Sashe 51
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ya kira LamiÉ—o ya taho Daura ya riga ya gama shirya komai. Ya san zai ce ba ya so shi ya sa ya ce umarni ne ba neman yarda ba, bai ma tsaya masa wani jawabi ba sai dai kawai ganin shi ya yi ya gayyato Kingmakers.
Majalisar zaɓe tunda ya ga haka ya san an zo bus stop, sannan ya saurari duk abin da suka tattauna suma ɗin dai wasu sun amince da tsarin Mai martaba wasu kuma ba su amince ba amma dai ya tattauna da su sannan ya kawo musu hujjojinsa masu ƙarfi ya kuma ce su je su zauna su sake nazarin komai a tsanake amma kar ya ɗau lokaci, Lamiɗo kuma ba a ba shi wata dama ba a wannan gabar jiran umarni ne kawai na shi ko ya yi magana a wannan gabar lokaci ya ƙure masa.
Received at 15:16
11 people reacted with â¤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ba duka ne waɗanda ke da alhakin zaɓen Sarki suka amince da tsarin tsohon Sarki ba amma tunda majority sun amince sun ga kuma cancantar Lamiɗo.
Majalisar zaɓe da Mai martaba ya fara ganawa da su, a hukumance su ke da alhakin zabe ko tsige Sarki. Ko kuma rashin lafiya mai tsanani. Kuma majalisar zaɓe ta ƙunshi manyan Hakimai guda hudu zuwa biyar.
Mai sarautar Madaki, Waziri,Galadima da Chiroma ko Yarima babban yaron Sarki da sallama mai kula da ƙofar fada.
Aikin su daman taruwa ne a ɓoye domin nazarin lamarin. Suna yin shawarwari kan mutumin da ya dace bisa tsarin mulki na gadon Masarautar. Su ne kuma ke gabatar da dalilai ga majalisar Sarki ya yin sauke shi ko tsige shi.
Babban Alƙali kuma shi ne shugaban sharia' yawaancin shawararsa kan halascin sauke sarki ko zaɓen shi a addini ne bisa shari'ar musulunci.
Sai limamin Juma'a; wannan mutumin yana da mutumci a idanuwan talakawan gari, shawararsa kan zaɓen shugaba mai adalci yana da tasiri ga al'ummar garin gabaɗaya.
Sai sauran Hakimai da Dattawan suma wajibi ne a ji ta bakin su domin samun amincin talakawa.
Sannan akwai alhakin amincewar Gwamnati shi ya sa Mai martaba bayan duk ya gama samun amincewar Fada da sauran masu ruwa da tsaki a safiyar da murabus ɗinsa zai fito ya ɗauki Lamiɗo suka je har gidan Gwamnati suka gana da Gwamnan Jahar Katsina tattaunawa mai tsawo bai baro gidan Gwamnatin Katsina a daran ba sai da ya samu sahalewarsa sannan Gwamna da kan shi ya ce zai yi waya ya sanar da shugaban ƙasa.
Shi ya sa a daran ba tare da sanin kowa ba wakilan fada da hakimai tare da dattawan fada da majalisar Sarki haÉ—e da limamin fada a gaban su a ka yi komai Mai martaba tsohon Sarki ya yi murabus nan take aka maye gurbin shi da Muhammad LamiÉ—o shi ya sa a wayewar gari labarin ya fita bayan tsohon sarki ya sanar ma media team É—in shi ya ba su izinin fitar da murabus É—in ga duniya.
Matan Mai martaba mai murabus ji suka yi kamar a mafarki. Kuma ba wacce ta ji daɗi, ba wacce za ta so tana matsayin matar Sarki ta tashi daga wannan muƙamin na ta. Ko da suke ganin Mai martaba ya fi son babban ɗan shi ya gaje shi ba su taɓa tunanin da ranshi haka zai faru ba sai ga shi ya faru kuma abin ya tabbata.
Gimbiya Shahida da ake ganin za ta nuna rashin jin daÉ—in ta ma ba ta nuna ba, tunda an fi ganin cancantar Saleem a kan karagar Mai martaba, ba ta nuna damuwa ko a fuska ba, koma akwai ba ta bayyana ba shi kan shi Saleem É—in bai nuna bore ba, shi kan shi ya faÉ—a LamiÉ—o ya fi shi cancanta.
Gimbiya Hadiza ce ita da take da yara mata amma ba ta ji daɗi ba, tana matsayin Gimbiya matar Sarki darajanta zai yi ƙasa amma ta yi murna saboda zamowar Bilkisu cikakkiyar Gimbiya a Masarautar Daura.
A bangaren Gimbiya Maimunatu ta fi jin zafi ganin ga yaranta Yazeed da Sagir, da arziƙi a garin wasu ai gwara a garin ku a garin ma na ku ma a gidan ku a gidan na ku ma ya kasance kai ne ke da alhakin komai. Maganganu dai na ta tashi kowa na faɗin albarkacin bakin shi amma babu abin da zai dawo baya bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Ƴa'ƴan Mai martaba ƙannen Lamiɗo suma duk haka suka ji batun wasu ma a kafafen sada zumunta suka fara sanin abin da ke faruwa wasu suna cewa an yi daidai wasu suna ganin Sarki ya yi son kai ko ya yi gaggawa.
Amma duk da haka sun fito group suna ta fatan alheri irin su Sakeena sun neme wayar Lamiɗo ba su samu ba amma sun tura masa saƙonnin ta ya murna.
Tunda tun ranar da tsohon Sarki ya yi murabus Sarki na yanzu Muhammad Lamiɗo ya fara gudanar da sha'anin mulki. Sarki ya haɗa shi da amintattun shi na fada irin su Waziri, Shamaki da madaki ya ce su zama idanuwan Lamiɗo tare da bashi shawarwari a mulkinsa tsohon Sarki ya yi ma Lamiɗo umarnin shima ya riƙe su domin za su taimaka masa, suma kuma ya ce su ji kamar shi ne domin inganta Masarautar Daura. Amma zai iya sauya wasu miƙaman na hakimai a matsayin shi na sabon Sarki yana da damar da zai yi sabon naɗe naɗe a tsarin mulkin shi.
Received at 15:16
14 people reacted with â¤

Sannan tuni tsohon Sarki ya ba da umarnin a fara gyaran gidan shi dake cikin garin Daura shima babban gida ne nan za su koma shi da iyalansa da mahaifiyarsa Fulanin Daura.
Gidan Sarki na yanzu kuma shima za a yi masa gyara ciki da waje domin sabon Sarki ne yanzu da iyalansa za su zauna a cikin gidan komai da ya danganci Sarauta hadimai, dogarai masu kaki duka yanzu suna ƙarƙashin mulkin sabon Sarki Muhammad Lamiɗo ne a yanzu a Daura gabaɗaya maganarsa tana sama da ta kowa har ta Tsohon sarkin gabaɗaya.
LamiÉ—o gani yake yi abin kamar wasa wai shi ne zaune a fada a kan kujeran Sarki yana hakimce da rawani da Alkeybba ga hakimai suna zagaye da shi, kamar a mafarki haka yake ganin faruwar komai kamar irin ya kwanta barci ya tashi ya ga ba haka ba ne.
Sai dai ba mafarki ba ne duk abin da ke faruwa gaskiya ne.
A daran ranar kwana na biyar da zamowarsa Sarki sun yi ganawa mai tsawo da Mai martaba a bangaren shi. Bangaren da nan da lokaci kaÉ—an zai zama mallakin LamiÉ—o a matsayin sa na sabon Sarki.
Ya yi masa batutuwa masu ratsa jiki da zuciya da suka saka Lamiɗo miƙa wuya. Ya kuma karɓi kaddaransa da hannayensa biyu. Mai martaba tsohon Sarki ya miƙa duka yardansa da yaƙininsa a kan Lamiɗo kuma yana fata ba zai ba shi kunya ba. Ya nuna masa muhimnancin miƙa wuya ga sabuwar rayuwarsa da kuma tunasar da shi irin nauyin da yahau kan shi na al'ummar mutanen Daura da ma arewancin nigeria gabaɗaya
Daga karshe Mai martaba mai murabus ya yi masa fatan alheri da fatan Ubangiji ya taya shi riƙo. Sannan daga ƙarshe ya ce yana tare da shi domin neman shawara ko wani abu da ya shige masa duhu na sha'anun mulki yana nan a gefen shi. Sannan sun yi magana kan haihuwan Ummu Salma, ya ce Gimbiya ta sanar da shi an samu ƙaruwa.
Ya tambayi Lamiɗo wani tsari gare shi, yanzu dai ba shi da ikon barin Fada sai komai ya natsa tukunnah. Amma zai iya tura wakili can ƙasar da Ummu Salma ta haihu tunda shi ba zai samu zuwa ba.
Nan Lamiɗo ya faɗa masa tsarin shi, ya tura Kabiru shi zai isa can ƙasar Egypt domin ya yi ma jaririyar huɗuba anan gida kuma zai kira Abdullahi za a siya raguna a can Adamawa a yanka.
"Hakan ya yi sosai Allah ya raya ya yi mata albarka wani suna za ku sanya mata?
Mai martaba mai murabus ya tambaya.
Cikin ƙanƙantar da kai, Lamiɗo ya ce" Ba mu riga mun yanke shawaran sunan ba Ranka ya daɗe."
"A'a yanzu ai kai ne ranka ya daÉ—e."
Mai martaba ya faÉ—a yana É—an mirmishi.
Yana zaune a ƙasan cafet Lamiɗo na gefen shi.
"Allah ya yi albarka. madallah sai ka yi magana da duka matanka ku tsara lokacin da za su baro can su dawo nan. Yanzu ne nan ne muhallinsu har zuwa lokacin da Ubangiji ya iyakance."
Sannan ya cigaba da faÉ—in daga baya za a yi taron naÉ—i da za a yi masa za a yi gayya tare da gangami taron taya shi murnan zamowarsa Sarkin Daura. Ya daÉ—e a bangaren Mai martaba har wajen sha É—ayan dare sannan ya koma bangaren shi barcin ma yanzu rabi da rabi ne yana jin sa kamar ba shi ba.
Kamfaninsu sun turo masa amsar saƙon shi na ajiye aiki sun nuna rashin jin daɗin barin shi aiki tare da su, suna kuma cewa matujar yana neman ƙarin albashi ne ya zo su tattauna za su iya ƙara masa amma suna jin daɗin aiki da shi.
Duk yadda yake son aikin shi amma ya rasa shi ba shi da wani zaɓi ne.
Rayuwarsa kamar ƙifawan ido komai na shi ya sauya a kwanaki shidda baya shi Captain ne na jirgin ruwa amma a yau kuma shi Sarki ne, sarkin Daura mai ƙaraga.