← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 75

Sashe 50

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Video ne ga Mai martaba zaune ya sha rawani, ana ta yawo da shi da fatan Allah ya ba sa lafiya wasu jama'ar Daura har da masu kuka domin sun san Tsohon Sarkin adali ne akwai masu cewa Saleem ne ya cancanta Hakimin Daura wasu kuma suna faÉ—in Yarima LamiÉ—o ne ya fi cancanta kowa dai na faÉ—in ra'ayin shi.

Sai da aka kwana biyu wannan murabus É—in na Sarkin Daura ke trending a social media.
Har kuma zuwa lokacin ba wanda ya ji daga wajen Sarki na yanzu wato LamiÉ—o.
Sai ranar ta uku ne cikin dare misalin uku da wani abu LamiÉ—o ko na ce Mai martaba Sarkin Daura na yanzu ya kunna wayarsa ya kira Aminin shi a waya.

Maganar haihuwar Ummu Salma sai jiya ya ji a bakin Fulani sarkaƙiyar da ya shiga ya sa ya manta da wata waya. Amma kuma duk damuwar da yake ciki bai manta da Ummu Salma dake can tsakanin rayuwa da mutuwa ba.

Daga saukarsa a garin Daura zuwa yau ɗin nan rayuwarsa ta juya daga sama zuwa ƙasa nw. Juyin da bai taɓa tunani ba tun yana ganin wasa har sai ga shi ya tabbata amna yana gani kamar a mafarki ne, kamar in ya buɗe ido zai ga komai bai faru ba.

Tun a daran da aka masa naɗin Sarautar Sarkin Daura bai sake cikakken barci ba. Ɓata dare yake yi cikin tunani da fargaba, ba zai iya ba ya faɗa ma Mai martaba amma bai saurare shi ba. Yanzu ɗin ma kafin ya kira Kabiru sai da ya tura ma kamfanin su takardaan ajiye aiki ya fi mintina talatin yana juya saƙon kafin ya tura musu ta email ɗin su.

Shike nan yanzu ya yi sallama da mafarkinsa. Yana ji yana gani kaddara ta sake juya masa sabuwar rayuwa
Da gaske ne shi ne Sarkin Daura an yi masa naÉ—i Mai martaba da iyalansa ma suna shirin barin fada ne zuwa wani gidansa dake cikin garin Daura shiryen shiryen gyara Masarautar ake yi tare da saka lokacin bikin naÉ—i yanzu shi ne ke zama a kan karagar mulki a fada, shi ake yi ma biyayya shi ne umarninsa ke saman na kowa. Allah mai iko da gagara misali.
Shi ne ke shiga irin ta Sarki, alhalin Sarki na raye bai mutu ba.

Ba zai iya magana da kowa ba a lokacin ba sai Aminin shi, yana kiran shi kuma har ta kusa katsewa ya É—aga saboda shima gani yake yi kamar wasa.

"Amini."

"Kai ne?

Sai kawai Lamiɗo ya yi gyaran murya Kabiru sai ya ji ya yi masa ƙwarjini duk da ba ganinsa yake yi ba.

"Allah ya taimake ka Allah ya ƙara lafiya. Allah ya taya ka riƙo."

"Amini."

"Na'am Ranka ya daÉ—e."
Received at 18:55
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Na zama Sarkin Daura amma kafin na zama haka ni ne dai Muhammad LamiÉ—o aminin ka."
Sai ya É—an ja fasali kafin ya cigaba da faÉ—in.

"So ka yi magana da ni kamar yadda muka saba."

"To."

Kabiru ya amsa domin yana ganin kamar a mafarki.
Aminin shi ya zama sarki falo ya fita kar ya tayar da Safina dake barci.
Duk da akwai yuyiwar faruwar haka amma komai ya faru a cikin lokacin da ba wanda ya yi tunanin faruwarsa.

"Ummu Salama ta haihu, ka nemi visa da sauri don Allah ka je ka duba mini su, ka yi ma yarinya huÉ—uba."

"In sha Allahu."

"Da wani suna?

"Ka tambayi Ummu Salama duk sunan da ta zaɓa ka yi mata huɗuba da shi."

"In sha Allahu."

Kabiru ya amsa masa kamar baƙin juna sai suka yi shuru.

"Kana dai lafiya ko? Muryanka ta yi kama da wanda ya daÉ—e bai sami barci ba"

"Lafiya lau."

Kawai ya iya cewa duk abin da zai faÉ—a ba za a gane ba, bai kuma san me zai ce ba domin bai iya bayani ba.

"In ka yi waya da Ammah ka ce ina gaisheta zan kirata in na samu sarari."

Kabiru ya amsa da zai faɗa mata daga nan suka yi sallama. Sarauta gaskiya ce a muryan Lamiɗo har ta canza yana magana cikin natsuwa da ƙasaita duk da daman halin shi ne amma yau na dabam ne.
Kafin ya kwanta ya fara neman visa ta online tunda yanzu komai a sauƙake ne ko wani kamfani suna da handel a social media xa ka iya samun su ko ta email.

A daran LamiÉ—o ya kunna data sakonni wasu na ture wasu bai buÉ—e na kowa ba sai na Ummu Salma ta turo masa hoton jaririyar ya buÉ—e ya gani.
Sai da zuciyarsa ta yi haske daga wani shashe.

Ya rasa me zai ce ma Ummu Salma ya so ya kira ta sai kuma ya kasa.

"Thank you Ummu Salama. Thank you."

Haka kawai ya iya rubuta mata. Sai saƙon Bilkisu na gayyar sticker da emojin murna da dogon magana da turanci na ta ya shi murna.

"Bilkisu"

"I will call you later."

Abin da kawai ya ce mata kenan yana buƙatar natsuwa. Yana bukatar lokacin da zai karɓi wannan sabuwar rayuwar tashi tukunna kafin abubuwa su daidaita.

*Janafty*
Received at 18:55
Muhammad reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
MASARAUTAR DAURA.

Har yau da kimanin kwana biyar kenan da tsohon Sarki Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu ya yi murabus daga ƙaragan mulki ya ɗora ɗan shi Muhammad Lamiɗo Al'ummar garinn Daura ba su daina cece-kuce ba.

Wasu kuma suna ganin abin kamar a mafarki domin abu ne da ya faru ba tare da shiri ko barin wata alama ba. Wasu kuna suna tunanin rashin cancantar Lamiɗo wasu kuma tsohon Sarki suke so suna ganin a shekarunsa bai dace ya yi murabus ba, duk da ya faɗi dalilinsa ai suna ganin jinyar tunda ba ta kwantar da shi ba, bai kamata ya yi saurin yin murabus ba. Wasu kuma suna faɗin dama Hakiman Daura Saleem ya ɗaura a ganin su, shi ne ya fi kowa cancanta da wannan karagan tunda yawancin abubuwan fada da shi ake gudanarwa sannan ya sha wakiltan Mai martaba tsohon Sarki a wasu tarurruka masu muhimmanci an fi sanin shi tunda ana ganin shi saɓanin Lamiɗo da sai salla salla, amma in dai yana gari matasan garin Daura suna shaida zuwan shi saboda alherin shi.

Sauran kuma ko maganarsu ba a yi. Yazeed da Sagir gani ake yi ana babbakan giwa wa zai tuna da zomo amma duk da haka a cikin mutane ba za a rasa masu kawo su a matsayin suma waɗanda suka cancanta ba ko'ina dai ceceku ce yaƙi karewa amma kuma ba abin da zai sauya wannan kaddara tun a ranar da Sarki ya yi murabus Al'umma Daura suka bar ƙarƙashinsa suka koma ƙarƙashin jagorancin Lamiɗo Sarki na yanzu.

A cikin Masarauta ma kowa ka gani lamarin bai gama kama jikinsa ba. Nan ma mganganu suna ta tashi da cewa Sarki ya yi gaggawa ko na ce tsohon Sarki sannan ya yi shammata. Duk da duk wanda yake tare da Mai martaba tsohon Sarki kowa zai iya shaida Lamiɗo yake so ya gaje shi amma ba wanda ya taɓa tunanin da ran tsohon Sarki hakan zai faru masu hangen nesa ma gani suke yi Lamiɗo ba zai yi Sarauta ba, in Sarki ya rasu ba lalle ma ya fito neman karagar ba duba da ba ya son Sarauta ko da ma ya fito suna ganin majalisar zaɓe ba za ta zaɓe shi ba.

Sai ga shi komai ya faru a cikin dare ɗaya aka wayi gari da fashewar boom ɗin da kowa bai taɓa tunani ba sai ƙalilan mutanen da suke da alhakin sanin komai kafin zartarwa.

Kafin kowa da Fulani tsohon Sarki ya fara tattauna shawaransa da matsayarsa ta kuma ba shi goyon baya saboda itama a suffa da hallaya ba tun yanzu ba ta daÉ—e da ganin cancantar LamiÉ—o a matsayin wanda zai gaji karagan mulkin Mai martaba. Kuma lokaci ya yi da zai dawo gida ya rumgumi rayuwarsa hannu biyu lokacin da ya ganawar sirri da sauran yan'uwansa mata ne wasu suka nuna ba su amince ba. Kamar Hajiya Kilishi a rashin nuna ba ta amince ba dalilinta shi ne ai ba jinya mai tsanani Mai martaba yake ciki ba, a ganinta bai kamata ya yi murabus ba.

Haka ma Hajiya Zaliha ta ce, sauran kuma irin su Hajiya Binta suna nuna cewa bai cancanta Lamiɗo ya yi gadon karaga ba. Me ya sani game da harkan mulki? sannan mahaifiyarsa ba yar sarki ba ce me ya sa zai mulke su! Mai martaba shi ne mahaifin Lamiɗo kuma ya cika duka sharaɗan zamowa Sarki saboda haka yana neman yardansu zai yi murabus sannan zai kai maganar wajen wakilan zaɓen Sarki, sun daɗe suna tattaunawa kafin a samu daidaito, kawai dai sun amince ne domin ba su da ta cewa tunda ba su cikin masu zartawa wannan alhakin majalisar zaɓe ne.
Chapter 50 · 0% Book details