Sashe 5
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba idan baayita anan ba mu karasa gida sai muyi acan ko gidanku ne kawai ya dacewa ayi magana mai mahimmanci ta lumshe masa idanunta alamun ce gidana zamu ! bangene gidanka zamu ba yallabai gasky ni dai a a idan har maganr ta wuce ayita anan ko a gidanmu sai dai a hakura daita . Baki isa ba nace ga abinda zaayi kice aa yana gama fad ar haka yaja mota kai tsaye gidansa ya nufa daita suna isa ya zare mata hijab din jikinta cire ki huta ! tana masa magana ko kallonta bai yi ba shigewa yayi ya barta tsaye a babban parlour nsa kam kema da jikinta tana kallon komai dake ajiye a parlour n har da kwalin sigarin da yake sha kusan minti goma sha biyar sai ga shi ya fito da doguwar rigar hutawa ta maza hannunsa rike da cup wanda ke d auke da lemu ya karaso ya zauna kusa daita yana cewa kinyi kyau fa ta dan yi musmushin dole bata ce masa komai ba ta gefen idonsa ya kalleta bani wayarki. me zakayi da wayata banason tamabya cikin tamabaya kuma nasan kinsan da haka Allah ya huci zuciyarka bani waayrki kafin komai ya biyo baya .ya fad a yana mika mata tafin hannunsa kyawawan yatsun hannunsa tabi da kallo k irjinta na bugawa da matsanancin k arfin gaske . Mmn Sudais MAR'ADAMS BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 2 "Ajiye cup din hannunsa yayi a gefensa ya matso da fuskarsa daf da nata har suna iya shakar numfashin juna ,wani irin tsalle zukatansu yayi ."lokacin d'aya zuciyar kowannensu ya fara lugud'en bugu ,ahankali ya lumshe mata tsuma mmun idanunshi yana cewa "bani mana wani abu zan duba" ya k'arasa maganar tare da bud'e idanunshi fes akanta ."shiru maryama tayi tana kallonsa cikin wani irin yanayi yayinda k'irjinta ke cigaba da bugawar da take "give me the phone.! ya sake bata umarni,bata san lokacin data hararashi tana mai kawar da fuskarta gefe acikin ranata tace "wannan mutumin ya cika damuwa banda neman magana me zai yi da wayata ." ya kai hannunsa ya juyo da fuskarta suka sake fuskantar juna"tsorona kike ji da bazaki maganar a fili ba ?"wata harara tai masa tare da tsuke bakinta matsota yayi sosai "irin wannan baiwar da Allah yayi miki kina saurin nuna min ita a arha kamata yayi sai na dinga biya kafin a nuna min ita saboda wannan irin kallo haka mai k'arawa mai kallonki ganin kyaun fuskarki, har ma yaji sonki ya kara shiga zuciyar wanda ya kamu da ciwon sonki ."Idan kuwa daman neman shiga yake idan kika yi masa irin wannan kallon lallai sai yayi tsammanin ya samu kar'buwa ne acikin zuciyarki ." Shiru tayi kamar yadda shima ayi shiru yana dubanta yana shafa sajen fuskarsa had'e da ciza lip's dinsa na k'asa yana jiran ta miko masa wayar ,baya son ya takura mata ne yasa ya bata dama ta bashi da kanta if not da tuni ya fara lalubarta, dan ko da bai ga wayar a hannunta ba yasan tana soke a jikinta" maryama ya kamata ace a yadda kike haka babu abinda Allah ya rageki dashi kamata yayi a samu hikima da wayo da iya jan hankali tare da tattali da biyayya ta hanyar aikata abu aloakcin da'aka umarceki batare da 'bata lokaci ko jayayya ba amman kashi da alamun banyi sa'a ba ta wannan bangaren ." "ina ganin ya kamata ki koma makarantar da'ake koyar da wad'an nan gaba saboda ni namiji ne mai son mace mai irin wad'an nan halayen kinga idan kina son ki juya ni na zamo sakarai a gareki dole sai kin zamo mai irin wad'an nan halayen dana lissafa." yana gama magana ta sake kawar da fuskarta dan ta fara shiga wani yanayi sakamakon numfashinsa da take shaka ." "Maryama!" Ya sake kiran sunanta a karo na biyu sai data ji duk wani gashi dake kwance a jikinta sun mike tsaye saboda sanyayyiyar muryar da yayi amfani daita sai dai batayi gangancin kallon inda yake ba dan tasan abinda zataji sai ya nikan wanda take a yanzu ."maryama ni namiji ne mai tsananin son ayi min biyayya sannan mai son idan ya bada umarni abi umarninsa, sannan a kula dashi kamar k'aramin yaron goye dan nifa shagwa babbe ne na bugawa ajarida sai kin gaji dani wajen son jiki koda yake zuwa yanzu kinsan wasu abubuwana ".ta d'an waigo ta kallesa ." "yes dole ne na fad'a miki dan kiyi biyayya dan kin samu dami akala ne dan samuna ba abu ne mai sauki ba"zaune kawai maryama take a wajen tana dubansa tana tunanin abinda ya d'auke ta?. "sakariya ya d'auketa ko me "?"eh mana ita ya d'auke ki "zuciyarta ta bata amsa da haka,bata san abinda ya kamata tayi ba dan tunda ya bukaci wayarta ta shiga cikin mummunar tashin hankali." Sake miko mata hannunsa yayi yana mata wannan d'an iskan kallon nasa mai matukar firgitarwa da jefe mutun cikin tsananin fargaba da tashin hankali,batare da 'bata lokaci ba ta ciro wayar dake soke a gefen siket dinta ta mika masa tana fesar da iska , ya amsa yana shan iska tare da ciza lip's dinsa na k'asa ."shiru tayi tana kallonsa tare da jin matsanancin tashin hankali da tsoron kar sakon yan'uwansa ya shigo adaidai lokacin gani tayi yana kokarin d'aura kanshi a saman cinyarta kamar ta janye k'afafunta sai dai tunawa da tayi a gidansa take da kuma sanin halinsa da tayi yasa ta hakura tayi zamanta a yadda take kar ta jawa kanta wata matsalar sai dai bakinta da zuciyarta basu yi shiru akan furta kalmar "la ila a illa anta subuhanaka inni kuntu minal zalimi ba ."tana kallonsa kai tsaye what's app dinta ya shiga ya fara duba sakonnin mutane cike da fargaba ta cigaba da kallonsa dan dai ta san anan bazai ga komai ba haka ma message bazai ga komai ba dan bata barin sako a wayarta da zarar sako ya shigo ta karanta take gogewa tashin hankalinta a yanzu shine kar sakon 'yanuwasa ya shigo ." bata san lokacin daya d'auka yana duba wayarta ba sai dai taji yana girgizata sannan tayi saurin dawowa haiyacinta cikin tsoro taga yadda yake kallonta yace "maryama me kike tunani haka ?." Nan fa ta soma in ina jikinta har karkarwa yayi wajen cewa "babu komai ."sake matsota yayi sosai fuskarsa a d'aure sosai sai dai ita tunin ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta duk da tasan babu abinda ya gani a wayarta amman zuciyarta cike take fal da fargaban abinda zai biyo baya,har tsawon minti goma yana kallon face dinta sannan ya sake kira sunanta "maryama d'ago ki kalleni ido cikin ido saboda maganar da zan miki babu wasa acikinta "jin abinda ya fad'a yasa ta d'ago kanta ahankali ta tsura masa shayayyun idanunta kamar zatayi kuka dan sosai zuciyarta ke bugawa da matsanancin sauri "a'a ya naga kamar kina son kiyi kuka ?"ta sake narke fuska "karki sake kiyi min kuka anan "ya k'arasa maganar cike da gargadi ,take ta soma kokarin maida hawayen dake kwance acikin kwarnin idanunta "Maryama waye ni agareki "?kai mai gidana ne a wajen aiki "ta bashi amsa tana sake jin fad'a uwar gaba mai tsananin ".ban dashi fa ?kai mai sona ne ."da kyau da kika gane haka ya kamo hannu wanta duka cikin nashi "ki saurareni sosai zanyi magana dake, ba zance wasa ko raha ko kuma tsorotaki zanyi ba amman ina son ki yarda a zuciyarki komai ya fito daga bakina to gasky ne ."ya d'an yi shiru kad'an yana kallonta ita kuma ta kawar da fuskarta gefe dan kallonsa ba k'aramin haddasa mata jin mummunar fad'uwar gaba yake ba "amatsayina na wanda zan aureki da zuciyata d'aya ba zan ta'ba yarda na cutar dake ba saboda haka kema banason ki aureni dan cutar dani sannan karki d'auki maganata a matsayin cutar wa ko takurawa domin magana ce ta amfanin ni dake amman fa idan kina sona dan Allah ". Tai shiru zuciyarta na wani irin bugawa da sauri sauri "kina son ki aureni dan kiyi rayuwar aure dani ta har abada ne ko kuma kina son ki aureni ne dan cima wani buri naki ?"yayi mata tambayr da batayi tsamaninta ba ,kwayar idanunshi na kanta kyam ko kiftasu bayayi yana nazarinta muryarta a sanyaye tace "bangane abinda kake nufi da maga ..."yayi mata wani kallon da yasa tayi shiru dan dole ba dan ta shirya yin hakan ba "idan har aurena zakiyi dan Allah to ina da sharid'd'ina guda uku da zan fad'a miki aciki zaki zabi biyu wanda yayi miki "ya sake had'e fuska "ina son idan kina da wani muradi ne aurena ki janye haka ki aure ni dan Allah ko kuma ki fasa aurena gabad'aya ."zance na fasa aurenka ma bai taso ba haka ma zance janye muradin aurenka bai taso ba ."tayi maganar acikin ranta ." "Na baki minti talatin kiyi tunani kafin na fad'a miki sauran duk maganar da yake fuskarsa a d'aure take "ni dai dan Allah ka cigaba da magana kawai dan hankalina ya fara tashi tayi maganar tana jin wani sabon tashin hankali na shigart "dole hankalinki ya tashi yayi maganar a cikin ranshi amman a zahiri cewa yayi "tunda na rigada na fad'a sai bayan minti talatin zan cigaba da magana sai kiyi hakuri har lokacin yayi ni yanzu yunwa nake ji abinci zanci ."ya mike tsaye ya barta nan zaune cikin jimami da zullumi mai tattare da tashin hankali da haushi da takaici duk sun taru sun rufeta alokci d'aya taji kamar ta shakesa ko ta rufesa da duka haka kawai tana zaman zamanta zai sake jefata cikin wani tashin hankali ."su kam wasu irin family's ne haka masu mugun hali ?"to kodai an halicci zuriarsu ne dan su jefa mutun cikin damuwa ?"daga shi har 'yan'uwansa da mahaifiyarsa duk