya ta d aga k irjinta wani na irin bugawa sai dai tayi shiru tana sauke masa numfashinta , yadda tayi shiru haka shima yayi har kusan minti biyar wanda daidai wannan lokacin da suke waya mami ta kira wani jami a wanda ta tabbatar da shine kawai zai iya binciko mata inda adamcy yake bayan ya daga suka gaisa ta sanar masa da bukatarta a take jami in ya tabbatar mata da lallai adamcy yana kasar dan yanzu haka ya gama waya da amar sannan yana kan waya da wata number mai sunan mryma hussein . katse wayar kawai mami tayi batare da sun qarasa maganar tasu ba sannan bata tsaya tasan a wani location yake ba wato ma zai har yana iya cigaba da rayuwarsa batare daya damu da halin da zata shiga akanshi ba, sosai ranta ya baci haka zalika sosai taji tsanar maryama ta sake ninkuwa acikin ranta Kira wayar amar tayi tace yazo yanzu yanzu tana nemansa yace okay mami daman gani ina kan hanyar zuwa gurinki muyi wata magana amar na gama karasowa ko gaisawar kirki mami bata bari sunyi ba ta rufesa da fad wallahi amar ka bani mamaki yanzu da had in bakinka adamcy ya bar gidan nan ,a matukar tsorace yace wallahi aa mami ba da had in bakina bane nima sai yau na samesa a waya duk tsawon kwanakin nan ban san inda yake ba sannan ban samesa a waya ba sai yau tai shiru bayan kmr second biyu ta numfasa tace ya fad a maka abinda yayi min dan nasan tunda kunyi waya zai fad a maka ? shiru yayi dan duk a tsorace yake daita . Adamcy yayi min mummunar bazatar da bazan ta ba sausauta masa ba subhanallah mami wani mummunar bazata ce haka ? ammar ya fad a haka da sauri dan bai d auka ta kawo maryama bace ,ta girgiza k afarta ta cigaba da magana yazo min da wannan yarinyar data kasance ma aikaciya agaresa amatsayin matar da zai aura. naunauyen ajiyar zuciya amar ya sauke yace maryama tace yayi kyau ashe har sunanta ma kasani? amm mami maryama tayi . .. dakata amar ka saurareni da kyau kaje ka binciko min menene asalinta da labarin ta kuma wannan ya zama sirri a tsakaninmu da kai bance adamcy ya sani ba ,shafa sumar kanshi yayi yace mami na d an jima da sanin maryama abu domin tayi aiki a karkshina ,abu na gaba mami maryama ba diyar kowa bace asalinsu talakawa ne futuk wanda a halin yanzu da aikin maryama suka dogara ,amman mami bai fad a miki cewar maryama yarinyar fa mafarkinsa ce ? na fahimci haka a ranar da yayi min mummunar bazata daita abinda yayi min ne yasa zan datse abinda ke tsakaninsa daita ta hanyarsa hanashi mallakatarta shima ya dandani dacin da muka dade muna ji akansa , wai a gaban danuwana adamcy yayi min yankar qauna ya tozartani Ina ne gidansu da maryama zanje gidan da kaina ? shiru yayi yana kallonta da bayayyanen tsoro akan fuskarsa ko zaka ce min bakassni ba tarihinta kawai kasani ? har ya girgiza mata kai sai kuma ya gyad a mata kai alamun ya sani okay tashi muje ka kai ni gidansu inna lillahi mami dan girman Allah kiyi hakuri karki je gidansu ,ki fad a min abinda kike so ayi a yanzu yanzu zaayi miki shi gbdy ya manta da abinda ya kawosa . bana bukatar komai gidansu kawai nake son zuwa .ammar bai san sanda ya durkusa agaban mami ya fara rokonta mami bamu sanki da haka ba ,kowa zai bud e baki alkhairinki yake fad a yanzu ma nasan laifin adamcy ne ya shafi maryama wallahi mami yarinyar mutunci ce maryama .duk mutuncinta ta Kai maryam dina? shiru ammar yayi yana kallonta da mamaki tambayerka nake ta kai maryam dina mutunci ? still dai shiru yayi ko da yake da kai ake shirya komai tunda gashi har kasan gidansu daman maryam ta fad a min akwai yarinyar da kayita kokarin had a shi daita .ammar ya dukar da kanshi k asa yana sake bata hakuri tabbas gsky maryam ta fad a ammna ba wata yarinya bace face maryama saboda ni na fara ganinta batare daya sa inda take ba hasalima tun kafin tayi aure naso nayi masa surprise daita sai dai girman kansa yasa ya kaga ammar bana son jin wani dogon turanci lallai ko ka Kai ni ko baka kaini gidansu ba zan nemo gidansu da kaina kuma wallahi zan bawa adamcy mamakin da bai ta ba expecting daga gareni ba tashi ka wuce na sallameka dan Allah mami .. nace kaje kawai bana son jin komai daga bakinka jiki a sanyaye ammar ya mike ya nufi kofar fita yana waiwaiyen mami wacce ta d auke idanunta akanshi tana kallon wani waje tana girgiza kafarta d aya . Yana fita ya kira layin mr ata da suka waya yaji number switchoff dan haka yayi tunanin tura masa sako akan yadda sukai da mami bangaren mami kuwa bayan fitar amar madam some ta kira bayan ta d aga kiran da girmamawa tace ki turo min da address din yarinyar nan maryama da number wayarta madam some tace okay ma ko kuna tare daita ne ? no ma ta kwana biyu bata zuwa aiki kamar ta ajiye aikin ne dai bamu sani ba duk dai bata rubuto mana latter ajiye aiki ba shikenan ki turo min yanzu yanzu okay ma ! mami ta katse kiran ta zauna tana jiran madam some tare da d aga kanta sama tana tunanin da jin zafin kaurace mata da adamcy yayi akan mace bayan second biyar taji shigowar sako wayarta ta duba taga sakon some ne dan haka ta soma Neman number maryama wacce ke duke abayan d akinta jikinta sanye da wata yar riga baka mai gajeren hannu da zani tana wanke kayan umma taji wayarta tana ringing da sauri ta cire hannun ta acikin ruwan wanki ta d auki d aya daga cikin rigunan umma mai dotti ta goge hannunta sannan ta d auki wayar tana dubawa dan a tunaninta mr ata ne sai dai taga sa banin haka domin kuwa wata bakuwar number ta gani tana yawo a screen din wayar . shiru tayi tana tunanin d aga kiran,bata d aga kiran ba har kiran ya katse wani kiran ya sake shigowa yana daf da katsewa ne tayi kundunbala ta d aga tare da yin sallama cikin sanyayyiyar muryarta mai cike da natsuwa sannan tayi shiru. madadin a amsa mata sallamarta sai taji murya wacce babu tantama ta ta ba jin muryar arayuwarta ke Ina adamcy yace miki yake ? gyara tsayuwa maryama tayi cikin tsananin tashin hankali da matsanancin firgici da tsoro dan take ta fahimci muryar sweetheart din mr ata ce akan layi muryata na rawa cike da ladabi tace Ina yini ma ! lafiya ! ta amsa mata atakaice tana sake tamabayrta wallahi mumy ban sani ba bai fad a min inda yake ba .karya kike kin sani dan kunyi waya dashi a yau din nan zaki ce bai fad a miki inda yake ba ? maryama tayi shiru zuciyarta na karkarwa da sake shiga mummunar tashin hankalin yadda tasan sunyi waya kece mutun ta qarshe da kukayi waya dashi idan wani abu ya samu yarona bazan barki ba ta fad a cike da tsawa nan take fad uwar da gaban maryama yake ya qaru ta fara zazzare idanu kuma take ta fahimci hanayr data bi tasan sunyi waya . jikinta na karkarwa inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta shiga furtawa yau kwanaki biyar kenan ban saka shi acikin kwayar idanuna ba sannan bai kirani ba abinda bai ta ba faruwa ba kenan duk yadda zai yi fushi tabbass zai nemi inda nake