← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 75

Sashe 32

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita haraba ya ga motar Ummu Salma lullube a cikin tamfol, ɗan kaɗa kai kawai ya yi ya wuce tunani ma ya manta bai nemi Sultan ba shi kaɗai ya tafi masallacin yana dawowa ya iske Bilkisu ta tafi sai su Sultan ya tambaya sun yi salla suka ce aa nan ya tara su zuwa ɗakinsu, suka yi alwala suka yi salla a gaban shi sannan ya ce kowa ya ɗauko littafan makarantan shi wanda ya fi ƙokari za a yi masa kyauta.
Suna rige rige, nan É—akin yaran ya zauna har La'asar yana tare da su yana biye ma surutunsu.

*
JIMETA.

Yau ta kama lahadi ne, weekend kusan duka ma'aikata suna gida.
Tun safe Umma Salma ke doka ma Hamma Saddam waya ba ya É—auka ta kira Hamma Abdulrahim shima bai É—aga wayarta ba.

Kasarta ta daina ƙamshi tun jiya ta yi ma Hamma Saddam magana a chart ya ce yau da safe zai ɗibo ya kawo mata amma kuma ta ji shuru, ƙarfe goma na safe har ta gota kuma in ba ta shaki kamshin wannan kasar ba yau ba zaman lafiya.

Har ƙasan waje Harira ta fito ta ɗibo mata ta jiƙa ta shinshina amma ba ta ji irin ƙamshin da na anguwan su Ammah ke yi ba ta ce ba ta so amai ma ƙamshin ƙasan ya saka ta.
Ta kasa cin komai tunda garin Allah ya waye. Sai ta shaƙi ƙamshin wannan ƙasan sannan za ta samu sukuni da zaman lafiya.

Daman ba ta aiki Harira ke yin komai a gidan.
Sai ɗan abin da ba za a rasa ba kamar gyara ɗakinta girki ma ba ta yi saboda ba ta son shaƙan ko wani ƙamshi in abinci ya tafasa ta shaƙi kamshi yini za ta yi amai sannan ba ta son wari maggi ɗunkule in abinci ne za ta iya ci amma ba ta son ƙamshin shi, shi ya sa in dai Harira za ta yi girki sai ta kulle kitchen ɗin yadda ƙamshin abincin ba zai fito ba. Kamshin ƙasan nan ta anguwan su Ammah kaɗai take so.

Tana zaune falo ne, daga ita sai riga doguwar riga bubu ce mai sakewa, ba ta da nauyi cikin rigunan da Baɗɗo ta saro ne ta siya wajen kala huɗu ta siya ma Harira ma su take sawa tana jin daɗin su domin yanzu ba ta son saka kaya saboda zafi. Wannan cikin iska yake so da A.C ma take kwana ta yi ma likita ƙorafi zuwanta na ƙarshe ya ce saboda da cikin ne sannan da BP. masu hawan jini ba sa shiri da zafi.

Harira ta gama gyaran falon tana kitchen tana wanke-wanke. Ita fa ko warin moneyfresh ba ta so, sabulun wanka ma da na wanki take amfani da shi mara ƙamshi, duk ta tattara showe gel ɗinta da sabulanta ta ajiyesu gefe.
Lotion na shafawa ma a jiki yanzu ta daina shafawa, saboda ƙamshi.
Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 🔥 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ko wani mai yana da ƙamshi har mankaɗe Ammah ta aiko mata ta dinga shafawa sau daya ta shafa ba ta kara ba wari warin ya dinga tashin zuciyarta.
Yanzu haka nan take wanka ba ta shafa mai ya fiye mata zaman lafiya.

Gajiya ta yi da zaman sai ta sauko ta zauna a saman cafet sannan ta miƙe kafafunta
Tv na kunne a tashar arewa24 hankalinta ba shi a wajen yana wajen wayarta da ke hannunta tana cigaba da kiran su Saddam amma ba su É—auka ba.

"Suna can suna ta barci"

Ta faÉ—a a sarari kafin ta É—an ja tsaki.
Ita fa in ba ta shaƙi wannan ƙamshin ba akwai matsala.

TV Ta ƙura ma idanuwana suna haska wani hausa film wai tarko. Ita yanzu ta rage ma wannan kalle kallen, tun rasuwar Baffa kamar an sauyata.

Bayan dawowarsu gidan sun daÉ—e ba sa kunna kallo.
Gabaɗaya komai ya fita kanta na waɗanda take ɗan bi a ma Tiktok ko Youtube duk ta daina bin su, girke-girken ma ta watsar da komai yanzu ta kanta take yi. Rasuwar Baffa ta sanyata cikin ƙunci sannan ga rashin jaririnta ga abin da ya faru tsakaninta da Hamma daga karshe ga cikin da ta samu duk sai rayuwarta ta zama kamar an juya ta daga sama zuwa ƙasa. Gwara ma littafan hausa da Baɗɗo ta matsa mata ta fara ji a youtube a tashar tsakar gida, na Mai sanyi ta fara sauraran wani littafi Ɗingishi kwaɗo na marubuciya Surayya Dee mai bojuwa, ta fahimci dai Baɗɗo na yin matan nan tunda har littafanta take matsa mata ta saurara.

Kuma ba laifi da ta fara sauraran ya fara mata daÉ—i, tunda karatun yanzu wahala zai zame mata. Ko Ep13 ba ta kai ba ta watsar sai tana cikin ji sai kawai tunani su yi mata yawa sai can in ta dawo ta ga karatu ya yi nisa baya ba ta fahimci komai ba. Tunda kuma ta watsar ba ta sake bi ta kan shi ba sam ba ta da natsuwa.

Kanta da ba ɗankwali ta sosa kalaba ne ya fi sati uku Baɗɗo ce ta zo ta yi mata shi. Ya tsufa shi ya sa yake ta ƙaiƙayi.
Da ta ga sun ƙi ɗaga wayarta sai kawai ta kira wayar Ammah ba ta jima tana ringing ba ta ɗaga wayar suka gaisa.

"Ammah ina tazuran samarin ki?

"Suna bangarensu suna barcin tunda suka shigo nan bayan sun dawo masallaci ban ƙara ganin su ba, ga abin karyawansu ma can a kitchen ba su ga dama sun tashi ba."

"Ammah ina ta kiran su ne ba su É—auka ba."

Ta faÉ—a kamar za ta yi kuka.

"Na ce miki suna can suna barci ba yau lahadi ba."

"To Ammah ya zan yi?

"Na me kenan?

Ammah ta amsa mata.

"Kasar ne ta daina ƙamshin Hamma Saddam ya ce yau zai ɗibo mini da safe har yanzu shuru."

"Ai fa shurun ne, to ki yi haƙuri in sun ta shi sai ya kawo miki."

"Ammah ina son in shaƙi kamshin ne, ba ki ji zuciya ta ba."

A shagwaɓe take magana

"Harira to ta É—ibo miki nan kofar gida mana "

"Ta ɗibo ba irin na ku ba, ba ta ƙamshi kamar na kofar gidan mu."

"To"

Ammah ta faÉ—a a fili a zuciyarta tana faÉ—in wannan cikin akwai tsirfa. A kullum addu'arta Allah ya sauki Auta lafiya.

"Ammah in ban shaƙa ba ji nake yi kamar sheɗata za ta ɗauke kuma ba zan iya cin abinci ba."

"To ai sai dai ki yi haƙuri su tashi barcin."

Kamar za ta yi kuka tana tambayan Ammah ba wanda zai kawo mata.

"Babu sai ni ko Ummarki A'i."

Baƙa Ammah ta mayar mata ya sa ta fara dariya.

"Ki fara gwada cin ko goro ne. Saboda tashin zuciya."

"To Ammah ki ba ma Hamma Saddam ya kawo mini."

"Ba ni da shi, zan ce ya biya kasuwa ya siyo miki mai yawa ki gwada ki gani."

Ta amsa da yauwa, Umma A'i ce ta karɓi wayar tana mata faɗan ta rage shan kankarar nan da ta ga tana sha, cewa kawai ta yi to domin in za ta kwana tana bayani ba za ta gane ba wannan cikin na dabam ne wahala kawai yake ba ta.

Bayan sun gama wayar har shaƙuwa ma ta fara yi tana jin zuciyarta wani iri kofofin hancinta na buɗewa ƙamshin da take son shaka ba ta samu ba.

Ta ga dai su Hamma Saddam jiran su ma ɓata lokaci ne watakila ma sai yamma.
Sai kawai ta jwala ma Harira kira sai ga shi ta fito tana goge ruwan hannunta a zanin jikinta

"Gani ranki ya daÉ—e kina bukatar wani abu ne?

Ta faɗa tana duƙawa a gefen in da take zaune

"Harira ni fa na ce ki daina ce mini wani ranki ya daÉ—e, ki ce mini Anty kawai."

Ta gama faɗa tana hararan Hariran da ta sadda kai ƙasa tana ɗan mirmishu.
Received at 07:54Reactions: ❤ 9, 👍 1, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"Aa ranki ya daÉ—e ai girman ki ne, na saba ne ba zan cewa Antyn ba ne.'

"Ke kika sani dai."

Ummu Salma ta faÉ—a tana É—an muskutawa

"Gida za ki zo ki je, ba ma sai kin shiga ba ki yi tashar adaidaita ya tsaya ki samu ƙatuwar leda ki ɗibo mini kasa yadda zan daɗe ina amfani da ita."

"To ranki ya daÉ—e."

"Kin gama wanke-wanken?

"Saura kaÉ—an."

"To karisa sai ki zo ki tafi Harira wallahi wani iri nake ji kin san in ba kasar nan yau ba zaman lafiya Hamma Saddam kuma da na dogara da shi ina ta kiran wayarsa ba ya É—agawa."

Harira ta miƙe tana faɗin bari ta ƙarisa da hanzari.
Ba daÉ—ewa kuma ta gama ta dawo, tana zuwa Ummu Salma ta toshe hanci.

"Harira kina ƙamshin sabulun nan na wanke wanke."

Harira ta shinshina hannunta kuma ƙamshin take yi, shi daman yana da ƙamshi sosai.
Sai ta yi baya tana faÉ—in

"Kuma na wanke hannu."

"Shiga É—akina a drower gefen gado ta hannun dama za ki ga kuÉ—i a farar takarda ki É—auko dubu biyu"
Ta gama faɗa tana sake toshe hancinta zuciyarta har ta fara tashi da sauri Harira ta amsa ta shiga ɗakin Umma Salma ta ɗauko sakon Harira Amintaciya ce a wajenta ta sha gwadata akan kuɗi ba ta taɓa kama ta da laifin sata ba, tana son Harira domin duk abin da take so kafin ma ta yi magana ta aiwatar.
Shi yasa itama take kyautata mata, tuni ta saka Hamma Saddam ya buÉ—e ma Harira Opay a wayarta tana tura mata kuÉ—i ta tura can wajen danginta sannan tana saka mata kati wanda za ta siya data Harira ta yi karatu kawai ba ta gama sakandiri ba ne ta faÉ—a aikin bauta. Amma tana da burin nan gaba ta ba ma Harira jari da za ta tsayu da kafafunta wata rana in har ta samu miji ita da Hamma LamiÉ—o za su aurar da ita.
Chapter 32 · 0% Book details