← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 94

Sashe 21

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suka saura ai duk daya ne a wajen Allah Allah dai ya kai mu yasa muna da rai da lafiya yace "ameen !" tun daga wannna lokacin gidansu ya samu bakunta mutane masu zuwa taya umma da aunty murna ta bangaren yan'uwa da abokan arziki duk da dangin mahaifinta basa sonta amman a wannnan karon jin wanda zata aura yasa taga sauyi akan fuskokinsu dan ."masu yara kanana har kamo hannunta suke ta dafa kan yaransu ko Allah yasa su dace irin nata ita kam abun shirme ta d'aukesa dan ta kanta take dan acikin tsananin damuwa da firgici take duk yadda take son ta cire tsoron mahaifiyar mr ata da yan uwansa aranta abun ya cutura kullum tsoronsu karuwa yake acikin zuciyarta wanda sanadiyar haka ta kamu da ciwon mummunar fad'uwar gaba second second gabata ke fad'uwa da karfi ,idan gabanta ya fad'i sai jikinta da hantar cikinta sun d'auki rawa karin damuwarta a yanzu yadda mr ata yayi mata banza kusan sati biyu kenan bai kiranta a waya ba dan tun kafin iyayensa suzo rabon ya kirata gashi har yau kwana biyar kenan babu shi babu labarinsa bare wayarsa.tashin hankali data shiga yasa ta kasa sheidawa kawayenta an kawo kudin aurenta da lokacin auren sai umma ce ta kira subai'a da yusura ta sheida masu dukkanin su babu wanda bai yi mamakin cewar mr ata zata aura ba ,ai ko kuwa da yamman ranar sai ga subai'a ta jawo motarta tazo tayata murna ". ta iske umma a parlour tare dasu aunty fatima da aunty hasana umma tace "subai'a har kin karaso?tace "ba dole ba umma ai kina fad'a min lokacin tashi ma bai yi ba na nemi excuse a wajen E D amar kinsan da yake dan'uwan mr ata ne jin uzurina ya barni " Allah sarki ashe har yanzu kuna aiki tare ?"eh umma! " ayya to Allah yasa albarka Allah kuma ya nuna mana naki haka subai'a tai murmushi ta gaishe dasu aunty fatima tana tamabayi umma maryama fa "?tana d'akinta kai tsaye ta shiga dakin inda ta iske maryama kwance tamkar mara lafiya tace "Ke shegiya tashi ki mike Allah yasamu a danshi ki domin kuwa kawata kinyi babban kamu mr ata fa ?inna lillahi ya rab Allah yasa albarka maryama ta yunkura ta zauna tana dubanta da fuskar babu yabo babu fallasa dan ita duk masu taya murna ganinta da kuka suka tayata da zai fiyye mata dadi dan ita kad'ai tasan abinda ke gabanta ,subai'a ta janyo kujerar da maryama Ke aiki daita ta zauna tana fuskartata tace "kawata daman soyayya kuke dashi amamn ko da wasa baki ta'ba labarta min ba gsky maryama Allah yayi miki zurfin ciki ?kema fa kinsan halin da nake ciki da zarar ance aure sai matsaloli su kunno kai ".haka ne kuma allah yasa albarka congratulations my friend maryama tai murmushi kawai yanayinta bai nunawa subai'a cewar akwai wata matsala ba dan tasan haka take normal." Subai'a tace "to yanzu ya ake ciki ?"meye shirye shiryen biki da za'a gabatar dan ga biki yazo wannan satin ne fa ?" maryama ta gyda mata kai alamun "eh!"tace "wannan satin ne za'a d'aura aure batun biki ne dai babu "ban gane babu ba ?"da gaske babu "haba haba karki mana haka mana ?"subai'a ta fad'a tana gyra zama gasky zan yiwa E D amar magana naji me ake ciki amman taya zaki ce babu biki tayi maganar cike da damuwa "maryama ta riko hannuwanta cikin nata "subai'a fad'a min wanda kike so Z&A shiru subai'a tayi tana jin mummunar fad'uwar gaba ". "me yasa bazaki fad'a min ba ?"maryama tayi maganar cike da marairaicewa tana duban fuskar subai'a "kinga ki bar wannnan maganr muyita daga baya yanzu maganar biki ne gabanmu dan zaki wani shigo da wata magana kenan dan ki shashatar da wacce muka fara ni dai kinji n fad'a miki zan yiwa ED amar magana numfashi kawai ta sauke tai shiru tana kallonta sun dan jima sannan subai'a tai mata sallama ta wuce tana zuwa gida tayi test din Amar yadda sukai da maryama bayan kamar awa biyu har ta fitar da rai zai reply dinta taga reply dinsa inda yace zai nemi adamcy yanzu duk abinda yace zai bari tasani ."bayan ta gama karanta sakonsa tayi shiru kawai rungume da pillow a kirjinta tana tunani nata damuwar ,akwai matukar ciwo ka kamu da son wanda bai ma san kana son shi ba ta kai hannunta tana shafa idanunta da suka cika da kwalla bata kai ga maidasu ba suka zubo akan kuncinta tana nan zaune ta sake jin shigowar sakonsa "he doesn't need a party"iya shi kawai ya rubuto sai dai ta karanta yafi sau babu adadi ." ****** Washegari ranar talata da yamma mami na zaune a babban parlour'nta sai ga wasu daga cikin ma'aikata mr ata suna neman izinin shigowa ta bassu izini inda tagansu ,su biyar suna shigowa da akwatunan shiru tayi zaune tana kallon guda biyar din da suka fara shigowa dashi ahankali suka dinga fita suna shigowa da akwatuna tun tana kirgawa har ta dawo ta daina akwatuna ne tsadaddu da matukar kyau da d'aukar hankali bugun england set set sukayi har sai da sukai goma shabiyar sannan suka suruna mata suka fice suka barta zaune tana kallon akwatuna wanda take ta fahimta akwanan auren 'yar gwal dinsa ne yasa akawo mata ." tana tsaka da kallon akwatinan ya shigo sanye da bakaken kaya da facin cap baki hatta takalmin afarsa baki ne kasancewarsa fari sai kayan suka amshesa fiyye da duk kayan daya saba sakawa sai kamshi yake zubawa fuskarsa ta sake fitowa sosai saboda gyaran fuskar da yayi ya karaso har gaban mami ya durkusa yana cire facing cap dinsa cike da girmamawa ya gaisheta"sweetheart kin yini lafya ?" "lafiya lau !" tayi maganar atakaice sannna fuskarta a daure tana daura hannunta akan cinyarta murmu shi yayi yana kallonta tace "wadan nan kayan fa ? kai tsaye yace mata "kayan maryama ne " ya fada yana mikewa tare da zama akan kujera idanu ta tsura masa for two second tana masa kallo mai cike da tsantsar mamaki"ikon Allah ashe yasan yadda akeyi komai amman alokacin maryam yayi buris ya share yakiyi dan kawai ya tozartata ita da diyarta ?" Yadda mami take kallonsa shima ita yake kallo hawaye ne suka fara turereniyar zubowa akan fuskarta, yayi saurin mikewa ya dawo gabanta ya kamo hannuwanta duk biyu yana cewa "no no sweetheart"?dan girman karki min haka idan na bata miki rai ne Kiyi hakuri "yanzu adamcy farinciki kake son nayi da wadan nan kayan ?"idan bai sakaki farinciki ba sweetheart sai amayar dan wallahi bana son ganin hawayenki yana daga min hankali ya kai hannu yana goge mata hawayen yana bata hakuri yana kallonta cike da tsananin kulawa Kiyi hakuri sweetheart bani da wata uwar da zan kaiwa kayan Bayan ke,ke din dai kece dole bari nasa a bud'e miki kiga kayan adamcynki ya fad'a yana goge mata fuskarta yana rarrashinta ,jinsa kawai take tana mamakin karfin halinsa yanzu ya gama cewa bai son damuwarta amman kuma yake maganar a bude mata kayan ta gani wanda yasan ganin kayan yana cikin damuwarta ,ita kan wani irin d'a ta haifawa kanta ?."har sanda ya kai hannu ya danna bell din dake kai sako bangaren ma'aikatan gidan tana cike da mamakinsa sannan fuskarta bayyane da tsananin bakinciki ." cikin kankani lokaci sai ga mutun uku sun fito cike da girmamawa suka gaishesa ya basu umarnin su bud'e akwatina da sauri suka fara aiwatar wa daya bayan daya suka dinga bud'e wa mami tace "wai ma a yaushe ka soma hada kayan lefe ban sani ba "jiya zuwa yau ne fa sweetheart ."ya karasa mganar yana murmushin gefen baki haka masu aiki suka dinga bud'e mata akwatin daya bayan daya shiru mami tayi tana jinjina kai tana sake mamakinsa a lokacin daaka bude mata akwatin kayan bacci ganin duk ya zabo hadaddun kayan zamani masu matukar kyau da daukar hankali tace "da kanka ka zabo wadan nan kayan bacci ?" Kai tsaye yace mata "yes "ta kalleshi tace "yes !"da saurin ya gyada mata kai alamun "eh " batare da yace mata komai ba"amman me yasa lokacin maryam bakayi mata ba ?ko abinda baka so baka bayar a auren ba "dan me yasa zan bayar wacan auren aurenki ne wannan kuma aurena ne" yayi maganar a kasan ranshi" yanzu duka kayan nan zaka bazawara har da ziniri fa naga ya kai goma anya kuwa baka haukace ba adamcy ?"ya fuskanceta sosai sai dai kafin ya soma magana sai daya sallame masu aiki bayan sun bar wajen yace "sweetheart babu abinda ya same ni wallahi ina cikin haiyacina fiyye da auren farko "okay to baza'a kai kayan nan ba ka ajiyesu tazo ta iskesu "dan Allah sweetheart karki yi haka na rigada na fad'a a gidansu za'a zo ranar alkhamis akawo idan kikayi haka kin zubar min da mutunci duk da nasan wadan nan kayan ba damu warsu bane ko dashi ko babu zasu bani auren maryama amman dan Allah kiyi hakuri nifa a yanzu a shirye nake da nayi miki komai idan akwai abinda kike so ki fad'a wallahi zan miki zare hannunta tayi tana jijiga kai "please sweetheart tace "naji banason magiya "thank you".mami yayanta kawai ta kira suzo suga kayan lefe su kansu sunyi mamaki irin kayan daya zuba sai dai suka ce iya rabonta kenan kwanaki kad'ai ya rage ungulu zata koma gidanta na tsamaiyya ." Koda mami tace suzo washegari akai kaya dasu suka ce a nemi wasu su kai amman su kam suna bayan maryam muddin sukaje kome yaya zataji babu dadi mami tace "to shikenan ta kira wasu daga cikin manyan gidan saboda babu isasshen lokaci mutane sukayita sawa kayan da auren albarka "Allah yasa auren yafi kayan albarka ranar alkhamis mr ata ya bada motocin da za'a kai lafe"tun safe gidansu maryama yake cike da mutane makwafta da yan'uwa da abokan arziki amman ban da aunty salma wacce Ke kunshe a daki cikin tsananin bakinciki ,dan duk inda taje magana daya ake fad'a mata wannan auren loacin yinsa yayi idan ta matsa komai zai iya faruwa daita wani waje dataj e akace mata idan zata
Chapter 21 · 0% Book details