← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 75

Sashe 54

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar ta kama bakwai da haihu itama ta sha kwalliyarta cikin leshi , kamar ba asibiti ba.
Sai ga Bilkisu ta yi ma Mami voice call sun gaisa.
Ta ce a ba ma Ummu Salma wayar, suka gaisa ta yi mata barka a status É—in Adda Safina ta ga sunan jaririyar Fatima.

Da yake ba su saba waya ba, kawai dai ta yi mata barka ne kawai sai ta haÉ—a ta da yara Sultan da su Beena har da Hanan suna ta cewa suna son ganin jariri.
Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 👏 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai Mami ta ce a kira video call, Mamin ta karɓi wayar ta kira yaran suka ga ƙanwarsu suna ta zillo a waya kamar za su faɗo ta cikin wayar lokacin sun yi shirin makaranta ne safiya ce a can Nigeria domin uniform ne ma a jikinsu. Har su Sabuwa sun leƙo sun gaishe da Ummu Salma da su Debora suna ta murna da suka ga yar jaririya fara sol da ita.

A cikin masu yi ma Ummu Salma murna da status É—in da ta saka har da Shamsiya da yake ta yi saving É—in lambarta. Ta gani ta yi mata magana da tambayan ta haihu ne? ta amsa mata da eh, ta yi mata barka da murna har tana cewa za ta zo barka tana ina ne?

"Ina Egpyt a can na haihu amma zan dawo Jimeta nan ba da daÉ—ewa ba"

Jiya sun yi magana da Hamma in suka dawo Jimeta za ta zauna kafin komai ya kamkama su koma Daura gabaÉ—aya.

Shamsiya ta yi mata alƙawarin za ta zo, in ta dawo ta kira ta ta ce in sha Allahu.
Tausayin Shamsiya take ji, duk da ta tsane ta a baya amma yanzu tausayi take ba ta, Habib ne har abada bai taɓa ba ta tausayi ba.

Abin da ya aikata ne ya ga sakamakon sa. Hanan ɗin da ya so ya salwartar ita ce dai sanyin idaniyarsa. Ba shi da wani ƙwai a duniya Allah ne ya jarabce sa.
Kuma ya ga ishara ga rai ga lafiya amma haihuwar ce Ubangiji ya hana shi domin nuna masa ishara kan niyarsa ta baya.

An yi yanka raguna huÉ—u a can Adamawa Ammah ta yi taron suna an ci an sha, naman suna kuma an soye shi an yi rabo sai fatan Allah ya raya Fatima Banafsha.

Sakeena daga England ta yi ma Ummu Salma barka haka ma Badia'tu daga Nigeria sai Gimbiya Shahida da suka sake yin magana Hajiya Kilishi da Hajiya Zaliha ba ma sau ɗaya ta yi magana da su ba Saleem dai ba su yi magana ba ya dai yi mata saƙon ta ya murna da Allah ya raya ta chart.

Kwanan Hamma Kabiru uku da zuwa suma suka fara shirin tahowa gabaÉ—aya sun sake magana da Hamma sau É—aya ya ce tunda likitocin sun ba da tabbacin ba wata matsala to ba amfanin zaman su taho kawai gida.
Sai da suka kwana ashirin cif da saukan su a ƙasar Egpyt a daran ranar Jirgi ya kwashe su zuwa Nigeria.
Ummu Salma da Banafsha sun sha hotuna da larabawan kasar Egypt kafin su baro kamar kar su dawo saboda yanayin kasar akwai daÉ—in zama.

Ta Abuja suka sauka da safe a gidan Hamma Jibo suka fara yada zango
Nan Mami ta fara gasa jikin Ummu Salma can fa ba sa bari ta yi amfani da ruwa mai zafi saboda BP ita kanta Banafsha da ruwa É—umi kawai suke mata wanka wata rana ma goge jiki ne.

Nan suka kwana Adda Nauwara ta dama mata kunun tsamiya ga ferfesun ganda da na kayan ciki, shi Hamma Kabiru a jiya ya bi jirgi zuwa Taraba.
Ya ce za su dawo tare da Adda Safina da yara in sun koma gida.

Su kuma sai a washegarin bayan sun kwana sun hatse suka bi jirgin Yamma zuwa Adamawa Yola.
Hamma Saddam ya je da motar Hamma LamiÉ—o ya É—auko su zuwa gidan Ammah.

Tuni an gyare É—akin Umma Salma nan ta sauka daman ta ce ma mijinta anan wajen Ammah za ta zauna ya ce yadda take so haka za a yi.

Gida ya cika da su Adda Suwaiba da su Ummi ikki É—akin Umma Salma cike ana ta hira ana mayar da magana da labarin komawa Daura Adda Suwaiba na faÉ—in za su sha bikin naÉ—in Sarauta har tana cewa kowa ya tanadi kuÉ—i shigar manyan mata suma za su yi ana ta dariya.

Ummu Salma ta tura ma Lamido sakon sun sauka.

"Mun dawo gida Mai martaba na"

"Welcome back home Sarauniya ta"

Ta yi mamakin yadda ya samu sararin bata amsa shi da yake can yana fama da sha'anin mulki ga shi komai sabo zai gani tunda baƙo ne hakan a gare shi a matsayin shi na Sarki.

Kowa sai mamakin kiban Ummu Salma yake yi ana cewa ƙasar waje ta karɓeta. Banafsha ma ta yi ɓul, kuma suna dawowa Ammah ta fara mata kunu gero da na shinkafa sai ga ruwan nono, Ummin ikki ke yi mata wankan jego, Mami ta koma Kaduna ita da Barira ta duba gida tunda ta daɗe bata nan.

In LamiÉ—o ya samu dama suna waya da Ummu Salma bayan kwana É—aya haka watarana ma duk dare.
Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 🔥 1, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Yanzu a ƙarshen watan nan Mai martaba mai murabus za su yi ƙaura zuwa can gidan shi na cikin garin Daura an tsara za a yi shagalin naɗin sarautar Lamiɗo a farkon watan December su Hajiya kilishi sun haɗu sun tattauna da cewa za a haɗe shi da taron sunan Banafsha a Masarautar Daura gabaɗaya.

Da suka zo barka ne suka faÉ—a ma Umma Salma.
Hajiya kilishi, Hajiya Zaliha da Hajiya Binta sai Gimbiya Shahida da Gimbiya Amaratu da matar Waziri da Shamaki.
Sun kawo akwati guda goma biyar na mai jego, biyar na Banafsha, sai kuÉ—i a takarda miliyan biyu daga Fulanin Daura.

Sai kyautar mota sabuwa GLK daga Uban LamiÉ—o kakan Banafsha tsohon Sarki mai murabus, Alhaji Dr Nasiru Muhammad Shitu mota na can masarauta tana jiran su.

Wani kaya sai amale, sun ce ranar tara ga watan December za a yi naÉ—in saboda haka Ummu Salma ta yi magana da LamiÉ—o, su fara shirin komawa can Daura domin gabatar da shirye shirye, ga shi kuma za a haÉ—e shi da taron suna
Sannan sun ce duk waÉ—anda za su je akwai jirgin da Mai martaba zai ba da, sannan za a turo lafiyayuun motoci daga Masarauta ta É—au mutane tare da wasu kaya.

Lokacin da suka zo Shamsiya na gidan tare da Habiba da Gwaggo sun zo barka tunda Shamsiyar da ta gaji jiran kiran Ummu Salma sai ta kira ta shi ne Ummu Salma ta sanar da ita ta dawo tana gida shi ne su ka zo zuwan su kenan ma sai ga baƙin Masarauta.

Sai suka koma gefe suna ganin arziƙi, Habiba a fili take faɗin Allah ya rabamu da talauci. Domin talauci bai yi ba Annabi ma Salallahu alaihi wasallam ya nemi tsari da talauci.
Sai da su Hajiya Kilishi suka tafi sannan aka ma tuna da su Shamsiya.

Da gayya BaÉ—É—o ta ce in za samu zuwa suna gayyatarsu Daura naÉ—in Sarauta da taron suna tun kafin Shamsiya ta amsa Habiba ta ce za su je. Domin za ta je ta ga kuÉ—i da masu kuÉ—i.
Shamsiya na faɗin sai sun tambayi Habib a zuciyar Habiba ta ce bai isa ya hana ta ba, duk da yanzu abubuwa sun ragu tunda yana koyarwa yana kuma aikin karfi kamar aikin gini sannan ga Shamsiya tunda ya aure ta ya samu wasu sauƙin abubuwa. Amma a rashin mutumcin Habiba ba wanda ya ragu ita sai Habib ya sake ta shi kuma ya ce da ita aka fara da ita kuma za a gama. Suna gidan har yamma sannan suka tafi.

A daran Ummu Salma ta kira Mai martaba mai murabua daman da suka dawo sun yi magana sau É—aya ya yi mata barka da samun kai lafiya. Godiya ta yi masa ya ce bakomai kin iya haihu tunda kika haifi Batula. Ya ce yana jiran amaryan sa ta zo ta gaishe shi. Ummu Salma ta amsa da in sha Allahu cikin ladabi mai yawa.

Da suka yi waya da LamiÉ—o ta faÉ—a masa zuwan su Hajiya kilishi duk da ya san da zuwan su amma bai gwalese labarin ba.

FaÉ—a mata yake yi an gama gyaran Masarauta Bilkisu za ta fara yo gaba ita da yara daga Lagos daga baya ita Ummu Salama sai ta taho daga nan Adamawa ta ce babu matsala hakan ma ya yi.

*Janafty*
Received at 15:16Reactions: ❤ 19, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

BAYAN SATI ÆŠAYA.

Ta ko'ina shirye-shirye ya fara gudana. Ga shi yau har biyar ga watan December saura kwana huÉ—u bikin naÉ—in sarautar LamiÉ—o tare da taron sunan Banafsha.

Tuni Mai martaba tsohon Sarki mai murabus da iyalansa sun bar cikin masarauta sun koma gidansa dake cikin garin Daura ɗan gaba kaɗan da masarautar, shi kenan fa haka rayuwa take ko mutuwa ne haka za a yi a gama suma ga shi kamar ba su zauna a cikin masarauta ba yau ga shi zamansu ya ƙare daman in yau kai ne gobe ba kai ba ne. Allah ya sa mu dace.

LamiÉ—o ya so Fulani ta zauna tare da shi a Masarauta ta ce ba za ta zauna ba duk in da Nasiru yake tana tare da shi. Tare da ita aka koma wancan gidan shima kato ne mai kyau na alfarma da zanen gidan Sarauta a jikinsa. Masarauta kuma tuni ana ta gyara an sauya tsarin duka bangarorin gabaÉ—aya komai sabo ake saka kama daga furnitures da komai da fenti sabon Sarki sabon gyara.
Tuni tsarin katin gayyata har ya fara isa ga manyan kasa da za a gayyata. Masu Sarautu ma'aikatan Gwamnati, gwamnoni yan kasuwa yan majalisu da sauran su.
Chapter 54 · 0% Book details