← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 94

Sashe 64

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

tana murzawa ahankali ". bai juyo ba ya kalleta ba ".muryarta a sanyaye tace "yalla 'bana ayi hakuri a yafe wa maryama duk da bata aikata laifin komai ba ".ahankali ya juyo ya zuba mata tsumammun idanunshi batare da yace mata uffan ba duk da magana yake son yi "kayi hakuri idan ba haka ba baza kaje second round ba "ta fad'a tana rufe fuskarta da hannunta d'aya sarai ya fahimci abinda take nufi damke hannunta yayi sosai cikin nashi yana cigaba da kallonta ganin ya saki ranshi tace "yalla'ba banji dadin irin tarbar da kayi wa mutanen can ba kamata yayi ka sakar masu fuska ko kad'an ne had'e fuskarka bashi zai sa raini ya shiga tsaka ninka da mutane ba amman fa ba dole nayi maka ba shawara ce idan kaji babu dadi kayi hakuri. yayi shiru kawai yana cigaba da kallonta kallon data fasaara da kallon Jan aji wani kallon kasan gira mai Kama da za'a lumshe ido "kace wani abu mana ka tsaya kana kallona?"me zan ce akan abinda ya shafi rayuwata "?jin abinda ya fad'a ta saki hannunsa ta mike zata tashi tana sakar masa harara yayi saurin riko hannunta ta fizge ya sake kamo yatsun hannunta,yayi masu riko mai kyau ya zagayo daita gefensa ya zaunar Daita yana cewa "ki natsu mana ko kin manta inda kike ne ."? Narke masa fuska tayi kamar zatayi kuka yayi murmushi yace "shikenan zan canza ai yanzu sai abinda kikace tunda kujerar mulki tana hannunki idan kina son na had'a miki da takobi sai ayi miki yalla'biya bata san lokacin data sakar masa murmushi ba ,ya ciza lip's dinsa "haka kake cewa akoda yaushe kujerar mulki tana hanuna amman daidai da second d'aya ban ta'ba jin dadin mulkina ba"karkiyi karya mana "!ya fad'a yana mata kallon kasan ido ahankali ya dinga fad'a mata kalamai masu sanyi da narkar da zuciya basu suka dawo ba sai cikin dare suka dawo bayan sunje sun d'an ciye ciyen su a restaurant din dake cikin hotel din suna komawa tare sukayi wanka dan idan da sabo yanzu ta saba da wankansu tare dan ko yayi nashi idan yaga zata shiga sai ya biyota ranar ma kwana yayi romancing dinta." kwannsu biyu a raddisi blue suna more wa rayuwa maryama taji kamar kar su koma gidan mami ,a kwana biyu din da basu gida yasa akayi capturing dinta wa international passport, ya'yan mami aranar suka zo gidan bata hakuri da kyar mami ta sauraresu ranta a 'bace tace "ai kun cuceni wata killa da wani zata aura bashi ba,gashi yau kwana biyu kenan tunda suka saka kafa suka bar gidan nan banga dawowarsu ba,babu kira babu komai Allah ya gani banason adamcy da yarinyar nan dan jikina yana bani iyayenta basu barshi haka ba duk da zulfa'u tace na daina fad'ar haka amman na kasa daina wa kana kallon adamcy kasan baya cikin haiyacinsa nifa nafi tunaninta yarinyar nan completely ba mutun bace ." Aunty khadija tace" mutun ce kmaar kowa tsabar dai biye biye ne da rashin imani irin na ya'yan talakawa nifa shawarar da nayi zan sa ayi edit din pictures dinsu da adamcy a buga a jaridu duniya ta gani ta haka ne kawai zan huce takaicin marin da yayi min"girgiza kai mami tayi fuskarta a d'aure tace "khadija bazan yarda da wannan shawarar ba kuma gara da kika fad'a naji domin kuwa da kin zartar da hukunci nan dana yi mugun sa'ba miki dan bazan ta'ba yarda ba duk abinda adamcy zai min bazan bari mutuncinsa ya zube a idanun duniya ba domin zubewar mutuncinsa kamar ta'ba kimar zuriar tariq ne zan dai tashi tsaye da addua da sadaka idan ma dauresa akayi Allah ya fidda shi. gabad'a yansu numfashi suka sauke kafin ahankali aunty shahida tace "ai kuwa zata ci uwrta a gidan nan karki sake barin ya fita koina daita ta shiga cikin sawun masu aikin gidan nan wata killa idan taga an maidaita baiwa zata bawa kafarta iska ."ita dai mami shiru tayi dan ba wannan bane damuwarta damuwarta yadda take hango rayuwar d'anta dan hatta soyayyarta gani take ya rag acikin zuciyarsa ." "Da wannan shawarar suka kawo karshen tau taunawwrsu washegari maryama suka koma gida zuciyarta cike da matsanancin fargaba suna shiga parlour'n mami idanunsu daita suka soma cin karo tana tsaye tana magana da wani mutun dake k'ok'arin kafa makeken hoton maryam ajikin bango shiru maryama tayi tana kallon hoton tana ma matar kallon sani bama kallon sani take mata ba ta ta'ba ganinta kuma acikin gidan a rana ta biyu data fara zuwa gidan matar zaune akan kujera na alfarma yayinda babynta ke zauen akan cinyarta tana bulbura murmushin maryama ta d'an waigo gefenta inda adamcy yake tsaye sai dai taga baya wajen can ta hangosa zaune yana kallon sama da alamun hoton bai d'auki hankalinsa ba kamar yadda ya d'auki nata ta d'auke idanunta akanshi ta k'arasa gaban mami ta durkusa har kasa sai dai ta rasa me zata tace mata "sannu da gida zata mata ko kuwa gaisheta".?shiru tayi durkushe har second goma tayi tana tunanin abun cewa can dai tayi tunanin gaisheta dan haka cikin kwantar da muryar tace "mami ina yini ?"shiru ne ya biyo bayan gaisuwar har ta cire rai da zata amsa sai taji tace mata "lafiya !" wani naunauyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike tsaye tana wasa da yatsun hannunta tamkar kazar da kwai ya fashe wa aciki haka ta dawo a gaban mami wacce ko kallo bata isheta ba cike da sanyin jiki ta nufi hanyar step har tayi taku biyu taji adamcy yayi gyaran murya ta tsaya tare da juyowa tana kallonsa da hannunsa yayi mata alamar tazo tai saurin girgiza masa kai tana kallon inda mami take tsaye alokacin har an gama kafa hotun nan take taga adamcy ya had'e fuska har kaminsa sai daya canza bata san lokacin data juyo gabad'aya ta soma taku zuwa inda yake cike da matsanancin fad'uwar gaba ba ta d'an zauna nesa kad'an dashi tana cewa "me zan maka ?!"shiru yayi yana ciza gefen lip's dinsa "dan Allah ka barni naje!"still share ta yayi tare da ware kafafunsa .zata sake magana mami ta k'arasa inda ya maida hankalinsa kanta yana gaisheta ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa sannna ta samu guri ta zauna a kujerar dake kallon nashi tana kallon maryama dake zaune cike da tsoro "tashi ki bani guri zan yi magana da "d'a..." ai maryama bata gama jin karshen maganr ba ta mike da sauri ta nufi hanyar step adamcy yabi bayanta da kallo har sai daya daina ganinta sannna ya dawo da kallonsa ga mami tace "baka ga yadda khaira ta k'ara girma ba ?"yace na gani tayi fine !yayi maganar batare daya sake kallon hoton ba tai shiru na second biyu tana nazarinsa sannan ta cigaba da magana "yanzu saboda manzon sallahu alaihi wa salam adamcy ka d'auki yarinyar nan tun sheka ranjiya sai yanzu ?"Menene illar haka sweetheart? "ya tamabya batare jin komai ba sai dai ganin irin kallon da take masa yace "am sorry "ta sauke numfashi ta cigaba da magana "na tura maka wasu addu'o i kajisu da kyau kuma kayi kokarin kayi duk wanda aka yiwa sihiri idan yana karan tasu safe da yamma Allah ubangiji zai maidawa mai shi kayansa dan na fahimci wannna yarinyar bata barka haka ba dan yanzu rashin jin barinka yayi maka yawa kana abubuwa baka san kanayi ba gabad'aya baka cikin hankalinka dan yadda kake bare bare akan yarinyar nan ba a banza ba dan dai Kai din nan ba adamcyn da ni na haifa bane ." tunda mami ta soma magana yanayinsa ya canza zuwa mummunar 'bacin rai sai dai yayita kokarin danne wa yace "sweetheart duk naji bayaninki kuma in sha allahu zan duba adduoin sai dai abinda kike tunani akan yarinyar nan ba haka bane dan ko qurni aka bani zan iya rantsuwa akan bata shirka dan Allah ki kwantar da hankalinki ki bari zuciyarki ta samu natsuwa daita kallonsa kawai tayi tana kwabe baki daman tayi expecting kareta zai yi "ni dai babu ruwana da ita dani wallahi har yanzu bana sonta da zaka rabu daita ka auro wata da zan fi jin natsuwa da kwanciyar hankali"ai kuwa mami sai dai kiyi hakuri ki cire wannan tunanin a ranki dan bazan ta'ba iya rabuwa daita ba, maryama ko aljanace ni ita zuciyata ta gani take so." An min haihu in sha allahu sai bayan suna zaku cigaba d jina Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 64 · 0% Book details