← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 75

Sashe 8

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lamiɗo dai tun jiya bai sake shigowa ba gida cike da mata. Amma zuciyarsa da tunaninsa suna wajem Ummu Salma ne a daran ma ya kira Bilkisu a waya ya ce ta duba masa ita. Domin ya yi ta kiran wayarta ba a ɗauka ba ita ba ta nemi wayar ba tana cikin jakarta, jakar kuma Adda Suwaiba ta tusa mata a wadrope ɗin Ammah ta saka maƙulli ta rufe.

Bilkisu ta ce masa tana tare da ƙawarta lafiyanta ƙalau shi ya sa hankalinshi ya ɗan kwanta amma ya san tana cikin damuwa sosai, su kan su dauriya ce irin ta maza amma rashin Baffa wani babban rashi ne a gare su gabaɗaya.

A ranar ma su Gimbiya Maimuna da Gimbiya Hadiza tare da Hajiya Zainab suka zo gaisuwa daga Daura.
Ba su jima ba, iyakarasu awa biyu suka juya.

Mutane suna ta zuwa gaisuwa daga garuruwa dabam dabam. Wasu mota ne wasu kuma jirgi ne.
Abinci ga shi nan ana kawowa wanda ake dafawa ma a cikin gida mai rai da lafiya ne sannan ga ruwa ga lemu, girkin ma da nama ake yin shi, shi ya sa gidan yake cika da mutane maƙil.
A ranar ma Hajiya Falmata ta zo tare da wasu dangin Daddy daga zamfara su dai yan zamfara a ranar suka koma Hajiya Falmata ne ta ce sai an yi uku

A ranar dakyar Mami ta iya cin abincin ba domin tana so ba Ammah kuma sai kunu aka dama mata ta sha kaɗan Ummu Salma kuma ta kasa cin abinci daƙyar ta sha tea shima sai da Gimbiya Shahida ta matsa mata tana gama sha kuma sai amai sai ga ta kwance jikinta ba karfi da za ta faɗi irin yadda kanta ke ciwo da sun tausaya mata tana kwance akan gadon Baffa tana ta hawaye da kukan zucci

Har bayan mangariba ba ta saka komai a cikinta ba, kuma mai rai ba zai zauna bai ci wani abu ba. Sai Gimbiya Shahida ta kira Saleem a waya ta ce ya yi magana da Lamido ya shigo cikin gida ya lallashi Ummu Salma ko za ta ci abinci saboda yanayinta

Yana faÉ—a masa bai tsaya ba tare da Saleem É—in suka shiga cikin gida falon Ammah ya fara tsayawa ya yi musu gaisuwa.
Ammah ya kalla a cikin kwana É—aya duk ta zabge kamar ba ita ba.

"Ammah kin ci abinci?

Ya tambayeta lokaci ɗaya yana kallonta cikin tausayi da wani abu daga ƙasan zuciyarsa

"Ta dai sha kunu amma abincin ya kasa ciyuwa LamiÉ—o."

Umma Balki ta amsa masa.
Sannan ta cigaba da faɗa masa Fatima dakyar ta yi cokula ta ce ta ƙoshi sun kasa cin abinci

"Kowa ya san an yi muku rashi amma hakuri za ku yi ku ci abinci saboda lafiyarku, ita Auta ma tea aka ce tasha ta amayar da shi tana can kwance tana kuka to gwara su sun samu sun yi kuka ita uwar taka ko hawaye ba ta yi ba. Na ce Jamila ki yi kuka in ba za ki a gaban mu ki kebe kanki ki koka domin abin kukan ne ya same ki , ta kasa yin kuka zuciyarta ne kawai ke cikin azaba ina tsoron kar zuciya ta kume mata itama wani abu ya same ta"

Hankalin shi ya tashi, ko daga ganin yanayin Ammah zafin dake cikin zuciyarta ya wuce tunanin mai tunani.
Gabanta ya sake matsowa ya durƙusa ya riƙo duka hannayenta ya sanya su a cikin na su ya ji sun yi ɗumi kuma suna ta rawa

Ya kalleta idanuwansa har sun sauya launi
Ba ya son ganin damuwarta, yanzu sai ya rikice

"Ammah."

Ya kira sunanta a cikin karaya domin shima ya karaya bai kuma san da wani kalamai zai yi amfani da shi wajen lallashinta ba. Rashi ne babba ya same su musamman ma ita, duk wanda ya zauna da Baffa da Ammah sai ya ji rayuwarsu ta birgeshi.

"Na'am LamiÉ—o."

Ta amsa masa tana kallon shi.

"Kar ku damu da ni, lafiya ta ƙalau na san Allah ne ya ɗauki ran Baffa, ni musulma ce na san kaddara na kuma karɓeta."

Ta É—an ja fasali kafin ta cigaba da faÉ—in

"Ku je ka samu Auta ka duba ta, an ce tun jiya ba ta ci komai ba tana ta kuka ga lalura a tare da ita."
Received at 09:59Reactions: ❤ 9, 😭 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta faÉ—a idanuwamta sun kawi ruwa amma ba ta barsu sun zubo ba.
Kowa a falon su kawai yake kallo.

"Ammah zan je, amma ke ma ki yi haƙuri."

"Na yi LamiÉ—o."

"Baffanku ma maganarsa ta ƙarshe kafin kalmar shahada haƙurin ya ba ni."

"Ammah to ki yi kuka. In wani abu ya same ki ina za mu saka kanmu."

"Babu abin da zai same ni Lamiɗo. Baffa ya ce na yi haƙuri yana gangaran mutuwa sau uku yana ba ni haƙuri Lamiɗo me ya sa zan masa kuka. Aikina shi ne na dauwama ina yi masa addu'an rahama har nima ta Allah ta kasance a gare ni."

Bakinta ne ya fara rawa daman hannayenta dake cikin na shi sun daɗe da kama rawa, bai san lokacin da ya durƙushe a gabanta ya jawota a ƙirjinsa ya rumgume ta yana mai lumshe idanuwana kamar shima ya fashe da kukan zuciyarsa ta yi wani dum kamar ba shi ba.

Ammah jin ta a jikin Lamiɗo ya sa wasu hawaye masu zafi suka saukar mata wannan hawayen ji ta yi kamar saukar dalma, ta yi saurin goge su a jikin shaddar jikin Lamiɗo dakyar hawayen suka fita amma zafin su ya fi  zafin zaman su a zuciyarta tana hana kanta kuka ne saboda in ta yi kuka za ta iya mutuwa ko ta haukace saboda rashin sanin abin da za ta yi gwara ta bar komai a zuciyanta yafi mata sauƙi akan zafin fitan hawayen nata.

Shi ya lallashi Ammah aka kawo tuwo miyar ganye ya takura mata ta ɗan ci kaɗan ba da yawa ba ta haɗa da ruwa. Kowa ya jinjina ma ƙaunar dake tsakanin Ammah da Lamiɗo.
Ya sanyata ta ci Abinci kuma ta yi masa yadda yake so.

Mami ma ya shiga wajenta tana cikin É—akin Ammah zaune saman darduma in da ta yi salla da hijabi ta haÉ—a kai da gwiwa tana kuka.
Ya daɗe da shigowa ɗakin ba ta sani ba sai da ya durƙusa a gabanta ya dafa kafaɗanta sannan ta dago fuskarta da idanuwanta jajir alamun dai ta sha kuka.

Tare da Hajiya Falmata suke zaune a É—akin shigowar LamiÉ—o ya sa ta tashi ta fita ta ba su wuri.
Ita kuma ta É—auka ma Falmatan ne sai ta ga wanda ba ta yi tunani ba.

Gaishe ta ya yi ta amsa tana É—an kauda kai tana É—auke hawayenta.

"Mami ki yi haƙuri ki daina kuka haka nan."

"Allah ne ya bamu Baffa kuma shi ya karɓesa daga hannunmu, muma mutuwar nan muke jira Mami, ki daure ki daina wannan kukan kar ki samu wata matsalan"

Ya faÉ—a a sanyaye yana kallonta
Kawai sai ta kalleshi ta girgiza kai lokaci É—aya ta fashe da kuka.
Daddy na nan bai koma ba yana tare da su Baffa Umaru sune manya masu karɓan gaisuwa.

Kukanta ya sake raunana masa zuciya kuka take yi har da sauti

"LamiÉ—o na rasa Baffa kuma sai ka ce na daina kuka."

"Baffa ne uwata Baffa ne ubana, shi ne dangina gabaÉ—aya ba ni da kowa sai shi. Yau babu shi Muhammadu yau na rasa Baffa ya zan yi in ban yi kuka ba?

Take faɗa cikin gunjin kuka lokaci ɗaya tana riƙe hannayensa.

"Baffa shi ne gata na, wallahi shi ne gata na, na rasa gata na."

Take faÉ—a tana jijjiga hannayensa cikin gunjin kuka.
Ya rasa yadda zai yi mata kukan ta ya fara yawa.

"Ki yi haƙuri Mami ki daina kuka."

"LamiÉ—o yanzu shike nan Baffa ya tafi ya barmu?
Sai ta sake fashewa da kuka.

"Tun iyayenmu na da rai Baffa ke amsa matsayin Uba a wajena. Lokacin da Gwaggo ta rasu Baffa ya so ya riƙeni amma aka hana shi riƙona lokacin da na koma Daura duk abin da Baffa ya samu sai ya raba shi da ni ya aiko mini da nawa. Baffa ya damu da rayuwata ya tattaleni ya mini dukkan gata. Lokacin da mahaifinka ya sake ni da a ce ba ni da Baffa da yanzu na mutu da yanzu ka mutu Lamiɗo. Baffa ne ya ba ni bayan shi na jingina Ammah ta ba ni Hannunta na kama, suka rumgume mu tare suka cicinɗa rayuwarmu Lamiɗo, Baffa ne gata na, na rantse da wanda raina ke hannun shi Baffa kaɗai nake da shi a duniya ta ya ba zan yi kuka ba."

Maganganun da take yi kamar ma ba a hayyacinta take yi ba jin ta kawai ta yi yi a cikin jikinsa ya rumgumeta.

"Na rasa Baffa. Na rasa farincikina na rasa gata na."

Take faÉ—a tana rumgume da shi cikin kuka.

"A'a bayan Baffa Ammah nan nan muma muna nan za mu taɓa bari ku yi kukan maraicin Baffa ba."

Yake faÉ—a yana É—an tapping bayanta alamun lallashi.
Amma Mami kuka take yi kamar ranta zai fita.
Received at 09:59Reactions: 😭 5, ❤ 3, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Baffa ya sha ce mini Fatima ki yi haƙuri wata rana sai labari. Baffa ya sha ce mini Fatima duk abin da ya faru dake ki ɗauke shi kaddara watarana komai zai wuce komai ya wuce Baffa ya yi gaskiya amma me ya sa tare da shi komai zai wuce ɗin me ya sa?

"Ubangiji ne ya fi mu son shi, shi ya sa ya É—auke shi daga cikin mu."

"Da ni mutuwan nan ta É—auka da ta sani ta bar Baffa.."

"Aa Mami kar ki yi saɓo don Allah."

Da a ce zai iya yin kuka da ya koka. Amma shima É—in ya kasa sai da tafafarsan zuciya.
Yau ne rana ta farko da hankalin shi ya taɓa jin Mami a jikinsa.
Ko hannun juna a matsayin uwa da ɗa ba su taɓa kamawa ba sai yau.
Chapter 8 · 0% Book details