← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 75

Sashe 71

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa ta saka yau ita abar girmamawa ce ga kowa, kowa na son ya raɓe ta saboda ta zama wani abu. Shamsiya ko kamar ta yi mata sujjuda, rayuwarsu akwai tausayi har ciki ta sake samu bai zauna ba.
Shi yasa itama Ummu Salma ta yi magana suka ɗauki Shamsiya ta a cikin agent ɗinsu, tana kawo musu sunayen mabuƙata su tantance sannan duk tallafin da za a ba da ana bayarwa da ita, ita kanta Baɗɗo da ke adawa yanzu ta daina daman ta ce burinta kenan Ummu Salma ta samu arziƙin da watarana daga Shamsiyar har Habib a ƙarkashinta za su samu sai ga shi ya faru tun a duniya suna ganin ƙarshen su.
Received at 08:04
14 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
A Masarautar Daura wannan karon aka sake yin taron sunan Hadi wanda Ummu Salma ta ce za su dinga kiran shi Sadauki, tabbas mai sunan Baffa ya cancanci ya zama Sadauki finally dai ta samu mai sunan Baffa shi ya sa aka ce wani hanin ga Allah baiwa ne sannan wani jinkirin alheri ne. Taron sunan da ya haÉ—a manyan mata masu ji da kansu, ma su ji da mulki da kuÉ—i bayan BaÉ—É—o yanzu Ummu Salma na da wasu mutane da suke da muhimmanci amma ba wanda zai kama kamar BaÉ—É—o a wajenta.

Akwai Badi'a ga Sakeena mutanen England ga Amaryan Gwamnar Katsina duk da ta girme mata sannan ga Hajiya Mardiya ga kuma Hajiya Hauwa(Anty Hairi) sai kuma Dr. Fadila Kabir, Anty Fadila suna da alaƙa da Masarautar Bunza shi yasa Ummu Salma ta san ta, ga Barrister Salamatu Doma, ga Hajiya Aisha Ahmad iya, ta santa sanadiyar Foundation, mace ce mai son kyautatawa da taimakon marasa karfi ga kuma Hajiya Zainab Inuwa(Antysis) itama sanadiyar Gidauniya ta san ta ana ɗaukan nauyi tana kai ruwan sadaka asibitoci da makarantu, itama mace ce mai kirki da karamci. gidauniyar Sarauniyar Daurama ma na shirin tallafa mata domin aikin alherin da take yi ya zagaya garin Funtu'a gabaɗaya.

Kamar sunan Banafsha wannan sunan ma haka Ummu Salma ta sake tara dukiya kamar ba son zafin ta ba wannan karon Ummu Balki da Ummin ikki sai da ta yi sati uku da haihuwa suka koma Mubi Mami ta zo taron suna ba ta kwana ba ta koma gidan ba kowa tunda Barira ta yi aure ba ta samu wata mai aikin ba sannan ga makaranta, Allah ya sa ma Islam na kusa to itama karatu ya saka ta gaba ko sunan Sadauki ba ta samu zuwa ba.

Bilkisu ta shigo ta yi barka ta dauki Sadauki ta gani, daga nan ba ta ƙara shigowa ba amma ta aiko da kayan jarirai masu kyau ta ce a ba ma Sadauki Ummu Salma ta ji daɗi a zuciyarta ta ce Bilkisu ta fara canzawa, sannan har shi kan shi Mai martaba da ta faɗa masa ko da bai yi magana ba amma gefe da gefen bakinsa ya motsa alamun ya ji daɗi.

Rayuwa ta cigaba da gangarawa gefe ɗaya Ummu Salma na renon Sadauki da taimakon su Harira sannan tana gudanar da Foundation ɗin su ƙarshen shekara na yi Bilkisu ta tafi Canada shekara ɗaya za ta yi sannan ta dawo yara kuma suna tare da Umma Salma ga Hadimai su Anitha ma duk suna nan amma sukan je garuruwansu hutu lokaci bayan lokaci.

Zuwa lokacin gidauniyar Ummu Salma ta kafu sosai sannan kuma yanzu ƙokarinta samar da wajen da za ta buɗe kamar makarantar koyon girki sun fara magana ma da Mai martaba ya ce za a gina mata tunda tana ra'ayi.

A lokacin shekaran Baffa uku da rasuwa shi kuma Lamiɗo yana da shekaru biyu a saman Ƙaraga.
Abubuwa sun canza domin ko can jimeta ma an ƙara gyara gida ya zama wani mansion. Hamma Saddam ya samu aiki da kamfanin leadership dake Abuja kiran sa kawai aka yi yaje aka yi masa gwaji kuma ya haye.

BaÉ—É—o ma wani cikin ne da ita amma hakan bai hana ta aikin alheri ba.
Shekaran É—aya Bilkisu ta yi a Canada ta dawo Mai martaba ya kai mata ziyara har sau biyu tana dawowa sai ga ta da ciki har ya fito ma.

A shekaran Ummu Salma ta je Saudiya ta sauke farali ita da Mai martaba LamiÉ—o suka je Bilkisu tana gida tare da yara, yanzu bayan dawowarta tana duba majinyata a clinic É—in Masarauta bayan ta dawo daga Canada kuma sai ta koma aiki da Federal goverment.
Bilkisu ta haihu ta ƙara samun namiji Lamiɗo ya ba ta zaɓi ta zaɓa masa suna Aliyu.

Burin Ummu Salma ya cika ta je ka'aba ta yi ma Baffanta addu'a ta yi ma mijinta da yaransu ba wanda ba ta yi ma addu'a ba.
Foudation É—inta na ta cigaba sun samu nasaran buÉ—e ofishi a Jimeta tunda nan ne mafarin komai, sukan je Jimeta da Babban salla in suka je ana kai Hanan gidan mahaifinta ta kwana biyu.

Mai martaba Lamiɗo ya cika alƙawari an siya fili a cikin garin Daura an kira magina da mazana sun zana, magina sun fara ginin center ɗin da Ummu Salma za ta buɗe na koyon girki, sannan duk shekara yanzu suke ba da tallafin jari ga mata, kuma alhamdullah matan da suka samu tallafin sun samu abin dogaro Shamsiya yanzu sabulun wanke wanke take siyarwa da turaren ƙamshi na ɗaki har da na tiolet a jarin da aka ba tana kuma ganin cigaba har Habiba ta kawo an ba ta jari da wasu
Received at 08:04
9 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
ƙannen Habib ko bakomai su ci albarkacin Hanan.

Sai da suka samu ofishin Jimeta sannan suka samu na Katsina Hajiya Mardiya na kula da shi
Lamiɗo na da shekara huɗu a kan ƙaraga Fulanin Daura ta rasu mai Martaba mai murabus da ake ganin kamar shi ne ba shi da lafiya to ta riga shi tafiya mutuwar da ta girgiza ahalin Muhammad Shitu tsohon sarki gabaɗaya an yi rashi a masarautar Daura, bayan rasuwarta Lamiɗo ya so Ammah ta dawo Masarauta da zama ta ce tana nan a Jimeta. Tunda kuma Lamiɗo ya yi magana ta ce a'a ba wanda zai iya tanƙwarata.

Tuni an saka Banafsha a makaranta da itama bakinta ya buɗe, wannan karon sai da ta yaye Sadauki sannan Ummu Salma ta ƙara samu cikin. Kuma a lokacin ma ta gama yanke shawaran za ta koma makaranta ta haɗa degre ɗinta akan abin da take so wato girke-girke tunda yanzu tana mu'amala da mutane sosai.

Tana faɗa ma Mai martaba, shi kuma ya ba ta goyon baya ta siya Jamb ta yi a garin katsina, kowa ya ji za ta koma makaranta sai ya yi mamaki Hamma Kabiru ya fi kowa jin daɗin haka ya ce lokaci bai ƙure mata ba.
Ta samu nasaran cin Jamb, ta yi kuma post UME ta samu nasaran samun course É—in da ta ke so.

Bechelor of Arts BA in culinary Arts 4years program ne a Alƙalam University Katsina. Mai martaba Lamiɗo ya siya mata ƙaton gida ta koma can da zama, amma tana zuwa weekend duk sati ko shi in ya samu sarari ya leƙata tana tare da Harira da Asabe sai kuma direba guda ɗaya sai kuma escort mace tana aiki da DSS, sai maigadin dake kula da gidan suna zaune tare da ita yara kuma suna Daura Sadauki ne kawai tare da ita sai cikin jikinta.

Da ta fara karatun ta ji kamar ta bari saboda wahala amma da ta yi kamar ta juya sai kafaɗan Lamiɗo ya tare ta sai ta sake miƙewa ta jajirce, tana kuma karatunta tana cigaba da gudanar da gidauniyarta tare da tsare tsaren buɗe SARAUNIYA DAURAMA CATERING CENTER DAURA.

Tana so a yi gagarumin biki za ta gayyaci duka manyan Food bloggers na arewa wajen taron buɗewa sannan ɗaliban farko kyauta za su samu karatu, sannan za a ɗauki ƙwararrun malaman da za su dinga koyarwa itama tana so ta zama malama burinta ta gama karatu ta kara CHEF a gaban sunan ta.

Wato CHEF UMMU SALMA MUHAMMAD LAMIÆŠO..
burinta guda É—aya ya cika sai godiya yanzu É—ayan ne take fatan ya cika kamar yadda ta É—aura niyya.

*Janafty*
Received at 08:04
7 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
RUFEWA.

BAYAN SHEKARA HUÆŠU.

Ƙarfe shidda na yammacin ranar laraba suka iso Daura. Direba ke jan ta a sabuwar motar ta corolla ta kamfanin Toyota shi dai Allah ya ƙara masa lafiya Mai martaba Sarkin Daura Muhammad Lamiɗo ya fi son kamfanin toyota in dai a bangaren motoci ne duka motocinsa kamfanin ne har waɗanda yake siya musu suma kamfanin Toyota ne.

Tare da Harira suke tafe sai Rukayya(Fulani) sai matashin cikin jikinta É—an wattani biyar, sai dogari guda É—aya da escort É—in ta Fadila.

Harira ke riƙe da Fulani da jakar tarkacen kayanta dake ciki, ƙaramar jakar Ummu Salma tana hannunta ta hana Harira ɗauka kar kayan su yi mata yawa, tunda itama ba ita kaɗai ba ne akwai ƙaramin ciki a jikinta.

Harira yanzu matar aure ce, direban masarautar da Mai martaba ya ba ta suka koma katsina shi ya aureta a shekaran da ta gabata suna zaune a katsina tare da ita, Harira yar amana ce a wajenta ba ta fatan su rabu har abada shi yasa ta fi kowa jin daÉ—in auren Harira a kusa da ita. Sannan ita karan kanta ta ba ta ma jari ta fara kasuwanci domin dogaro da kanta.

Sanye take da atamfa mai blue sai abaya kalan blue da mayafi takalmin kafarta mai sauƙin tudu ne, Ummu Salma Sarauniyar Daurama ta yi wani irin kyau da jikin murjewa tana tafiya ɗaya bayan ɗaya Fadila da Harira na take mata baya, dogarai da Hadimai na zubewa wajen kwasan gaisuwa.
Chapter 71 · 0% Book details