← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 94

Sashe 25

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin nashi ya fara tafiya daita ta turje." Yace "da kyau ki cigaba da nuna min kina da sauran kuzari ajikinki wanda hakan zai samarwa gangar jikina karsashi da mazantaka ."bata san sanda ta zabga masa wata katuwar harara ba " Yace "na gode da wannan kallon i really miss it ko zan sake samun wani kallon irinsa ?tai shiru tana maida hawayenta tare da hura masa hanci ita dai ta shiga ukunta Allah yasa tayi tsawon rai a hannunsa "da kallon nan da hawayenki su kad'ai suna wadatar da zuciyar adam da irin zunzuruntun kaunar da kike masa har ta motsa baki zata bashi amsa suka jiyo sallamar subai'a da alamun tana son shigowa d'akin ne bai janye jikinsa ba sai itace ta d'an matsa baya tare da amsa sallamar tace "shigo !"ta d'auki dan kwa linta ta d'aura ta jingina jikinta da bangon d'akin adaidai lokcin subai'a ta shigo ta iskesu tsaye". Cike da girmamawa tace "sir wai suna jiranka .""okay !" ya fad'a atakaice sannna ya kalli mryma tare da yin kusa daita yayi mata mgn cikin rad'a "ni zan wuce anjima kad'an motocin zasu zo d'aukarki dan Allah ki taimakeni ki cire duk wani tsoro da damuwa aranki ki ajiye su a gidan umma kizo min fresh". yana mata magana subai'a na d'aukar su video batare da saninsu ba dan sunyi mata kyau sosai cikin shigar fararen kaya ."ahankali mr ata ya juyo alamun zai wuce tayi sauri tace "yallabai dan Allah bari nayi maku hoto kafin ka wuce "shiru yayi kamar yace mata no sai kuma ya tsaya ya matso kusa da maryama wani zirrrr taji na shocking kamar yana jona mata wutar lantarki.tayi masu hotuna masu kyau sannan yasa kai ya fice daga d'akin . " a parlour ya iske umma tsaye yana kokarin yi mata sallama tace "adamu tsaya ayi mana hoto babu yadda ya iya dan shi din ba mutun ne mai son yin hoto ba ,yaja tsaya umma ta kwalla wa subai'a kira ta k'araso da saurin dan daman tana kan fitowa parlour'n ne "subai'a maryama zata iya fitowa kuwa?"zata iya dan taji ssuki "to maza kirata kuzo tare yanzu hoto zaayi mana ,kice nace karta ' batawa mana lokaci da wannan sanyin nata .subai'a tace "to !tare da juya wa da sauri ta nufi d'akin tare suka dawo daita cike da sanyi jiki ganinsa yasa gabanta ya fad'i dan ta d'auka ya rigada ya wuce ,mutane na ganinta suka hau washe baki suna kiranta da amarya amarya kin sha kanshi ita dai bata iya cewa komai ba dan gabad'aya jikinta a sanyaye yake umma tace subai'a ta kira mai hoton dasu adamcy suka taho dashi tace to bata wani jima ba suka shigo tare ."umma ta shiga tsakiyar su aka d'aukesu bayan an d'aukesu tace a d'auki maryama da adamcy ta tsaida maryama a kusa dashi jikinsu na haduwa wani irin shock ne ya sake janta kamar na d'azu wanda ba ita kad'ai taji ba har shi ma yaji abinda taji ana gama d'aukarsu Itace ta soma kokarin janye jikinta daga nashi dan har wani rawa rawa jikinta yake ya sa kai ya nufi kofar fita bayansa tabi da kallo ." Yana da matukar kyau bare na yau kyau din ya fita dabam har bata san yadda zata musalta ba shadar dake jikinsa tayi matukar karbar jikinsa ga wani kamshi da yake zubawa gabad'aya kamshin turarensa ya mamaye parlour'n ahankali zuciyarta ta dinga bugawa tamkar zata fasa kirjinta sai dai a duk sanda ta tuna yan'uwan sa da mahaifiyarsa sai taji komai ya tsaya mata dan bata san wani irin aure tayi ba mai dorewa ne ko kuma na wuncin gadi ne ?zata so ace na har abada ne amman tasan hakan ba mai yuwu bane jikinta yayi matsefar sanyi har ma ya kama rawa babu shiri ta dafe bango parlour'n domin shi yafi kusa daita sosai idanun subai'a yake kanta t ai saurin rikota tana kallonta da tsananin mamaki ." a haraban gidan ya iske abokansa tsaye aiko suna ganinsa suka hau masa dariya tare da shakiyanci shawal yace "gabad'aya zuciyarka ta gama fallasaka abokina "hisham yace "wallahi kana kallonsa kasan hannun yake "wata dariya suka sa kallonsu kawai yayi sannan yayi gaba abunsa nan take wasu daga cikin masu tsaronsa suka zagayesa yayinda wasu suke tare da sauran abokansa dole tasa suka biyosa har suka karaso bakin titi murmushin taya d'an kuma abokinsu farinciki suke inda aka bud'e masa gidan baya ya shiga ya zauna amar ya zagaya ya zauna a d'ayan bangarensa akaja su suka bar unguwar ." Subai'a ta kalli maryama da jikinta ke rawa ta rikota zata nufi d'akin yaya sadam daita sai dai tuno maganarsa yasa tace"subai'a mu shiga d'akina kawai ,bayan sun shiga ta zaunar daita sannan ta kiran sunanta "maryama kamar baki so yallabai ko"?cikin sanyi ta d'ago shayayyun idanunta ta kalleta sannan tace "wannan wace irin tambaya ce subai'a?"tace amsa kawai zaki bani ba tamabayata zakiyi ."tace "to Ina son shi shikenan "karki min karya maryama bakya son shi kalli yadda yanayin ki ya canza jikinki har rawa yake saboda tsananin tsoro wanda ya tabbatar da baki son shi kamar dole yayi miki kika auresa ". karki zargi wani abu akanshi maganar bana son shi wannan ba gasky bace wallahi ina son shi kawai dai shi nashi son ne yayi yawa har yake rikitani "subai'a ta zuba mata ido kawai itama maryama ido ta zuba mata saboda a halin yanzu duk abinda zata fad'a ba fahimtarta zatayi ba shiyasa tayi shiru taki cigaba da cewa komai ba sai dai ahankali take Jin wata irin matsefaffiyar kaunarsa na bin jinin jikinta had'e da ratsa kowani part na jikinta damuwarta yan'uwansa."ahankali ta d'aga kanta sama tana kallon celling d'akin take ta soma tariyo abinda ya faru atsakaninsu a mintuna data gabata" mskilili zakin maza,ya tafi ya bar zuciyarta da daddadan kamshin turarensa tare da tsananin fargaba amman shi kallon yanayinsa kawai zaayi a fahimci yana cikin tsananin farinciki." Amar dake zaune kusa da adamcy ya kallesa yace"ya jikin maryama din !"?taji sauki "dan Allah adamcy ka tausaya kabi yarinyar nan ahankali kaga bata da lafiya,babu fa wani rashin lafiya, tsabar tsoro ne yayi mata yauwa ." ai dole yadda kake nuna mata ne yake tsoratata ". "me nake mata !?yayi masa tambayar yana kallonsa da gefen ido yayinda ahankali yaji gamshin jikinta ya gilma cikin hancinsa ya kawata numfashinsa kamar tana kusa dashi amar cigaba da kallonsa yayi yace "kafi ni sanin abinda kake mata "is like ka manta tarin abubuwan dake binne acikin zuciyata akanta?"nasani ban kuma manta ba , nasan irin k'awa zucin da kake dashi akanta, amman kasani maryama na bukatar sausauci daga gareka domin har yanzu yarinya ce da bata wuce shekarun kuruciyarta ba dan da anyi maka aure a shekaru a shirin da uku zuwa da hud'u wallahi da ka isa ka haifa kamarta." wani mugun kallo adamcy yayi masa wanda yasa take amar yayi shiru yana kunshe dariya adamcy yace "a'a yanzu ma zaka iya cewa ni ne babanta "dariyar da amar ya kunshe ce ta samu nasarar su'buce masa ai kuwa yasa dariya "kai me yasa baka son ace ka girma ne ?a ina girman yake ?"adamcy ya tambayesa yana had'e fuska ,"kai kake mata kallon yarinya amman yarinyar tasan abinda take sarai kuma tasan menene aure tunda ta ta'ba yi".duk da haka ni dai dan Allah na rokar mata alfarma ayi mata sausauci."Ka damu mutane da maganar sausauci sausauci as how ?"yarinyar nan fa ba wai bata ta'ba aure ba ta ta'ba yi har ma tasan dadinsa ,"duk da haka kafini sanin kanka Kai din cikakken namiji ne sosai ko a tafiyarka an sheida haka gaba d'aya ajikinka babu alamun ragwanta atattare da kai zaka had'a kanka da wancan lusarin mijin na.."shiru amar yayi ya kasa k'arasa maganarsa tare da lumshe idanunshi, yayi d'an gyaran murya kamar zai yi magana sai kuma yaja bakinsa yayi shiru ." shima mr ata shiru yayi zaune yana tunanin maganarsa da kuma dalilin da yasa ya kasa cigaba da maganar yace "ma marigayi tsohon mijinta lusari ne ta yaya zai ce masa lusari ko maryama ta ta'ba fad'a masa wani abu ne akan shi ?"kai she can't do that !"nasan halinta bazata ta'ba fad'a masa komai akan rayuwar aurenta ba ."sai dai haka nan yaji babu dadi aransa kwata kwata bai ji dadin kalmar lusari da amar ya kirasa dashi ba ,duk da ya fahimci yana tayasa kishi ne ,amman koma menene a yanzu baya duniyar ya rigada ya zama mamaci ko shima wani lokaci da yake jin kishinsa idan ya fahimci maryama na cikin alhininsa ne duk sai yaji babu dadi acikin ransa,har suka k'arasa gida babu wanda ya sake cewa d'anuwansa kala ." bayan motocin sunyi parking suka firfito daga cikin motocin kai tsaye inda zasu gabatar da walimarsu sauran abokansu suka nufa inda aka bar amar ,hisham ,mb tare da adamcy tsaye mb yace "yanzu ya zaayi da wad'an nan kulolin abincin ?"adamcy yayi shiru dan shima bai san yadda zaayi dasu ba "ko akai wa mami ne ?"iniicewar amar "kana ganin babu matsala idan an Kai mata "?mb ya fad'a yana dubansu d'aya bayan d'aya "bana ce ba amman a gwada kai wa adamcy ya fad'a nan take yasa aka shiga da kulolin guda biyu d'aya na tuwon shimkafa d'aya kuma na miya ."ahankali ya dubi abokansa yace "bari na shiga naje naga sweetheart na fito "okay "! suka fad'a a natse yabi bayan wad'an da suka shiga da kulolin alokcin da wasu tsirarun mutane ke zaune a parlour'n mami dan bata gayyaci mutane ba sai wad'an da baza'a rasa ba suma kuma na gidan ne sai yaranta da hajiya zulfa'u wacce tun jiya ta sauka tana faman bawa mami baki akan ta saki ranta amman furrrr mami taki sanki ranta ." Byn wasu yan mintina sai ga mr ata ya shigo da sallamarsa,mutane dake zaune a parlour'n suka amsa suna masa Allah ya sanya alkhairi bai ga mami ba ,haka zalika bai ga yaranta ba dan haka yayi tunanin suna tare daita a d'akinta kai tsaye ya zarce zuwa d'akinta ilai kuwa anan ya iskesu gabad'aya suna tautaunawa wani mugun kallo ya d'aukesu dashi
Chapter 25 · 0% Book details