Sashe 24
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko ya janye kalamanshi ko kuma ya cika abin da ya faɗa. Gidan shi suka wuce domin sai yamma suka zo gidan abin da ya kara baƙanta ma Ummu Salma zuciya bai neme ta ba tana jin shi a falo tare da su Ammah amma bai leƙo in da take ba. Itama ta yi kudirin ba za ta fita ta gaishe shi ba sannan ba za ta neme shi ba.
Sai Bilkisu ce ta shigo tare da su Sultan sai ta ga kamar ma Bilkisun dariya take yi mata lokacin da ta shigo ta ganta ta fito wanka ne É—aure da towel tana yin wanka da safe da Yamma da ruwan zafi sosai Mami ta ce ta dinga yi har sai ta yi arba'in amma ba ruwan zafi sosai ba
Ta ga tana mata kallom sama da ƙasa tana dariyan fatan baki. Sai take tunanin me take yi ma dariya? Sai da ta fita ta kalli kanta a madubi ta fahimci abin da Bilkisu take yi ma dariya. Duk ta lalace fuskarta ta yi baƙi gashin kanta ya yi biji biji, ga tumbi da ta ga wannan haihuwar ya yi mata kumbiyu a jikinta. Hawaye suka cika kwarmin idanuwanta, duk a dalilin wa ta koma haka! A dalilin wanda ya ce zai iya sakinta bai damu da halin da take ciki ba. Dole kishiya ta zo tana yi mata dariya.
Baƙinciki da kishi suka rufe mata jin ta da ganinta sai da ta yi kuka ta samu salama.
Har kuma suka bar gidan bai neme ta ba Hanan ma bin su ta yi domin da ta fito ta ga ba ta gan ta ba Umma Balki ta ce ta bi babanta zuwa gida.
A tunaninnta in ya zo washegari zai neme ta amma ta ji shuru.
Ya zo gidan da yamma sannan suka fita da su Hamma Abdulrrahaman zuciyarta ba ta ƙara zafi ba sai da Umma Balki ta leƙo ɗakin da take tana ce mata ya ba ta ga tana shiri ba ne.
"Shirin me ne Umma Balki?
"Shirin tafiya mana, ko ba da ke za a koma Lagos É—in a goben ba ne?
Kenan gobe za su tafi amma bai faÉ—a mata ba, kuma a tunanin shi ta shirya ta bisa bayan ya gama tozarta ta, ya ja mata dariyan kishiya.
Amsa ma Umma Balki ta yi da cewa kayanta a haɗe suke. Harira za ta haɗa mata sauran. Amma baƙincikin ya yi mata hawa hawa a zuciya.
Ba za ta bari sai goben ba a yau koma mai zai faru zai zo ƙarshe. Ƙarshen renin hankali ya gama yi mata.
Wato tunda shi yana da ya'ya ba zai damu don ta rasa jaririnta ba tuna haka kawai in ta yi kuka yake sakata yankata fa aka yi amma ba ta samu kulawa daga wajen wanda take tunanin ya fi kowa son ta ba.
Tana idar da salla ta jawo wayarta ta tura masa saƙo.
Tun wannan kiran da ya yi mata ba ta É—auka ba, bai sake neman ta ba.
Shima kiran saboda Mami ne bai yi ra'ayi ba.
Kenan har gobe yana nan akan bakan shi ita ce mai laifi shi kalaman da ya faÉ—a daidai ya yi.
"Hamma ka ce za ka sake ni amma na ji shuru."
Sakon ya tafi da wajen mintina goma bai dawo mata da amsa ba.
"Abin da ka nuna na rashin damuwa da ni ya fayyace mini nufin ka a kaina. Kar ka damu ko ka sake ni ba zan tagyayara ba"
"Ina jiran ka, domin ba zan bi ka ko'ina ba."
Ta jira amsar shi shuru shuru har takwas ta gota sai ta tashi ta kabbarta sallar isha'i.
Tana cikin sallar wayarta ta yi haske tana idarwa gabanta na faÉ—uwa ta jawo wayar ta duba shi ne.
"Okay."
"Ki zo ki karɓa abin da kike so ɗin"
Abin da ya ce mata kenan da sauri ta tura masa tambaya.
"A ina?
"Bangaren su Saddam."
Received at 07:52Reactions: ⤠6, 😠1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ko fita daga kan saƙon shi ba ta yi ta miƙe da Hijabin da ta yi salla ta fice.
Umma Balki ce kawai a falo tana salla Ammah na ciki, tana jin Umma Balki na uhm uhm da gyaran murya ta zura takalmin silafas ɗin dake ƙofar ɗakin Harira na kitchen tana wanke wanke sai da ta leƙo.
"Ranki ya daÉ—e ina za ki je?
Sai ta juya tana kallonta
"Hamma ke magana da ni a waje."
Sai ta jinjina mata kanta ko tsaya ma sauraranta ba ta yi ba ta wuce
Zuciya ce ke tura ta gwara ta san matsayinta.
A hanya ta haÉ—u da Saddam da Abdulrahim za su shiga cikin gida.
Ta tambaye su ina Hamma LamiÉ—o?
"Yana bangaren mu."
Ba ta ma tsaya jin ƙarshen maganar ba ta wuce da sauri.
Suka bi ta da kallo ganin saurin da take yi cikin gida suka nufa ita kuma har tana haÉ—awa da gudu da gudu.
Akwai haske a bangaren tunda akwai nepa a lokacin.
Tana shiga falon shuru kamar ba kowa amma ta ji ƙamshin turaren shi tana ɗago idanuwa suka haɗu da na shi kallon mai kassara sauran kuzarinta.
Yana hakimce a saman kujera, sanye yake da ƙananun kaya wando baki rigar fara mai layi layin baki sannan tana da dogon hannu.
Kafa É—aya kan É—aya.
Ta daɗe ba ta gan shi ba, tun ranar da kalamansa suka ɓata komai.
Ta ga ya ƙara yi mata wani kyau da ƙwarjini ne
Cak ta tsaya ta kasa ƙarisawa domin mutuwar jiki ne ya same ta duk ƙarfin gwiwan da ta zo da shi ganinsa kawai da ta yi yana neman ya ruguza shirinta.
Saurin kauda kai ta yi idanuwanta na tara ƙwalla amma ba ta bari sun zu bo ba.
Shi kuma a hankali ya miƙe yana takun nan na sa na ƙasaita har zuwa gaban ta.
Ya tsaya lokaci É—aya yana tusa hannuwansa a cikin aljihun wandon jikinsa.
Kafe ta da idanuwana ya yi yana kallonta kuma tana jin kallon a cikin jikinta.
Amma ta ƙi yarda su haɗa ido, kar ya yaudare ta da kallon shi ta ji kawai ta bar maganar ba tare da ta bi kadin wulakancin da ya yi mata ba.
Shi kuma Lamiɗo ƙura mata idanuwa yake yi sosai so yake yi ya fahimci ko tana da wata matsala ne! Domin abin da take yi ya yi kama da na wanda bai da lafiya
Abin da ta yi ma Ammah ya yi masa ciwo sosai, maganar da ya yi ɓacin rai ne da kishi amma har a zuciyansa ba haka ba ne ko giya ya sha ba zai iya sakin Ummu Salma ba. A lokacin dai ya ji in har ta fi son wani akan shi zai iya sakinta sai da ya tafi Daura tunaninta ya hana shi sakat daga nan ya gane ba zai iya rayuwa babu ita ba.
Ya fahimceta amma abin da ta yi ne ba ta kyauta ba amma ta kasa gane laifinta.
A zuciyarsa kawai in ya tuna da kalamanta sai ya ji yana fushi wai ita ke cewa ya sake ta ɗin mana sai me? Bai taɓa tunanin haka daga gare ta ba. Da farko ya yi fushi amma daga baya ya sauka ya yarda da maganar Mami tana bukatar kulawa saboda yanayin da take ciki.
Ya ɗauka da gaske ta yi nadama za su daidaita kan su, Sai ga shi ita ba haka take so ba tun a ranar da Mami ta ba ta wayar ya son rigima take ji ta ƙi magana sannan ta kashe wayar, ya kira wayarta kuma ya san tana gani ba ta ɗauka ba.
Shi kuma ya ba ta lokaci ne ba ya so yadda take cikin ɓacin rai ya sake nemanta a tunanin shi in suka koma can gidansu sai su zauna su daidaita kan su, ya dawo idanuwansa na kewar ganinta amma ba ta fitowa, yana da dalilin da ya sa bai neme ta ba ai shine a gaba da ita. Ita ya kamata ta fara neman shi a matsayin shi na namiji kuma mijinta.
Duk da haka ya sauke komai na shi ya yi niyyar a daran nan zai bita ya lallasheta ya É—auketa su koma gida da safe kuma su bi jirgi zuwa Lagos.
Amma sai ga saƙonnin ta masu rikitarwa.
"Why Ummu Salama"
Yake faɗa a zuciyarsa duk da ranshi ya ɓaci ba zai biye mata ba. Gaskiya Mami ta faɗa tana bukatar lallashi duba da yanayinta. Duk da har Ammah cewa suka yi ya fita batun ta, ba zai iya ba ne duk mulkinsa da komai na shi zai rusuna mata in dai za ta haƙura.
"Ina saƙon?
Ya ji ta faÉ—a kai tsaye, sai ya É—aga idanuwana yana kallon ta.
Har tana miƙa masa hannu.
"A takarda ka rubuta ko a baki za ka faÉ—a mini?
Mirmishi ya yi ta kasa ma kallon fuskar shi ashe ƙaryan rashin kunya take yi.
"Ba anan zan ba ki ba."

Ya fada yana É—an lumshe idanuwana sannan ya sake buÉ—ewa a kanta sai da ta É—an yi baya ta daburce.
Matsota ya fara yi ta jingina da bango
"Hamma ka tsaya fa."
Take faÉ—a tana kare shi da hannayenta.
Ko kusa da ita ma bai yi ba.
Giransa ya sosa yana É—an mirmishi.
"Ni ba taɓa ki zan yi ba."
"Mu je ciki ki karɓa saƙon na ki."
Ya faɗa yana wucewa, ɗakin farko na jerin ɗakunan ukun dake falon ya nufa ya shiga, kafafunta suka lamkwashe saƙon me? Sakin na ta ya yi da gaske?
Ƙirjinta ya buga wani hadari ya ruguzo mata a saman kanta.
Ta kasa gaba ballatana baya domin kafafunta har sun yi wani gara gara.
"Ki zo ki karɓa mana?
Ya leƙo yana kallonta.
"Ko ba ki so ne?
Ya faɗa yana shafa sumar kansa. Daƙyar ta ja kafafunta ta bi bayan shi. Ita ce ta ce ya yi abin da ya furta amma barazana ce ba ta taɓa tunanin zai iya sakinta da gaske ba.