← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 75

Sashe 2

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bini bini ta juya tana kallon Baffa tana taba shi ta ga dai yana ta barcinsa.
Itama barcin ne ɓarawo ya sake tafiya da ita.
Received at 09:09Reactions: ❤ 13, 👎 1, 🥰 1, 🤔 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Sai dai kamar a cikin barcin ta yi mafarkin Baffa na kiran sunanta ta farka a firgice.
Sai tarin shi ta ji daman ba ta kashe hasken É—akin ba ta yi kanshi cikin firgicewa

Tari kawai Baffa yake yi har gadon da suke kwance yana jijjiga.
ÆŠago shi ta yi ya jingina da filo tana shafa masa bayansa lokaci É—aya tana yi masa sannu.

"Sannu Baffa me ya faru ne?

"Tari ne kawai ya sarƙe ni."

Ya amsa mata cikin rawam murya. Har a lokacin gumi yake yi ta sauko daga kan gadon ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta kunna filitar kitchen ɗin ta dauko kofi ko da ta dawo tarin ya dawo ma Baffa jikinta ba in da ba ya rawa ta durƙusa ta tsiyaya masa ruwan a kofi ta zauna a gefen shi ta ɗago kan shi tana ba shi ruwa jikinta ya saki ne lokacin da ta ga ruwan da take ba ma Baffa yana dawowa ta gefen bakin shi sannsn tarin bai tsaya ba.

Har yana hawaye wasu suna zuba wasu na sake tunkuÉ—owa.
Ammah ta ruÉ—e hankali tashe take kiran sunan Baffa.
Amma ba ya iya amsawa tarin ya sarƙeshi kamar wanda ya ci wani abu ya sarƙe shi.

Idanuwansa sun yi jajir gwanin ban tsausayi.
Amma ya miƙe tana faɗin bari ta je ta taso su Saddam su zo su tafi asibiti amma sai Baffa ya riƙo hannunta ta dawo ta zauna tana yi masa sannu.

"Ka bari na je na taso su, ba ka da lafiya Baffa mu je asibitin tarin nan naka ya yi yawa."

Bai saki hannun na ta ba, kan shi ya fara girgiza mata tarin ya É—an lafa masa.

"Ki yi haƙuri Jamila."

Baffa ya faÉ—a cikin dashewar murya.
Hawaye na zubo masa ta gefe da gefen kunnuwansa.

Kamar an kwarara ma Ammah ruwan sanyi haka ta ji, ta kasa magana kawai ta kafe Baffa da idanuwana.

"Ki yi haƙuri lokaci ya yi da za mu yi sallama da juna haka nan."

Ya faɗa tarin na sake kama shi, Ammah ta durƙushe a ƙasa a gaban shi zuciyanta ke bugawa hannunta da jikinta babu in da ba ya rawa

"Baffa me kake faÉ—a haka? Ina kuma za ka je?

Bakinta na sarkewa saboda tashin hankali.
Kuma ya riƙe hannunta gam yaƙi sakinta.
Cewa ya yi ta zo ta zauna dole ta mije ta zauna a gefen gadon ya janyo jikinsa da ya saki ya É—ora kan shi a samam cinyarta suna masu kallon juna.

"Ki yi haƙuri Jamila lokaci ya yi."

Sai ga hawaye, yaushe ne rana na ƙarshe da ta ga kukan Baffa? Duk da yana da raunin zuciya amma ba kuka irin wannan ba.

Ta san mutuwa tunda iyayenta sun rasu amma ba'a taɓa mata mutuwa ana ta zuru'an ba. Yadda Baffa ke yi kawai ya sa jikin Ammah ya saki gabaɗaya.
Baffa ya gama kwanakin da aka diɓo a duniya yau ko tana so ko ba ta so lokaci ya yi da Baffa zai tafi ya barta.

Yadda Baffa ke yi lokaci ne ya yi watakila ma mala'ikun ɗaukan rai suna cikin ɗakin. Tarin da yake yi na kiran ajali ne. Ba ta san a ina ta samun ƙwarin gwiwa ba amma jin bakinta kawai ta yi, tana maimaita ma Baffa kalmar shahada kuma sau ɗaya ta maimaita ya kama yana yi.

Baffa ya cika idanuwansa kamar suna kallonta amma ba ita yake kallo ba idanuwansa sun yi sama ya rufe kalmar shi ta ƙarshe da la'ila ha illallahu muhammdun rasulillah.'
A man cinyar Amma ya cika har a lokacin akwai danshi hawayensa a gefe da gefen kunnuwansa.

Ammah ta kasa gane a wani yanayi take ciki. Ta É—ago idanuwanta tana kallon agogo Uku da mintina arba'in na daren ranar Litini Baffa ya koma ga Allah.

Hannunta da ta ji ya sandare ta miƙa ta shafe idanuwan Baffa. Sannan ta yi jarumtar sauke kan shi a saman gado ita kuma ta sauko ƙasa ta durƙusa a gaban shi tana kallon shi.

Me take ji? Wani abu ne ƙullutu mai girma ya yi mata tsaye cak a wajen zuciyarta shi bai wuce ba shi kuma bai faɗa mata ba.

Baffa ne ya tafi ya barta? Ta kasa gasgasta abin da ya faru cikin mintina. Ga shi kwance kamar mai barci kamar ta kira shi ya amsa.
Wai ba ɗazu nan nan ba daɗewa suka gama hira tare da su Saddam ba lafiyan shi ƙalau fa, cewa kawai ya yi kan shi na ciwo ashe na ajali ne.

Hawaye ko kaÉ—an ba su kawo mata ba zuciyarta ta bushe, amma ta yi mata nauyi jikinta ya saki gabaÉ—aya.
Received at 09:09Reactions: ❤ 12, 😭 6, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta miƙe tana jin kamar ba ita ba. Tana jin ta kamar falle takarda saboda yadda take jin kanta. Gyara ma Baffa kwanciya ta yi akwai zanin ta a gefe ta jawo shi ta yaga shi da ƙarfin tsiya da kanta ta duka ta haɗa babban yatsun kafafun Baffa ta kulle su kar kafin safe su sandare. Sannan ta fita ta koma ɗakinta ta buɗe wardrope ta ɗau zaninta sabo ko taɓa sa shi ba ta yi ba ta zo ta rufe Baffa ruf daga kafafunsa har kansa.

Sannan ta shiga toilet ta ɗauro akwala ta zo ta shimfiɗa darduma ta fara sallla, ba ta san ko raka'a nawa ta yi ba ita kawai salla take yi da ta sallame ta sake miƙewa ga Baffa kwance a kan gado a matsayin gawa

Ta kasa zama ko na minti ɗaya ballatana ta yi wani tunani ji take yi kamar za ta haukace kamar ƙarya ne sai dai ba ƙarya ba ne ga Baffa nan kwance babu rai a tare da shi.

Ta yi salla har sai da kafafunta suka ga ji, har sai da ta ji an fara kiran sallar asuba a wasu masallatan da suke kusa da su. Sannan ta dakata ta zauna tana jan casbaha ta ƙura ma gawar Baffa idanuwanta amma ta kasa kuka ta rasa ma abin da take ji amma wani abu mai nauyi yana yi mata ɗaci ya tokare mata a maƙoshi ya kasa wucewa.
Tana nan zaune har lokacin salla ya yi ba ta iya tashi ba Hasbunallahi wani'imal wakeel kawai take maimaitawa bakinta na motsi kamar ba ta cikin hayyacinta

Daga tsakar gida ta ji muryan Saddam na kiran sunanta. Ƙofar dakin Baffa a buɗe take sannan akwai hasken wuta zumbur ta miƙe ba ta son ya shigo ya fahimci halin da ake ciki yanzu sai ta yi zaraf ta fito suka haɗu a tsakar gida.

"Ina kwana Ammah"

Bai fahimci yanayin ta ba ganin ta da hijabi bai kawo masa wani tunani ba.

"Ina Baffa? Har wasu masalatan fa sun tayar da salla?

"Ku je kawai, yau a gida Baffa zai yi salla ba ya jin daÉ—in jikinsa."

Ya ce Subhanallah me ke damun shi ta ce zazzaɓi ne.
Sai ya wuce yana faÉ—in to bari su je masallaci su dawo sai su shigo su duba shi ta amsa masa, bayan ficewarsa ta daÉ—e a tsaye

Baffa ke fara tashi, ya tashe ta ya yi alwala sannan ya fita ya tayar da su Saddam ya tada su domin su tafi masallaci.
Allahu akbar ga shi yau sun sun tashi amma Baffa bai tashi ba. ÆŠakin ta koma ta tayar da salla.
Sai da ta idar da salla sannan ta zo gaban gawan Baffa ta buÉ—e shi tana kallon shi kamar ta kira shi ya amsa.

"Allah ya jiƙan ka da rahama Baffa. Allah ya haɗa ka da mala'ikun rahama Allah ya sa su yi murna da zuwanka. Ubangiji ya karɓi baƙunci ka."

Ta kasa ƙarisawa tana jin wani irin abu na ta so mata.

"Allah ya haÉ—amu a darussalam."
Sannan ta miƙe ta ja zanin ta sake rufe shi.
Fita ta yi zuwa falonta ta É—auki wayarta sannan ta nemi gefen gado ta zauna ta kira wayar Abdulrahaman

Lokacin baya gida ya je masallaci Ummu Sulaim kuma ba ta ji kiran ba wayar tana chaji ne kuma a silent take. Ganin bai É—aga kiran ba sai ta kira Abdullahi

Shi ta same shi, domin ya dawo daga masallaci kenan ya kwanta wayar ma tana hannun shi ne sai ga kiran Ammah gaban shi ya faÉ—i kiran waya wajen shidda na safe Allah ya sa lafiya.

Sai ya É—aga wayar da sallama amma kirjinsa na duka.

"Baba."

Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi.
Ya ji wani kaifi a muryanta da zai ce bai taɓa jin Amma ta kira shi da wannan muryan ba.

"Na'am Ammah lafiya kuwa?

"Lafiya ƙalau ka taho gida yanzu."

"Amma me ya faru?

Ya faÉ—a yana saukowa daga kan gado cikin ruÉ—ewa jikinsa ya ba shi ba lafiya.

"Na kira Abdulrahaman bai É—auka ba, ka kira shi, shima ya taho gida yanzu."
Ammah ta faɗa tana ƙokarin daidaita yanayinta.

"Ammah wani abu ne ya faru?

"Ku zo dai. Ku zo gida"

Da sauri ta kashe wayar tana numfarfashi lokaci É—aya ta dafe kanta tana kiran sunan Allah.

Dai dai lokacin su Saddam suka dawo daga masallaci, hango Ammah suka yi a falonta ya sa suka shiga dakin suna gaisheta

Ta mike da sauri ba ta son su haÉ—a idanuwana.

"Ammah ya jikin Baffan? Mu je mu ga jikinsa na shi ko kuma kawai mu je asibiti ."

Abdulrahim ya faÉ—a Saddam ya ce shima dai haka ya gani.

"Yanzu haka maleria ce."

"Ba ta wuce ita É—in ce."
Received
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ammah ta yi gaba suka bi bayanta har zuwa cikin É—akin Baffa.
Ta tsaya a gaban gawan Baffa su kuma suna bayanta tunda suka shigo É—akin kamar an zare musu lakkan jiki ganin Baffa kwance rufe da zani ya sa suka fara kallon juna.

"Ammah zazzaɓin ne ya yi zafi haka?
Chapter 2 · 0% Book details