← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 75

Sashe 27

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye ya amsa da shi ya ce ta zauna ta sake warwarewa daga baya sai ta biyo su.
Bilkisu murna kamar me, tana ta mirmishi ita kaÉ—ai duk da bai faÉ—a ba, ta san wani abu ne ya faru a tsskaninsu da ya hana tafiyar Ummu Salma addu'a take yi a zuciyanta da Allah ya sa daga nan auren ya kare kowa ya huta.
Ita kadai za ta dinga juyi a wannan ƙaton gidan da daman baƙin cikinta ɗaya yadda za ta juya a sabon gida itama Umma Salma za ta juya gani take yi ai ba matsayinsu ɗaya ba ma.

Tafiya da Hanan kuma sai yanzu ta fahimci saboda makaranta ne. Ba ta damu ba in dai Umma Salma ta fara barin mata mijinta ita ma Hanan É—in ba daÉ—ewa za ta bi bayan uwarta.

Kayanta ma Harira aka ce ta haÉ—a, sannan ko a gilmawa ba ta ga Ummu Salma ba kuma LamiÉ—o bai neme ta ba. DaÉ—i ya yi kusa kasheta tana zaune tana girgiza kafa tana faman mirmishi.
Duk maganganun da aka yi a falo Ummu Salma na laɓe daga ƙofar ɗakinta tana ji.

Ita kaɗai ta yanke ma kanta hukunci, hukuncin da take da yaƙinin shi Hamma Lamiɗo zai yanke, daman ita ta ce ba za ta bi shi ba ta faɗa gaban yan amin, yadda ya ki ɗaukan wayanta ya rufe ma hanyar da za ta same shi ta samar ma kanta mafita.
Bayan ta idar da salla asuba ta samu Ammah har É—akinta ta yi mata karyan ita anan za ta zauna in ji LamiÉ—o Ammah ta ce in ya zo za ta yi magana da shi ta ji.

Tunda ta ji hayaniyarsu ta laɓe, ba za ta iya fitowa ba, ba ta yi mamakin cewar da ya yi ta zauna ba daman ta yi tunanin haka. Itama kunya ba zai barta ta bi su ba, sannan kuma ita ce ta ce daman ba za ta bi shi ba, shi ya sa ba ta shirya ma tafiyan ba. Gwara su tafi daga baya sai ta bi su in ta tabbatar da ya koma bakin aiki sai ta koma zuwa lokacin da zai dawo ya wuce, sai ta tattaro duka kalaman bakinta ta sake bashi hakuri. Amma yanzu ita kanta kunyar abin da ta faɗa masa take ji.

Ta san kuma ba zai taɓa shigowa yi mata sallama ba, itama ba ta san da wani idanuwa za ta kalle shi ba.
Tana zaune gefen gado Harira ta shigo tana ce mata Ammah ta ce a haÉ—a kayan Hanan ta amsa mata.

Tana sake ganin girman Hamma LamiÉ—o da kuma nadamarta duk abin da ta yi masa bai bambanta Hanan da su Sultan ba, kuma bai fasa amsa sunan uba a gare ta ba.

Harira ke tambayan ta su ba tare za su tafi ba? Ta ce mata sai daga baya sai ta koma ganin likita.
Ashe da ba ta ga Hidaya da Sabuwa suna Lagos Bilkisu ta tura su kafin ta wuce Daura suna can sabon gida suna kimtse kimtse ma'aikatan ma sun dawo bakin aiki har su Debora su kaÉ—ai ne masu gidan ba su dawo ba.

Tana jin Harira ne kawai na magana amma ita tunanin ta ya yi nisa, sai da Harira ta gama haɗa kayan a ƙaramar akwati ne, kamar za ta yi magana ganin har da wasu kayan da aka ɗinka mata a can gidan su Habibu, watsar da kayan ma ta so yi daga farko daga baya kuma sai ta fasa.

Tana zaune har Harira ta fice ta yi tagumi kawai, tana jin hayaniya a falo sai da suka yi breakfast itama an shigo mata da nata amma ta kasa ci a lokacin ma ta sake kiran wayar Hamma LamiÉ—o ba ta shiga.

Tun da ta ji zuwan Hamma Abdullahi ta san tafiya ta tashi tunda shi zai kai su filin jirgi. Ta maƙale a jikin kofa tana leƙe.
Ta hango Hamma Lamiɗo a durkushe a gaban Ammah ya rike hannunta yana mata magana a hankali ko kana kusa ba lalle ka ji abin da ya ke cewa ba, ballatana ita da take leƙe daga cikin ɗaki.

Bilkisu da yaran sun fita Harira ta É—aukan musu jakunkuna, Hanan ko nemanta ba ta yi ba, ballatana su yi sallama itama ba ita ce a gabanta ba yanzu.
Received at 07:52Reactions: ❤ 12, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Tana gani ya saka ma Ammah farar evelope jikinta. Tana jin muryan Ammah na godiya da saka albarka.
Umma Balki har da ita a masu fita rakiya lokacin da ya miƙe sai ya ɗan waiwayo kamar zai kalli ɗakin da Umma Salma ke ciki sai ta yi saurin yin baya tana dafe kirji kar ya kamata tana leƙensa.

Bakin yadi ne a jikinsa É—inkin zamani da bakar hula mai gashi gashi.
Juya baya ta yi tana dafe ƙirjinta dake bugawa.

Ba ta taɓa tunanin zai shigo ba sai ji kawai ta yi an buɗe kofa. Da juyawarta da shaƙam ƙamshin turaran shi duk a lokaci daya ne.

Sun haÉ—a idanuwana amma shi ya yi saurin kauda kan shi. Baya son kallonta ita kuma tana ganin shi wani irin nadama abin da ta aikata ya ruguzo mata.
Ta yi narai narai har kwarmin idanuwanta ya cika da ƙwalla.

Kafafunta suka shiga rawa ganin yadda ya haÉ—e fuska ya fito a sak Yarima Daura ko LamiÉ—on da ta sani a can baya.
Wanzuwarsa a ɗakin sai ta ji kamar ta matsu, kamar babu wajen iska ƙwarjinsa ya babbake ko'ina da ya sa ta kasa ma numfashi mai ƙarfi.

Duk nacin kallon shi da take yi bai yarda ya kalleta ba a cikin aljihun wandon sa ya fito da farin evelope mai tudu ya ajiye mata a gefen gado.

Ya juya zai fita ba tare da ko hawa da saukan numfashin sa ba ta ji ba.

"Hamma."

Ta kira shi cikin karyewan sauti sai hawaye shar.

"Ka yi haƙuri don Allah.."

Ya tsaya amma bai juyo ba.

"Na tuba ba zan ƙara ba."
Kukan har yana sauti ya lumshe idanuwana ya buÉ—e.

"Take care of yourself"

"Ummu Salaama"

Yana gama faɗin haka ya buɗe ƙofa ya fita ya barta tana durƙushewa a ƙasan cafet tana kuka yana jin ta amma ba zai bari kukanta ya yi masa tasiri ba.

Daga shi har ita suna bukatar lokaci. Gwara ta zauna tare da Ammah a kula da lafiyanta ta samu natsuwa shima gwara ya yi nisa da ita ko zai samu zuciyarsa ta yi sauƙi. Amma zencen gaskiya yana buƙatar lokaci sannan ko zai saurare ta ba yanzu ba. Yana jin kalamanta har yanzu yana tunanin kuma zai daɗe yana jin maimaicinsu a cikin kan shi, Ummu Salma ta ruguza komai, in ya ce komai yana nufin komai amma soyayyarta dake cikin zuciyarsa ba ta samu rauni ko tawaya ba sai dai hakan ba shi zai hana ya nuna mata kuskuran abin da ta yi ba.

Daman ya yi niyar ya shiga ya yi mata sallama. Ya fuskanci uzirinta ta bangaren halin da take ciki amma ba shi zai sa ta riƙe a matsayin makamin da za ta kwatsa masa wannan maganar ba. Ba ta da lafiya har yanzu tana kan dokokin likita ne, ya bar mata kuɗi masu yawa domin nauyin ta yana wuyan sa ne ta kula da kanta har zuwa lokacin da zukata za su huce.

Yana jin kukanta amma bai juya ba haka ya fita, Ammah ba ta fita ba amma ta bi shi da fatan alheri mai yawa.
A motarsa Hamma Abdullahi ya tuƙa su zuwa filin jirgi a ranar da Baffa ke cika kwana talatin da ɗaya a ƙasa.

Sai da jirgin su ya tashi ya tashi sannan Hamma Abdullahi ya dawo gida da motar ya ba ma Ammah key É—in motar da na bangaren Bilkisu.

Ummu Salma kuma ba ma wanda ya sake bi ta kanta.
Tun da Hamma Abdullahi ya tambaya ganin ya ga ba da ita aka tafi ba Umma Balki ta ce LamiÉ—on ya ce ta zauna daga baya sai ta bi su.
Ko su Hamma Saddam da suka dawo aka ce ta na nan ba ta tafi ba ganin Harira ba wanda ya damu da ya shigo ya duba ta.

Tun a yau ta fara nadama, da a ce ta ji haƙurin da ake bata da tuni tana gidan mijinta. Ga shi tana gidan amma ba ma wanda ya damu da ita.
BaÉ—É—o kuma ta yi fushi da ita ta daina zuwa ta daina nemanta.

Zaman gidan ma sai ya zame mata kamar a gidan yari kwata kwata ba ta jin daɗi. Ga shi tun da Hamma Lamiɗo ya tafi sama da sati bai taɓa kiranta ba ko ta kira shi ba ta samu sannan tana jin suna waya da Ammah daga baya ma a bakinta take jin ya koma wajen aikinsa.

Ga kewa duk ya sake surkukuta ta, ba wanda ya lura tana ta ramewa.
Mami ma da suka yi waya ba ta san kwanan zencen ba har tana faÉ—in sai ta yi gyaran jikinta a tsanake, kayan da tunda aka kawo su ba ta duba su ba

Sai ranar ta saka Harira ta buÉ—e tunda a leda suke ciccibi da kazar sababi sun É—an fara lalacewa sai kawai ta ce Harira ta zubar garin magunganur kawai ta bari sai maganin sanyi.
Abin ta aikata ne ya zo yana damunta ga shi ta kasa faÉ—a ma kowa.
Received at 07:52Reactions: ❤ 9, 👍 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
BaÉ—É—o ce abokiyar cin mushenta ta kira ta domin ta nemi sulhu ta ce za ta zo amma ba ta zo ba.
Shamsiya sau biyu tana kiranta na farko ta É—auka.
Na biyun kuma ba ta É—auka ba, ba ta ga amfaniin kiran wayar ba. Ta faÉ—a mata Hanan na Lagos ita tana Adamawa.

Har abada ba ta buƙatar Shamsiya a rayuwarta yanzu, ita ta zama past tense a cikin rayuwarta ne.
Daƙyar Baɗɗo ta hakura ta zo ranar Hamma Lamiɗo ya yi sati biyu da ta tafiya da ta zo ta ga Ummu Salma sai da ta yi magana.

"Sisna kin ga yadda kika rame kika lalace?
Chapter 27 · 0% Book details