← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 75

Sashe 56

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allahu Akbar. Allah ya gafarta maka Baffa Ubangiji ya sa kana cikin rahamar Ubangiji."

Ammah ta faÉ—a tana jin hawaye na cika kwarmin idanuwanta Banafsha na cikin jikinta ta rufeta ruf ta sake rumgumeta. Da a ce yau Baffa na raye ya zai ji in har ya ga jinin Ummu Salama da LamiÉ—o ga shi yau LamuÉ—o ya zama Sarki ga shi Baffa ba ya raye shi daman ya daÉ—e yana faÉ—in yana ji a jikinsa watarana LamiÉ—o zai iya Shugabantar al'ummar Daura.

Kowa jikinsa ya yi sanyi da tuna Baffa.
Ummu Salma sai da ta share hawaye. Ta jima tana tunanin yadda radaÉ—in rasa mahaifi yake, sai da ta rasa nata ta san irin zafi da raÉ—aÉ—in da ake ji, ta kasa mantawa da Baffa rana ba za ta fito har ta faÉ—i ba ta tuna da shi ba, Allah ya gafarta masa amma mikin nan na rashin Baffa mai girma ne a zukatansu ba zai gushe ba har abada.

Suka taru suka yi ma Baffa addu'a sannan suka cigaba da hiran tafiya Daura.
Hamma Abdullahi na faÉ—in jirgin da za a ba da ma ai ba zai É—auki duka mutanen ba.

"Ai wasu dole su bi mota. ÆŠazu ma mun yi charting da Gimbiya Shahida ta ce mota za ta zo ranar alhamis ranar da za mu tafi kenan da yamma ta kwashi wasu da kaya a safiyar Jumma'a kenan za su isa Daura a daran ranar."

Ummu Salma ta faÉ—a tana cigaba da faÉ—in Mami ta tsara waÉ—anda za su rakata. Tunda Hamma Jibo daga can Abuja za su wuce Daura haka ma Hamma Kabiru ya ce ba za su biyo ta nan ba shima ranar alhamis za su isa Hamma Mustapha ne kawai za su biyo ta nan sannan su tafi tare da su Ummu Salama.

"Mami ta ce ni da Ammah da Ummin ikki da Ummu Balki da su Umma A'i, da su Baffa Umaru sai BaÉ—É—o da ku gabaÉ—aya ni ban ma san waÉ—anda za su bi motar ba"

"To ku matan ku bi jirgin ku, mu kuma mazan sai mu tsaya mu tafi a mota za a tafi da wasu kaya ne?

Hamma Abdullahi ya tambaya yana kallon Ummu Salama.

"E akwai kayana a can gida da wasu anan da zan tafi da su gaskiya."

"To ba matsala sai mu yi hakan ko?

Ya faÉ—a yana kallon Hamma Abdulrrahan da ya jinjina kai ya ce hakan ya yi.
Saddam ya tura baki ya ce jirgi zai bi, ba zai iya tafiyan mota ba.

Hamma Abdulrahim ya ce suma ai ba wai kuÉ—in jirgin ne ya gagaresu ba, gwara su yi tafiyar mota ko za su ga gari. Ammah ta amsa da cewa tafiya kuma mabuÉ—in ilimi ba.
Saddam tunda ya ce ba ya son tafiyar mota aka ce sai su tafi tare da su Ummu Salama amma har su Baffa Umaru Hamma Abdullahi ya ce tafiyar mota za su yi gabaÉ—aya su mazan a daran Jumma'a za su isa a yi taron naÉ—i ranar asabar, lahadi litini su dawo gida ba shikenan ba.

"Shike nan, kuwa amma ni ina gida ba zan je ba"

GabaÉ—ayansu suka kalli Ammah, sun É—auka ta daina maganar cewa ba za ta je ba

"Ammah za ki je mana, Hamma LamiÉ—o ba zai ji daÉ—i in ba ki je ba."

In ji Hamma Abdullahi, Hamma Saddam na ta faÉ—in Ammah sai fa kin je tana faÉ—in to ubana.

"Ammah Hamma ya ce da ke za a zo fa."

Ummu Salma ta faÉ—a tana kallon ta.

"To in ma ba ta je ba gida fa ba kowa."

In ji BaÉ—É—o.

"Za ta je ma in sha Allahu."

Hamma Abdulrraham ya faÉ—a yana danna wayarsa.
Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 👏 2
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Me zan je na yi? Fatan alheri ne, na yi ma LamiÉ—o a waya duk waÉ—anda ya kamata za su tafi ni ba sai na je ba."

Ammah ta gama ta faÉ—a tana jadaddawa amma ba ta rantse ba.

"Kowa fa zuwan shi na dabam, Ammah ke ce uwar Sarki ce kin ga ko zuwa Daura Dole "

In ji Hamma Saddam yana dariya.

"Mami fa a matsayin uwar Auta za ta je gwara ki je, ke ma ki yi capacity a matsayinki na wacce Sarki ya fi darajawa a duniya "

"Gaskiya Ammah sai kin je, haba ya ma za a yi ba ki je ba ai sai Hamma ya ce duk mu ba mu da amfani in har bai gan ki ba."

Hamma Saddam ya faɗa yana girgiza kai, har yana haɗa hannayensa yana riƙon Ammah ta je kar ta ce ba za ta je ba.

"Kai ba zan je ba, kar ka dame ni."

Ammah ta gwale shi, Baɗɗo ta saka baki Ammah ta ce ba za ta je ba ta ñaɗa Ummin ikki ga su Umma Balki ba sai ta je ba.

Kowa ya yi shuru ganin ta dake, Ummu Salma ta ce a zuciyanta Allah ya jiƙan Baffa da yana raye shi zai tankwasa Ammah sai ta je amma tunda ba shi Lamiɗo na raye shi ne kawai in ya yi magana da ita za ta amince.

"Ammah Hamma ya ce tare dake zamu taho "

"Shima zan faÉ—a masa dalilina."

Ammah ta faɗa alamun da gaske take yi, sai kowa ya yi shuru domin anan dai ba wanda zai tursasata ta amince, Ummu Salma ta kira wayar Lamiɗo ta shiga amma bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙon text massages da cewa Ammah ta tubure ta ce ba za ta zo ba, ya kira waya ya yi magana da ita.

Daga baya ma sai aka bar maganar. Falon ya zama kowa da abokin hiran shi, ita Ummu Salma da BaÉ—É—o suke hira tana nuna mata irin É—inkin da Mami ta turo mata ta ce a I.g ta gani ko a yi mata a leshinta ne BaÉ—É—o ta ce É—inkin ya fita gaskiya a yi mata irin shi, itama ta ce shigen shi ta ba da a yi mata a wani É—aya daga cikin leshinta na lefe suna ta kuskus É—in su Hamma Saddam da Hamma Abdulrahima ma sun haÉ—a kai suna kallon wani abu a wayar Saddam É—inm

Hamma Abdullahi ne da Hamma Abdulrrahaman suma suke hiran su, Ammah ta yi shuru kawai tana tunanin Allah ya taimaketa ma ba ta da hawan jini amma da a halin da ta shiga na damuwar rashin Baffa da tana da shi da yanzu ta faÉ—i, Allah kuma ya taimaka daman ita É—in Jaruma ce.

Sun daÉ—e suna hira sai goma da rabi suka watse a bangaren Ammah.
Su Hamma Abdullahi suka yi sallama suka tafi gidajen su Baɗɗo ta wuce bangarenta ita da mijinta haka ma Hamma Saddam Ummu Salma ta karɓi Banafsha ta shiga ciki itama Ammah ciki ta shiga ta yi shirin kwanciya.

Sai da asuba Ummu Salma ta ga saƙon Hamma Lamiɗo.

"Ammah za ta je Daura in sha Allahu."

Kuma ta duba ba ta ga kiran shi ba, ita kaɗai ta yi ta tura baki tana kunƙuni ta yi kewarsa, kewarsa na murƙukusan mata zuciya da gangan jiki haƙuri kawai take yi sama da kwana ashirin ba ta gan shi ba Banafsha ba ta ji ɗumin babanta ba tunda ta zo duniya.

Da gari ya waye ranar laraba kenan bayan ta yi wanka Ammah ta yi ma Banafsha wanka suka shirya. Breakfast BaÉ—É—o ta ba su ita ke girki tana ba ma Ammah yanzu Harira ce ke taya ta aikace aikace gida kamar shara ko wanke wanke.

Tare da BaÉ—É—on suka fita zuwa wajen Saloon Ummu Salma ta yi driving É—in su a motar LamiÉ—o.
Zuwa wani ƙaton shagon saloon suka je mai kyau booking Ummu Salma ta yi musu har da gyaran kafa za a yi musu Harira dai wanke mata gashin ta aka yi ta ce kitso za ta yi, ita ce ke renon Banafsha.

Suna can shagon har bayan azahar an gama musu gabaÉ—aya suna ma shirin tahowa ne ma sai ga wayar LamiÉ—o.
Ta yi mamakin kiran shi da rana tsaka haka.
Yanzu ba H. lamiÉ—o ba ne tuni ta goge ta mayar da shi Hamma na.

Yanzu ma jikinta na rawa ta É—aga kiran na shi cikin zumuÉ—i.

"Hamma na."

"Ranki ya daÉ—e."

Ya faÉ—a cikin kasaitar shi wanda da yanzu kamar ma ya fi na da.

Sai ta ji kunya, ita fa mantawa take yi da yanzu Hamma Sarki ne sai ta dinga ganin kamar komai bai sauyawa ba.

"Ayi mini afuwa ranka ya daÉ—e"

Ta faÉ—a tana mirmishi gefe ta koma tunda BaÉ—É—o ta ga tana dariya a fili ta furta mai Daura ne.

"Kina ina?
Received at 15:21Reactions: ❤ 14, 🥰 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Abin da ya faÉ—a kenan ta amsa masa da cewa suna shagon Saloon ita da BaÉ—É—o sai ya tambaya za su koma gida wuri ne? ta ce sun gama ma, ga su nan a hanya daga haka ya kashe wayar ta É—auka ma za su yi magana ne jin ba ta gida shi ya sa ya kashe.

Nan ta ce su tashi su tafi ATM ta ba da aka cire kuÉ—in masu yawa tunda speacial booking suka yi sannan mai tsada ne Saloon É—in da aka yi musu.
Sun taho ma suna hanya Ammah ta kira wayar BaÉ—É—o tana ta faÉ—an sun je sun zauna ta kira wayar Ummu Salma ba ta samu ba ahalin ta san ana jiran ta.

Da BaÉ—É—o ta faÉ—a mata abin da Ammah ta ce sai da ta yi mamaki.

"Ana jirana? Waye ke jirana?

Ta tambaya cikin mamaki, lokaci ɗaya tana mayar da hankalinta wajen tuƙi.

"Ban sani ba haka dai ta ce."

"Ko baƙi kika yi?

"To ƙila masu zuwa barka ne mu ƙarisa gidan"

Suna zuwa gidan a waje Ummu Salma ta yi parking É—in motar in wani cikin su Hamma Saddam sun dawo sai su shigo da ita.
Suna shiga haraba suka ga wasu manyan jifa jifai baƙaƙen motoci guda biyu, ga dogari guda ɗaya da ɗan sanda sai wani mai suit.
Chapter 56 · 0% Book details