← Book details Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 94

Sashe 91

Mar'adams Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BOOK 4 AYSHA A BAGUDO WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Page 30 Sadam dake kwance akan doguwar kujera yaji an watsa masa hotunan a fuska,sama yayi da kwayar idanunshi yana duban nadia dake tsaye akan shi tana faman cika tana batsewa,ahankali ya mike zaune tare da dawo da idanunshi kasa yana kallon hotunan data yayyaga sosai gaban shi ya tsananta fad'uwa k'irjinshi na dokawa da wani irin k'arfi. hannunshi na rawa ya kai kan yagaggun hotunan yana dubawa a nutse hotunan daya sha wahala ya bari akayi masa print dinsu ne duk tama wulakancin haka ?"dan gabad'aya tayi masu kaca kaca idan ba wanda yayi wa maryama mugun sanin gaske ba ba zai ta'ba gane itace ba .cke da tarin damuwa ya sake d'agowa ya zuba mata kwayar idanunshi cikin 'bacin rai batare da yace mata komai ba "sadam !"ta kira sunansa tana jin fad'uwar gaba mai tsananin "still kallonta ya cigaba da yi "bafa zan juri wannan iskancin a gidana ba ,ko da yake idan ma ba hauka da toshewar basera irin naka ba banga ta inda matacce zai zauna yana 'batawa kanshi lokaci ba." kayi maza ka dawo tunaninka domin kuwa abinda kake hangowa kanka yayi maka nisa kuma har abada bazai dawo gareka ba gara ma tun wuri ka zauna ka shiga hankalinka sannan ka daina tunanin zaka dawo da abinda ka rasa sannan duk abinda ya faru recording video's din yadda kayi mutuwar karya yana nan a gurina kuma zan bayyanasu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso ,sannan ga babban albishiri a halin yanzu maryama matar aure ce " sak tsareta yayi da idanunshi kafin ahankali ya soma furta kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..! yana goge gumi d'aya rufesa alokci guda hankali ya b'alle mab'allan gaban rigarshi saboda zafin da yaji yana ratsa har cikin b'argon shi lokaci d'aya kuma jikinsa ya kama rawa"ya rage naka ka cigaba da rayuwar a sabuwar duniyarka ka manta da abinda ya faru abaya ko kuma ka zauna kana tuna nin abinda ka rasa rashi kuma na har abada "shiru yayi yana sauraronta har ta dasa aya gabad'aya yama rasa abinyi ya rasa me zayyi."maryamarsa ce tayi aure ?"ya tambayi kansa cikin tsananin firgici da tashin hankali. "yes tayi aure tana gidan mijinta idan ma da rabo watakilla zuwa yanzu ta samu, dan haka life goes on ka saki ranka kazo mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka tsara .bai san a fili yayiwa kan shi tambayr ba sai da yaji amsar data bashi "anya kuwa abinda nadia ta fad'a gaskiya ne?"aiko idan ya kasance gaskiya ne ba'a ta'ba fad'a masa abinda ya girgiza zuciyarsa ba sai yau .har ta juya tayi taku biyu ta tsaya tare da juyo da fuskarta kad'an tana masa murmushi wanda kana kallo kasan na mugunta ne ." "Ka tuna yadda aka shirya komai akan mutuwa rka?"kika shirya komai dai!"ya bata amsa a zafafe yana huci yana jin kamar ya tashi ya rufeta da duka .tai murmushi"okay naji amman ka tuna ka amsa makudan kudad'e akan zaka saki mryama?" yayi shiru yana kallonta jikinsa na rawa "nasan duk ka manta da hakan ?"ta cigaba da magana tana kallonsa abun na mata dadi "ka amshi maku dan kudi kuma kace saki mai sauki ne amman bayan mun dawo gida babu yadda banyi da kai ba kace na baka lokaci zaka saketa amman kaki sbd munafurci irin naka "saurin runtse idanunshi yayi da karfi yana jin bugun zuciyarsa na karuwa "ko kasan su waye wad'an da suka bada kud'aden nan ?"ya bud'e idanunshi da sauri ya zuba mata kawai yana kallonta yana jiran ta fad'a masa ko su waye sai dai yaga tayi dif tana cigaba da yi masa murmushi wanda yayi masa lakabi da harsashi dan jinsa yake tamkar harbinsa dashi take ." "tunda yake ba'a ta'ba yaudararsa anyi wasa da hankalinshi da tunaninsa irin wannan ba a iya tsayin rayuwarshi, lallai nadia tayi wasa da rayuwarsa kuma muguwa ce ,mahainciya ce kuma makiyiyarsa ce sa'banin yadda take nuna masa duk duniya tafi kowa son shi ahankali ya mik'e tsaye ya nufi fridge ya bud'e ya d'auko ruwa mai sanyi ya kafa a bakinsa. sakamakon makoshinsa daya ji ya bushe ,sai daya sha sosai sannan ya cire robar daga bakinshi tare sauke ajiyar zuciya da k'arfi yayi wurgi da roban yana furzar da iska mai zafi daga cikin bakinsa sannan ya nunata da d'an yatsansa "daga kaina kin gama rainawa kowa hankali nadia,in sha Allahu koda zan rasa raina ,koda zan rasa komai sai na dawo da maryama tunda dai har yanzu ban furta mata kalmar na saketa ba, sai na dawo daita rayuwarta idan zaki zauna daita fine idan bazaki zauna ba a shirye nake dana rabu dake nayi rayuwa daita ban san me ya faru dani ba da nayita biye miki amman nayi danasanin mara misaltuwa hatta had'uwa dake Ina danasaninsa a yanzu ".yana gama fad'ar haka ya ra'ba ta gefenta ya haye sama." wani murmushin mugunta ta saki sannan ta biyo bayansa tana magana tana taka step "ai muddin maryama ta bar matsayin da take a yanzu ta dawo maka lallai ya tabbata talauci ajininta yake kuma ita da arziki har abada .sai abu na gaba sadam kana da yawon mantuwa anan fa mukayi aure da kai ba'a africa ba kayi singn nayi sign idan ka shirya rabuwa dani fine ni kuma na shirya makaka a kotu duk ta hanayr da kake son kabi dani zan bi da kai ko zaman lafiya ko akasa sinsa "bai tsaya ya cigaba da sauraronta ba ya cigaba taku yana jin yadda zuciyarsa ke sake d'aukar zafi ."ya shiga d'aki ya kasa zama sai zariya yake gumi na sake tsatsafo masa ta koina ajikjnsa .ta turo kofar ta shigo d'akin ta kallesa tana jin dadi acikin ranta ko babu komai a yanzu tana da makaman da zata yakesa ta hana rayuwarsa sukuni da samun kwanciyar hankali . maryama tayi aure idan ta tuna da haka wani farinciki ke mamaye zuciyarta sannan da hannunsa ya kar'ba kudin sakin maryama .wani sanyi taji ya sake ratsa ilahirin jikinta kuma duk tana da sheida a hannunta dan haka zata ga ta yadda zai mallaketa arayuwarsa tunda tasan bashi da wad'an makudan kud'ad'en dashi suka yi komai kuma dashi suka cigaba da gudanar da rayuwarsu kafin samuwar aikinsa kuma tayi imani maryama bazata rabu da mr ata ta dawo masa ba most especially ma idan taji abinda yayi ya waigo ahankali ya kalleta yana jin kamar yaje ya shake mata wuya ya kasheta ko ya huta da bakinci da tayi sanadin jefasa ciki amman kuma d'an cikinta fa?" ko bama haka ba bazai ta'ba iya kisa ba ." "Kana kallona!ya d'auke kanshi yana jan tsaki ". "A kallon da kake min kana tunanin kasheni domin ka biyawa kanka bukatar ka ko ?"da zan iya aikata hakan zanyi amman bazan iya ba amman nadia me yasa kika yi wasa da hankalina da tunanin ?"me yasa kika yaudareni me yasa kika bari na kar'ba kud'ad'an nan ?"ya jera mata wad'an nan tambayoyin yana cizan lip's dinsa da karfi dan wani irin rad'ad'i azaba yake ji acikin zuciya dama gangar jiki "duk saboda Ina sonka ne sadam kasan zan iya rayuwa da kai ko baka da kowa baka da komai tunda kasan a baka da komai na fara sonka to kai mai yasa zaka canza raayinka bayan nasan ni kad'ai zuciyarka take so ."tsura mata idanunshi yayi yana kallonta yana nazarinta "tabbas yasan tana matsanancin son shi kuma zata iya aikata komai akanshi shima kuma yana sonta daga baya ne ya fara jin son maryama da tunanin komawa ga mahaifiyarsa wanda yasan hakin ummansa ne yayi saurin Kama shi.to shi yanzu menene mafuta agaresa ?" Yayi shiru yana tunanin yana son nemawa kanshi mafuta tun lokaci bai sake Kure masa ba ". "Ka zaunar daita ka tsarata kawai ka nuna mata ka hakura da maryama wajen ummanka zaka tasan kana raye .kana ganin zata amince da haka ?"zaka iya gwada sa'arka mata kuma da karamin kwakwaluwa tsab zata amince idan ta kama ka sakin maryama sai kayi alabashi bayan ka furta sakin sai ka dawo daita tunda yasan shi Allah da zuciya yake amfani .wannan itace mafutar da zuciyarsa ta tsayu akai dan haka ya sake kallonta adaidai lokacin data mike tsaye ta haura kan gado ta kwanta tare da juya masa baya ."ya sauke numfashi ya karaso ya kwanta abayanta yana kokarin kai hannunsa jikinta tayi saurin mikewa zaune tana cewa "bana son muna furci menene haka kuma ?"I'm really sorry nadia kin san Ina sonki son maryama hakinta dana mahaifiyata ne Allah ya jarabeni amamn nayi tunanin hakura daita tunda har tayi aure ." numfashi kawai ta sauke ba tace masa uhm ba bare uhm ta sauko ta d'auko takarda da biro ta mika masa rubuta mata sakin anan tare da sa hannunka kana min haka magana ta kare zaka iya tafiya ." "Yayi shiru yana kallonta daman yasa karshe abinda zata bukata Kenan daga garesa nan da nan kwakwaluwarsa ta shiga kai kawo "in dai har acikin zuciyarsa yasan da gaske ba sakinta zai yi ba koya furta bata saku ba sai dai idan yasan da gaske ya saketa to wannan fa ta saku dan shi saki koda wasa akayisa ya saku kuma ko batasani ba ta saku kuma duk randa labari yaje mata a sak take daga ranar zata kama gabanta amman shi yasan a zuciyarsa ba sakinta zai yi ba neman mafuta yake kuma zai iya mata saki d'aya kuma ya dawo daita a take. ya sauke numfashi yace anything for you ya kar'bi takada da biro tace "saki uku zaka mata ya tsaya yana dubanta yace "ai kinsan a muslimci ba'a saki uku a take ko anyi amatsayin d'aya ne dan haka zan mata d'aya ." tai shiru tana tunanin can tace bari na tambaya ta mike tare da wayarta ta fita ta barshi cikin tsana nin tashin hankali bayan kamar minti goma ta dawo d'akin tace "ka rubuta d'ayan yayi kmaar yadda ta bukata ya mika mata ta nad'e takardar ta tura karkashin pillow ta rungunesa ajikinsa "ban ta'ba jin natsuwa da kwanciyar hankali irin na yau ba." ka faranta min sosai ka yafe
Chapter 91 · 0% Book details