← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 75

Sashe 52

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai samu sararin kiran kowa ba, ba ya cikin natsuwarsa. Da Kabiru kaÉ—ai ya yi magana da asuba ma sun sake magana daman ya ce ya matsa a samu visa da wuri tunda gobe ne bakwai da haihuwa to ya kira shi ya ce Visa ta samu jirgin shi zai É—aga daran yau ta Abuja zai isa kasar Cairo a wayewar garin gobe. Da yake kuÉ—i ya saki a wajen Visa yanzu kuma kasar mu in dai da kuÉ—i abin da ma ba zai yuyu ba yuyu yake yi.
Received at 15:16Reactions: ❤ 5, 👍 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Bai kira Abdullahi ba saƙo ya tura masa na cewa ya tura masa kuɗi a siya raguna a yi ma jaririyar Umma Salama Shaƙika na suna, duk da tarin saƙonnin da mutane ke ta tura masa na fatan alheri bai buɗe ko ɗaya ba, har su Hamma Jibo duk sun yi masa saƙo ko zai iya duba wannan sai daga baya in hankalin shi ya kwanta wannan sabuwar rayuwar ta bi jikinsa tukunna.

A ranar ma ya gana da duka wakilan fada da hakimai manya da ƙanana sannan ya gana da shugaban dogarai da magajiyar Hadimai na bangaren mata, sannan ya nemi zai gana da sarakunan ƙauyakun dake zagaye da garin Daura da Katsina gabaɗaya.

Jakadiya kuma daman tana nan a matsayin jakadiyar Sarki mai zamani a yanzu kuma abin sha'awa a gefen Lamiɗo ƙanin sa ne Saleem tare suke gudanar da komai hakan kuma ya yi ma Mai martaba daɗi, ko bakomai Saleem ma zai sake taimaka masa sosai. Sabanin Yazeed da yake can ƙasar da yake karatu cikin takaici yana son mulki sosai ko daga yadda yake jin ƙansa yaro ne matashi amma yana da izza da girman kai har ya fi Sageer da yake yayan shi son mulki da izza. Mai martaba ya shammace su sosai da a ce mutuwa ya yi za a yi zaɓe sun tabbata Lamiɗo ba zai taɓa kai labari ba.

A daran kuma a bangaren Fulani ya ci abincin dare itama sun daɗe suna tattaunawa kamar dai Mai martaba mai murabus, itama sake nuna masa muhinmancin zamowar sa Sarki tare da tunasar da shi nauyin dake kansa ta yi. Kowa sai ya ce ya cancanta shi kuma yana ganin bai cancanta ba a shekarunsa na arba'in da haihuwa a duniya gani yake yi ya yi ƙanƙanta da hawa wannan ƙaragar sannan yana ganin ba zai iya ba amma Mai nartaba ya saka yaƙini akan shi da zai iya haka ma Fulani.

Itama ta yi maganar sunan jaririya yadda ya faÉ—a ma Mai martaba haka ya faÉ—a mata.

"Na yi magana da ita Ummu Salaman da rana, ta ce har yanzu ba ku yi magana ba"

LamiÉ—o ya jinjina mata kai.
Saƙo nan kawai ya tura musu daga ita har Bilkisu ba ma su ba, bai yi magana da kowa ba bayan Kabiru da Abdullahi. Fulani ta ce ya kama ta ya neme ta su yi magana duk asan abubuwa sun zo ba yadda aka yi tsammani ba.
Amma dai ya kira ta tunda haihuwa ta yi, ko yaya ne za ta ji daÉ—i. Ya amsa ma Fulani a ladabce da cewa zai kira in sha Allahu.

Shi yasa yana komawa bangaren shi wajen sha ɗaya na dare ya yi wanka ya yi shirin kwanciya lokacin sha biyu na dare a Nigeria yana tunanin Ƙarfe ɗaya na dare a can Egypt tunda tsakaninsu da Nigeria awa ɗaya.
Ya ga saƙon Aminin shi ma da cewa ya isa Abuja tun da yamma zai tsaya gidan Hamma Jibo, ƙarfe ɗaya na dare jirginsu zai ta shi. Ya ga saƙon amma bai ba shi amsa ba lokacin yana ganaawa da malaman fada ne.

Datar shi daman a kunne ta ke a kodayaushe Ummu Salama ya duba tana online sai ya kira ta vioce call har sau biyu ba ta É—auka ba, ya san cewa ta yi barci tunda can dare ya yi nisa sai kawai ya yi ma Bilkisu waya direct call. Kira É—aya kamar wayar na hannunta ta É—aga kiran shi.

"Ranka ya daÉ—e"

Ta faÉ—a cikin zumuÉ—i domin wayar na hannunta tana I.g tana kalle kalle.
Ita fa ba ta san haka zamowar matar sarki ke da daraja ba sai da ta zamo, ta shaida zamowar yar Sarki da matar Yarima amma zamowa Gimbiya ne sai yanzu ta san yadda ake ji.
Ashe ko a baya kishi ne ya rufe mata idanuwana take ganin gwara Lamiɗo kar ya zama Sarki da ya zama Sarki ya ƙaro auro, yanzu kuma wannan ba ya gabanta tunda dai ta zama Gimbiya tana tunanin ta sha gaban kowa. Har Umma Salaman ta manta da ita, duk da ta ga jaririyar su Hamma Saddam na ta sawa ba ta da lambarta ba ta yi mata barka ba amma ta kira Ammah sun yi magana.

Tun yanzu har an fara kiran ta Gimbiya Bilkisu, kafin ta shiga Masarautar Daura ta fara zuba mulki da iko lokacin da ta ga kiran Lamiɗo ta ɗauka wasa ne domin tun saƙon da ya tura mata ta chart ba ta sake jin sa ba.
Shi ya sa jikinta na rawa ta daga kiran a muryanta ma za ka fahimci tana cikin tsananin farinciki.

Gyaran murya ya yi,amma bai yi magana ba. Shi fa mulki ba ƙarya ba ne yawo ma yake yi a cikin jini. Ko ba ya so yanzu shi Shugaba ne sannan wakilin Alumma, ba ya ma sanin lokacin da komai na shi ke sauyawa yanzu ko magana zai yi za ka fahimci natsuwa da kamewa a cikinta.
Received at 15:16
10 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Ranka ya daÉ—e muna murna ni da yara mun yi kewar ka."

Ta sake faÉ—a cikin bayyana farincikinta.

"Congratulations Papa. Allah ya taya ka riƙo."

"Amin"

Karo na farko da ya yi magana sannan a kame ya ce ya gida yana fatan tana lafiya tare da yaran gabaÉ—aya.?
Ta ce duk suna nan lafiya sai dai kewarsa.

"Yaushe za ka zo?

"Ku ne za ku taho."

Ya faÉ—a a rabe kafin ya sanar da ita cewa in komai ya daidaita an gama gyara Masaurata za su tattaro su dawo nan gabaÉ—aya.

Bilkisu ta washe baki kamar yana ganin ta, murna da farinciki sun cika ta. Tana tambayan shi wai dukkansu gabaÉ—aya har da su Debora ya ce in tana so ba shi da matsala.
Farincikin Bilkisu ya kasa ɓoyuwa, tana faɗa masa Umman Kano ta ce ta kira shi ba ta same shi ba, ya ce bai ɗaga wayar kowa ba amma daga baya zai kira ta.

Sun jima suna mgana yara daman ta ce sun yi barci amma ba su da magana sai na shi, ya ce yana gaishe su zai samu lokaci ya kira lokacin da suke gida sun yi maganar makarantarsu, yanzu sun kusa fara jarabawar second term ne, wataƙila ma ba lalle ko an fara jarabawan a gama da su ba da zaran lokaci ya yi za su bar Lagos gabaɗaya su koma Daura.

Har suka yi sallama bai yi mata maganar Ummu Salma ba, itama ba ta yi masa ba daman kuma shi ba zai yi ba. Bai taɓa kawo mata maganar ta ba in dai ba ita ta kawo ba ko ta kawon ma yana kaucewa.
Lokacin da suka gama waya da Bilkisu É—aya saura na dare sai ya sake kiran Ummu Salama ta vioce call, har ya cire rai da zai same ta sai kuma kawai ya ji ta É—aga kiran.

"Hello."

Ummu Salma ta faÉ—a cikin barci, barci take yi ba ta ma ko duba mai kiran ba. Cikin magagin barci ne wayar ta dame ta da kara ta zura hannu idanuwanta a rufe suke.

Ta ce Hello amma ta ji shuru ba a yi magana ba ta ƙara cewa Hello nan ma shuru gyaran murya da ya yi ne ya sa ta fahimci wane ne.

Da sauri ta watsaƙe ta miƙe zaune akan gadon da take, daga gefen gadon ta ta latsa wani abu sai fitilar ɗakin ta kawo gabaɗaya haske ya haskaka ɗakin ta cire wayar a kunne ta duba sai ta ga Hamma ne yake kiran ta.
Daman tunda ta ga saƙon shi kewar sa ya ta so mata. Ko ba ta ganshi ba ta yi magana da shi ko ta ji sanyi.

Ta mayar da wayar kunne a shagwaɓe ta ce.

"Hamma."

"Hamma ka manta dani."

"Ka manta da ƙanwarka."

Sai da ya yi mirmishi, gefe da gefen bakin shi suka motsa.
Mirmishin da tun da ya zama Sarki bai yi irin shi ba.

Shi a wajenta ba Sarki ba ne mijinta ne da kuma Hammanta.

Kuka kawai ta saka masa tana masa shagwaɓa da rigiman ya manta da ita.

"Shike nan haka ake yi tunda ka zama Sarki ka manta da ni"

Ta gama faÉ—a har tana matse murya, kuma kukan da gaske take so ta yi.

"I'm sorry."

Ya furta a hankali.

"Ba wani sorry, na haihu amma ba ka damu da ni ba ballatana jaririyar da muka haifa."

"I'm sorry na damu mana"

Ya furta a hankali yana mai lumshewa idanuwana ya san halinta da rigima daman.

"Ummu Salama."

Ya kira sunanta a kausashe.
Bai jira ta amsa ba ya cigaba da faÉ—in.

"Ba ki san na zama Sarkin Daura ba ne? Abubuwa sun zo ban shirya musu ba."

"Ni ina ruwana da zamowarka Sarki, Ni Hamma na sani, da mijina ba ruwana da wata Sarauta."

Ta gama faÉ—a har tana tura baki kamar yana ganinta.
Ya yi mirmishi mai sauti.

"Ummu Salama."

"Mu yi video call?

Ya tambaye ta cikin wani narke murya, yana kwance ne amma kuma kewar Ummu Salama duk ta gama mamaye shi daurewa kawai yake yi da abin na hausawa da ake cewa sahun giwa ya take na raƙumi.

Bai jira cewarta ba ya katse vioce call nan take ya kira ta video call itama kamar tana jira ta É—auka suna masu kallon juna.
Chapter 52 · 0% Book details