← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 75

Sashe 43

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habib ya ba ta amsa yana jinjina kai.
Har gobe yana son Umma Salma, amma yana ƙokarin cire ta daga zuciyarsa ya tabbata yau ko mutuwa Lamiɗo ya yi Ummu Salma tafi ƙarfin shi har gaban abada.

*Janafty*
Received at 08:42Reactions: ❤ 8, 😁 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Bayan sallar isha'i da misalin karfe takwas na dare abokan Hamma Abdulrahim suka zo É—aukan Amarya.
Har da su Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman a cikin su.

An kai BaÉ—É—o wajen dangin mahaifinta sun yi mata nasiha, sannan Ummin ikki ma ta yi mata.
Da cewa in da za ta je ba baƙon ta ba ne, Ammah ba uwar miji ba ce uwa ce a gare ta. Ta yi biyayya iya iyawarta domin bautar aure ne ya kaita. In ta ji ko da sau ɗaya ta yi ma Ammah wani kallo ba ta yafe mata ba.

Baɗɗo ta sha kukan rabuwa da gida, Ummu Salma na gefenta duk da ta gaji ciwon kai na damunta kafafunta suna ta ciwo amma ba ta bar gefen Baɗɗo a matsayin ta na babbar ƙawa kuma ƴar'uwa ba duk da akwai wasu ƙawayen ƴa'ƴan yan'uwan Ummin ikki daga Mubi da wasu yanmata a dangin babansu Baɗɗo.

Ga kuma maƙota har da mai yi ma Ummu Salma kitso Maijida da Bilkisu ke yi mata ƙunshi in tana gari.
Sannan akwai yan makarantar su BaÉ—É—o da suka yi karatu tare, duk sun zo kuma sun yi mata kara sosai.

An kawo motoci masu yawa shi ya sa kowa ya tafi. Ammah aka damƙa ma Amarya tare da cewa daman ɗiyar ta ce dawo mata da ita kawai suka yi. Ammah ta ce ta karɓa ta yi kuma alƙwarin zama da Baɗɗo ba a matsayin suruka ba, sai a matsayin ɗiya a gare ta. Aka yi addu'a da fatan alheri sun ba ma Ammah turmin atamfa na uwar miji da botikan cincin da dublan na Ammah da danginta daman kuma an riga an yi jere Ammah da kanta ta shigar da Amarya har kan gadonta bayan ta yi addu'an da ko wata amarya ke yi a lokacin da za ta shiga ɗakin auren ta.

ÆŠaki ya yi kyau sosai sai fatan alheri kawai mutane ke yi da fatan zaman lafiya. Gado biyu aka yi mata kuma masu kyau da quality. Mutane suna gama ganin É—aki bayan sun ci abinci tunda su Adda Suwaiba sun yi abinci mai rai da lafiya na tarban Amarya, suka yi fatan alheri duk aka mayar da su gida.

BaÉ—É—o kawai aka bari sai Umma Salma dake tare da ita, sai wata É—iyar yayar Ummin ikki Mubeena sai Islam su kaÉ—ai a tare da BaÉ—É—on. Nan suka kwana tare da ita tunda ba kowa a wajenta.
Ummu Salma ta yi waya da Hamma LamiÉ—o shi gida suka kwana tare da Bilkisu da yara har da Hanan ita kuma sai ta tsaya a wajen Amarya.

Da safe kuma aka yi musu abin ƙaryawa mai rai da lafiya aikin su Adda Suwaiba ne. Suka kuma shigo dukkansu suna ta tsokanar Baɗɗo.
Sai dai ta sunkuyar da kanta ta kasa magana bakinta ya mutu Ummu Salma ce ke tare mata.

A ranar lahadin ma an yi biki sosai a gidan Ammah tunda an kawo Amarya. Shagali sai ya dawo sabo gida ya sake cika aka ci aka sha' babu abin da babu nama da naman kaza ko har ana ragewa a saman abinci Alhamdulillah kawai Ammah za ta ce, daga Masarautar Daura ma kuÉ—i ne masu yawa daga Mai martaba da Fulani, a ranar su Gimbiya Shahida suka koma ba su kwana ba.
biki ne na yan gayu na masu kuÉ—i ba a yi wani shagali ba sosai saboda mutuwar Baffa amma dai an haÉ—u an yi zumunci an yi wasa an yi dariya.

A ranar ma sun  sake yin hoto gabaɗayansu har da surukai da jikoki Baffa ne kaɗai ba shi a cikin wannan hoton an yi na tarihi ne domin sai a daɗe ba a sake haɗuwa ba ballatana a yi hoton. Har da Bilkisu tunda itama ai surukar gidan ce.

Zuwa dare gida ya watse sai bakin nesa da ba su koma ba.
Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim sun koma gidajensu da yaran su. Adda Nauwara ne da Adda Aisha sai Adda Safina ke gidan. Sai Ummu Salma da su Islam da su Mami tare da su Umma Balki har da Bilkisu da sauran yaran.

Ummu Salma da Islam tare da su Adda Safina suna bangaren Amarya suna É—an yi mata gyare gyare tunda yau ango zai shigo É—aki.
Su Mami ne ke can falon Ammah suna ta hiran su, da Bilkisu da ta hakimce cikin manya ana magana tana kallon bakin kowa É—aya bayan É—aya.

Ummu Salma na zaune saboda ba za ta iya wani aiki ba, jikinta ciwo yake yi ga bayanta. Sannan kafafunta sun tasa aikin ma su Harira ne, ita ke shara Hidaya na mopping Sabuwa na tare da Bilkisu. Daman su Anitha suna can Lagos aka bar su tare da su James suna tsaron gida.
Received at 08:43Reactions: ❤ 7, 👏 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Adda Safina na ta yi ma Baɗɗo shaƙiyanci da cewa Amarya ta ango yau dai Abdulrahim zai shiga ɗakin Amarya.

"Ko kunya haka zai wuce bangaren Ammah ya shigo nan ko?

In ji Adda Nauwara aka kwashe da dariya.
Adda Safina na faÉ—in ga Abdulrahim da kunya dama Saddam ne mai ido a tsakar ka, ita dai BaÉ—É—o ba ta magana sai dai mirmishi.
Ummu Salma na gefenta ita ce ke shigar mata.
Baɗɗo kafafun Ummun Salma ta kalla da ta miƙar da su a saman cafet ɗin dake falon. Ta ga yadda suka kumbura suna sheƙi.

"Kafafun ki sun kumbura fa Sisna?

Ta faÉ—a tana kallon Ummu Salma.

"Zirga zirga ne ya sa suka É—an haye sosai"

"Ko jinin ki ya hau ne?

"E ya ɗan hau zuwa asibitin da na yi na ƙarshe likita ya ce jinina ya ɗan yi sama."

"Allah ya sauwake. Ubangiji ya raba lafiya, yaushe ne tafiyar ta ku?

"Visa muke jira, tana fitowa za mu tafi."

"Allah ya kai ku lafiya. Allah ya sa a rabu lafiya cikin Aminci."

Ummu Salma ta amsa da Amin Amin.
Sai da suka gyara mata ko'ina suka turara shi da turaran ƙamshi ko'ina ya yi ƙal gwanin sha'awa.
Sallama suka yi ma BaÉ—É—o suka koma bangaren Ammah tunda ga tashin muryoyin maza nan a can bangaren.
Baɗɗo ta roƙi Ummu Salma ta zauna da ita kafin Hamma Abdulrahim ya shigo.

"Na gaji Sisna, zan je na yi wanka  ga Islam ta zauna dake."

Dole aka bar Islam da BaÉ—É—o.
A bangaren Ammah kuma mazan suna nan gabaÉ—aya ango ne kawai da Saddam ba su a wajen suna can tare da abokan ango lokacin da Ummu Salma ta shigo tana tura ciki a gaba sai da Umma Balki ta yi mata maganar kumburun kafafunta.

"Ki huta yar nan, nauyi ne a tare dake fa."

In ji Umma A'i Mami ta ce itama tun safe ta ga kafafun Ummu Salman sun É—an kumbura LamiÉ—o na gefen Hamma Kabiru yana kallon Umma Salma dake tsaye a gefen Mami shima ya ga kumburin kafafun nata.

"Zirga zirga ne fa ba wani abu."

Ummu Salma ta faÉ—a sannan ta ce za ta shiga ta yi wanka bayanta ma na ciwo.
Umma Balki ta ce ko tana kan gwiwa ne.
Mami ta amsa mata da cewa akwai saura EDD É—in ta farkon watan November ne.

"To ina ruwan Allah da abin da bature ya ce? Ko yanzu Haihuwa ta zo É—a zai fita fes."

Umma Balki ta faɗa har tana tafa hannu, Umma A'i na cewa ƙwarai kuma yadda cikin Ummu Salman ma ya yi ƙasa daga gani ya kusa fitowa duniya.
Mami ta karɓe da cewa da ikon Allah sai sun isa Egpyt sannan Ummu Salma za ta haihu a hannun ƙwararrun likitoci aka amsa da in sha Allahu.

Bilkisu ta na zaune ta ji maganar kamar daga sama.
Ta kalli LamiÉ—o zuciyanta ta rufe saboda kishi ashe a Misra Ummu Salma za ta haihu bai faÉ—a mata ba.
Ta kalle shi amma shi hankalin shi ma ba ya kan kowa sai Ummu Salma, Hamma Kabiru ma na yi masa magana kunnensa ne kawai ke ji amma hankalin shi na kan Ummu Salma da suke magana da Mami.

Har duhu take gani saboda kishi da baƙin ciki. Ta daɗe tana tunanin Lamiɗo ya fi son Ummu Salma akanta sai yanzu take sake samun tabbacin haka. Ita duk haihuwanta a Nigeria take haihuwa na Sultan ma a wani babban asibitin kuɗi ta haihu a Abuja na Beena ta haihu a Lagos.
Kuma ita daman ba ta da ra'ayin fita kasar waje ta haihu tunda duka haihuwanta ba ta samu matsala ba, ko ƙaruwa da mata ke yi wajen haihuwa Allah ya ba ta da sauƙi ba ta taɓa samun wata matsalar ba.
Chapter 43 · 0% Book details