Sashe 71
Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BOOK 4 *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Page 24 Idanuwanta dake cike da ruwan hawaye ta zuba masa shima idanuwanshi ya zuba mata yana jin yadda soyayyarta ke sake ratsa shi yana tsananin sonta kuma bazai ta'ba son wata halitta sama daita ba,ya kusan minti goma yana tsotsar lip's dinta da hakoranta sannan ya cire bakinsa ya damke yatsun hannunta cikin nashi ya tsurawa fuskarta ido yana cigaba da kallonta da yadda numfa shinta ke fita da sauri sauri "kiyi hakuri in sha allahu zan d'auki mataki akai "d'ayan hannunta ta kai saman nashi ta zare hannunta tana cewa "karka wani d'auki mataki akan kowa dan bazan so na zama silar shiga tsakanin yan'uwa ba kawai dai mu nisanci juna kamar kowa zai fi samun kwanciyar hankali da salama ".had'e fuska taga yayi sosai yana jifanta da mummunar kallo mai d'aga hankali wanda a duk sanda yayi irin haka to ransa yayi kololuwar 'baci,hakan yasa taji wani irin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinta,k'irjinta ya dinga bugawa da karfin gaske kamar wacce ake bugawa guduma dan haka ta dinga sauke ajiyar zuciya tana wasa da yatsun hannunta bayan ya gama hukuntata da mugun kallo har na tsawon mintuna shabiyar sannan yace "to be your first and last da zaki sake furta min wannan kalmar idan ba haka ba zan canza miki canzawar da zai baki mamaki "sake tsura masa shayayyun idanu wanta tayi wanda yaji kamar ya sume a zaunen da yake a gabanta ."tana kallonsa ya mike tsaye a natse yana daidaita natsuwarsa da bugun zuciyar sa dake faman bugawa ,ya cire suit dinsa ya saura daga shi sai yar samanta da fara riga da dogon wondo ya cire shoe's din kafafunsa ya sanya slippers ya fita ." tana ganin fitarsa ta janyo numfashi da kyar ta sauke tana fashewa da wani kuka mai cin zuciya ita kad'ai tasan yanayin data shiga alokcin da suka kira mahaifinta da d'an giwa tare da ai banta mata mahaifiya wacce duk duniya bata da kamarta ,ta sak runtse idanwunta da karfi alokcin taji tsokar zuciyarta tana tattarewa waje d'aya acikin ranta take hango girman tashin hankalin dake sak shirin tunkarota"da kikace ku rabu ke zaki iya rabuwa dashi ne?"nan take wani bangare na zuciyarta ta jefa mata wannan tmbayr "zan iya rabuwa dashi mana tunda ba tare muka zo duniya ba na rasa mahaifina ma na cigaba da rayuwata bare wani miji akan dai a dinga ciwa iyayena mutunci gara na hakura dashi. shiru tayi zaune kafin ahankali ta zame ta kwanta tana sauke numfashi da tunanin inda ya nufa dan tasan ba ma'akata zashi ba tunda ya rage kayan jikinsa "kai tsaye adamcy bangaren mami ya nufa inda ya isketa zaune tana waya wanda ke nuna masa alamun da d'aya daga cikin ya'yanta ne bai tsaya ta gama wayar ba ya soma magana cikin zafin rai "a gaskiya sweetheart abinda kike yi kwata kwata ba girmanki bane ki dinga biye ma wad'an nan ya'yan naki ana ciwa yarinyar mutane mutunci a gidan nan ana zalintarta ke daya kamata ki tsawata masu amman kece kike karfafa masu gwiwa kina biye masu mussaman ma wannan 'yar iskar khadija din to gaskiya Ina ganin lokacin zamanmu a gidan nan ya kare gaskiya zan d'auki matata mu kara gaba muje inda zamu samu zaman lafiya da kwanciyar hankali tunda kema tsamgwamarta kike yi ." tunda ya soma magana take kallonsa hankalinta bai tashi ba sai data ji batun zai d'auki matarsa su bar mata gidan muryarta cike da matsanancin tashin hankali tace"adamcy ni sa,arka ce da kake fad'a min magna da min gargadi ?"idan ka manta ko ni wacece bari na tunatar da kai ni magaifiya ce agurinka ba rikonka nake yi ba da kazo kayi tsaye akaina kana fad'a min magana son ranka tunda yar gwal ta fad'a maka magana akaina bayan ma nice na taka masu burki da yanzu ba wannan maganar akeyi ba dan da baka dawo gidan nan ka isketa da lafiyar jikjnta ba ai dana san wannan iskancin zaka min dana barin sun d'auki mataki akanta ko shahida sa'arta ce da zata fad'a mata magana?" to ko auta ba sa'arta bace bare khadija saboda ka rasa hankalinka da tunaninka yarinya ta fad'a maka karya da gaskiya kabi ka hau batun tsam gwama kuma daman ni nace maka Ina sonta ne ?".Ai bance Ina sonta ba kuma baka isa kasani na sota ba kamar yadda ban isa nasa kaso abinda nake so ba dan haka zaka iya d'aukarta ka bar gidan nan daita saboda baka san ciwon kanka ba sannan ka cigaba da bata kofar da zata raina maka yan'uwanka kuma na sak jin ka Kira khadija da yar iska sai 'bata maka rai sha shashan banza sha shashan wofi kawai ."ta k'arasa maganar tana goge hawaye Wanda yasa yaji hankalinsa yayi mugu mugun tashi domin kuwa zubar hawayenta na cikin abinda yake saurin d'aga masa hankali da dagula masa lissafi." Muryarsa a sanyaye yace "kiyi hakuri sweetheart ba wai na fad'a miki magana bane gani nayi abinda suke yi kece ya kamata ki taka mutsu burki sai kuma naga ..."saurin d'aga masa hannu tayi ta hanyar cewa "karka bani hakuri kaje can ka bawa ita yar gwal din taka hakuri tunda kana gudun 'bacin ranta amman kasani idan ka bar gidan nan da yarinya nan batare da izinina ba wallahi har abada karka dawo min daita cikin ahlina ."tana gama fad'ar haka ta juya masa baya tana cigaba da zubar da hawaye "inna lillahi ...!"ya furta a fili yana jin wani sabon tashin hankali ya shigarsa yayinda zuciyarsa ta dinga tafasa tana tuttukin bakinciki da sauri ya fito daga d'akin yana neman layin baba babba cikin sa'a ya d'aga sun d'auki lokaci yana koro masa halin da'ake ciki inda baba babba yace" karka damu in sha allahu zan sawatar masu idan baka fita ba ka tsaya zan kirasu har mazajensu su ja masu kunne ban da rashin hankali da rashin tunani ina so Ina aikata matarka saboda Allah?."suna gama waya da baba babba ya dawo part dinsa inda ya iske maryama a inda ya barta ya karaso ya shige jikinta yana shakar numfashinta da kamshi turarenta mai sanyaya masa zuciya ." bata ce masa komai ba ta juya masa baya tana janye jikinta daga nashi matsota yayi sosai tare da kai bayan hannunsa yana shafa wuyanta yana lumshe idanuwanshi jiki a sanyaye ta kai hannu ta cire hannunsa ta mike ta barshi nan kwance ."bayanta yabi da kallon kafin ahankali ya tashi ya biyota tana ganinsa tai saurin shigewa bayi ta kulle ya karaso jikin kofar bayin ya tsaya yana sauke numfashi." kusan awa biyu yana d'akin yana jiran fitowarta sai dai bata fito ba cikin haka wayar ta soma ringin ya ciro wayar yana duba screen din sunan baba babba ya gani dan haka ya d'aga kiran"okay to baba babba gani nan fitowa". ya fad'a yana k'arasawa jikin kofar bayi ya tsaya "my princess ..!"ya kira sunanta tana jinsa ta sha resa ".ki bud'e ki fito"muryarta a shagwa'be tace "nayi maka me !" "ke dai nace ki fito"ni dai dan Allah ka barni bana son wani tashin hankali yanz "baba babba ne yazo ."ai tana jin haka ta fashe da kuka tana cewa "yanzu saboda Allah zuwa kayi ka fad'a masa dan ka sake jamin bakin jini agurin su me yasa kayi min haka ?"ta fad'a tana sak fashe wa da wani sabon kuka "ki fito tun kafin ki k'ara min 'bacin rai "ni dai kayi hakuri bazan fito ba."wani dagon tsaki yaja sannna ya juya a fusace ya fita daga d'akin ya sauko zuwa kasa inda ya iske baba babba da 'yan'uwansa mata banda nana hauwa'u wacce bai san dalilin rashin zuwanta ba." ya k'arasa a natse ya zauna batare da yayiwa kowa magana acikinsu ba ."bayan ya zauna baba babba ya soma magana cike da natsuwa da man yantaka "shahida!!ya kirata har sau biyu cike da girmamawa ta amsa da "na'am baba !"mai yasa kuka shiga rayuwar auren adam?"shiru tayi ta kasa cewa komai" yanzu ke a matsayinki na babba kuma uwa kinga ya dace kiyi haka bare har ki bawa sauran 'yan'uwanki kofar taka matar d'anuwanku a gaskiya banji dadi faruwar haka ba yana cikin magana mami ta shigo itama ta zauna ayi daita "yanzu ku bakwa gudun abinda zai kashewa d'anuwanku aurensa auren ma da yaya aka samu yayi gaskiya banji dadi ba dan Allah ku kiyaye idan akwai abinda yarinyar take maku da bakwa jin dadi ku fad'awa mijinta ya tsawata mata ."bare ma baba babba babu abinda take masu kawai dai basa sonta ne saboda ban zauna da wacan zabin nasu ba, to dole ne sai nayi rayu wa daita nace bana sonta ko dole ne ?"itama ai tace tana sonka ba kuma daman tun asali bata sonka ta aureka ne dan ta farantawa mami wanda kai d'an data haifa ka kasa faranta mata ". inji cewar aunty khadija wata katuwar harara ya buga mata yana jan tsaki a fili "baba babba ya tambayesu d'aya baya d'aya "ko akwai laifin da yarinyar tayi maku?"duk sukai shiru suna shan kamshi babu wacce tayi magana duk da magana zabiba take son yi amman babu hali dan haka tayita bada hakuri ." "na rantse da girman Allah bazan sake daga maku kafa ba duk wacce ta sake kokarin ta'ba min jikin matata zan ta'ba lafiyar jikinta ,bayan haka kuma nasa ayi arresting dinta"idan ka isa Allah ya tsine min Allah yasa kasan wa nake aure idan hukuma kake ji dashi ai mune hukuma "to dan girman Allah karku daina shiga tsabgar matata ni kuma zan ajiye komai na d'auki mataki akanku mami kan shi kawai take kallo yana sak bata mamaki "matata yaki karewa kamar wanda ya auri zinariya adamcy yana gama rufe baki nana hauwa'u ta shigo tana ganinsa ta juya da sauri zata koma yace"dawo munafukar Allah da fuskar kamar na biri !tsimi tsimi nana hauwa'u ta dawo ta tsaya nesa dashi kar yaje ya kai mata mari "zo nan !yayi maganar yana jifanta da wani mugun kallo "taku biyu ta k'ara ta tsaya nesa da shi bata yarda ta matso kusa dashi ba "banyi mamaki duk abinda kika aikata ba