← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 75

Sashe 37

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaran suka É—ebe mata kewa. Da yake duk an haÉ—a musu tasoshin ta kunna musu Tv a tashar Mbc3 ana cartoon.
Suna ta bidirinsu a falo, ita kuma sai ta shiga ciki ta dauki wayarta ta kira Mami suka gaisa take faÉ—a mata Hamman ya taho har yau sun dawo Lagos.
Bayan ita ta kira BaÉ—É—o sun yi magana da yake ba ta faÉ—a mata za ta zo Lagos ba.
Tana É—akin ma suka biyo ta ciki dole ta tarkata su zuwa falo nan suka sha zamansu itama tana biye musu.

Har mangariba sannan ta ce a tashi a yi salla.
Sai ga Hamma LamiÉ—o ma ya shigo ya ce Sultan ya zo su tafi massllaci. Su Hanan kuma tare suka yi na su salla a falo. Bayan sun idar ta ce su karanta azkar suka fara rerawa tana É—an yi musu gyara kaÉ—an. Har bayan isha'i suna bangaren Ummu Salma Bilkisu ta dawo tun bayan la'asar Sabuwa ta faÉ—a mata Yarima ya dawo amma ba ta faÉ—a mata dawowar Ummu Salma ba ganin ba huruminta ba ne.
Received at 17:29Reactions: ❤ 10, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Wanka kawai ta yi a bangarenta ta je bangaren LamiÉ—o shima kuma bai faÉ—a mata ba, ita kuma ta sakankance da cewa ya saki Ummu Salma tafiyar da ya yi wannan karon shi yasa ba ta damu ba. Yara kuma da ta ga ba ta ji motsin su ba, ta dauka suna bangarensu ne ba ta neme su ba.

Sai da za su yi dinner ta ga Sultan a falo babu Hanan ba Beena ba ta yi magana ba ta É—auka suna ciki ne. LamiÉ—o ya yi wanka sannan ya fito sanye da dogon wando da riga mai gajeren hannu.
Ya zauna a saman dinning Debora ta jera abincin cikin birgewa.

"Sultan ina Beena?

Bilkisu ta tambaya tana serving É—in LamiÉ—o.

"Suna wajen Anty Umma."

KaÉ—an ya rage cokalin hannunta bai faÉ—i kasa ba tsabar yadda ta razana.

Ta zaro ma Sultan idanuwana amma ta kasa magana.

"Go and call them"

LamiÉ—o ya faÉ—a yana kallon Sultan yaron ya mike har zai tafi sai ya dawo.

"Papa Anty Umma? har da ita?

"No."

Ya tuna ba ta son ƙamshin komai.

"Ba ta son ƙamshi."
Ya samu kanshi da ba ma Sultan amsa.
Sultan yaro ne bai fahimta ba sai ya yi wucewarsa kawai.

Bilkisu ta kasa iya motsa hannunta tsabar firgici.
Wata Anty Umma? ba dai Ummu Salma ba.
Kafafunta suka fara rawa, da hannunta ta kasa cigaba da abinda take yi.

Ba ya saketa ba? Me ya dawo da ita?

"Akwai matsala ne?

Ya faÉ—a yana kallonta ganin ta tsaye ta kasa cigaba da abin da take yi.
Lokacin ne ta farga ta yi saurin zuba masa ta tura masa filet É—in faten dankalin turawan gabansa.

Ta koma ta zauna tana jin zufa duk da sanyin A.C dake wajen.

"Is she back?

Ta faɗa tana kallon shi, idanuwanta har sun tara ƙwalla zuciyarta na wani irin rawa.

Ya kalleta amma bai yi magana ba.
Sai da ya fara cin abinci har ta cire rai da zai yi magana.

"She is."

KaÉ—an ya rage zuciyarta ba ta buga a lokacin ba. Ta yi masa zuru da idanuwana kawai tana kallon shi.

"Bilkisu."

Ya kira sunanta.

"Ummu Salama."

Sai ta ga ya yi mirmishi har gefe da gefen bakin shi ya motsa.

"She is pregnant."

Kirjinta ya buga dam!.

"Ciki?

"Ba ka sake ta ba?

Maganar ta fito ne daga zuciyarta ba tare da ta sani ba.

Sai da ya tsaya da cin abinci yana kallonta.
Sai ta yi saurin cewa.

"A'a na É—auka kun rabu ne."

"Na ga ita ta ce ka sake ta."

Ta faɗa ne domin ta kare kanta. Ba ta san ta sake kwaɓa komai ba ne

LamiÉ—o ya kalli Bilkisu kafin ya kauda kai ya cigaba da cin abincinsa tana so ta yi magana ta kasa bakinta ya yi nauyi ga zuciyarta na rawa, tana tunanin Ummu Salma ta bar mata mijinta ashe zaune ba ta kare ba ciki ma gare ta.

Dowawar su Sultan ya dakatar da ita daga kan maganar da ta yi niyar yi, kanta ta dafe ta bata komai kishi ya sa ta furta abinda ke cikin zuciyarta.

Sultan ne ke ba da labarin yadda su Beena suka ce za su ci abincin Anty Umma da yadda suka zubar da na bakin su. LamiÉ—o har yana murmusawa wa zai iya cin wannan abincin na Umma Salma ai sai ita. Bilkisu na zaune kamar ba ta wajen ta kasa cin abinci tana ta wasa da cokalin hannunta LamiÉ—o kuma kallo É—aya bai sake yi ma Bilkisu ba.

Abinci ma bai ci da yawa ba ya tashi. Ya bar Bilkisu anan ya wuce bangaren Ummu Salma.
Har ta yi shirin kwanciya Harira kuma tana bangaren su Sabuwa.

Gefen gado ya zauna ya janyota kan cinyarsa ta zauna yana shafa cikinta.

"Kin ci abincin ki?

"Uhm"

Ta faɗa tana toshe hanci domin ya yi wanka da sabulu mai kamshi kayan jikinsa ma suna ta ƙamshi.

Fuska ya kwaɓe kamar zai yi kuka.

"Wari nake yi?

"Ni yanzu ba a son ƙamshi na."

Yadda ya yi da fuska ne yasa ta fara masa dariya shi kuma yana É—an mirmishi.

Sakinta ya yi tunda ta ce kar ya saka ta amai.

"Hamma to yaushe za a aiko mini da saƙon?

Ya kalleta domin shi ya ma manta da wayaun da ya yi mata.

"Kasar da ka ce kar na É—auko."

"Oh na tuna."

Ya faÉ—a yana dafe kansa.

"Kasar nan fa babu sai dai a samo miki anan"

Ummu Salma ta fara kallon shi kamar za ta yi kuka.

"James zai samo miki mai ƙamshi."

Ya faÉ—a yana jan karan hancinta.
Sannan ya sumbaci goshinta.
Cewa ya yi ta kwanta ba gaddama ta koma ta kwanta ya rufa mata bargo.
Ya rike tafin hannunta yana mata wani irin kallo.

"Good night Sweetheart."

"Good night Darling."

Ya yi dariya mai sauti.

"Ni Hamma Darling"
Received at 17:29Reactions: ❤ 19, 🥰 1
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ya gama faÉ—a yana dariya.

"Ni ƙanwa ni Sweetheart."

A tare suka yi dariya sannan ya saki hannunta.
Ya yi mata bye itama ta yi masa hasken wutar ya kashe mata ya kunna mata A.C tunda yanzu tana son sanyi sosai.

Yana fita falo ya haÉ—u da Harira ta shigo ta duka ta gaishe ya amsa.
Ya kalleta sau É—aya ya kauda kansa.

"Me sunan ki ma?

In da amana ya kamata ya haddace sunan nan saboda yadda Ummu Salma ke jadadda masa

"Sunana Harira. Harira ranka ya daÉ—e."

Ta faɗa kanta na ƙasa cikin ladabi

"Umma Salama."

"Ki kula da ita"

"In sha Allahu ranka ya daÉ—e."

Ya wuce ya fita sannan Harira ta ƙarisa ɗakin Umma Salma ta leka ta ga har ta kwanta sai kawai ta rufe mata ƙofa ta shiga na ta ɗakin.

*
Bilkisu ta kasa zuwa bangaren LamiÉ—o ko bai yi mata magana ba. Kallon da zai yi mata kaÉ—ai zai kassara sauran É—an kuzarinta.

Ta firgice da dawowar Ummu Salma, ba ta taɓa tunanin za ta dawo ba. Ta ɗauka ta bar mata mijinta kenan har abada. Abincin ma ta kasa ci Lamiɗo na ta shi itama ta tashi ta shige bangarenta.
Yaran ma Sabuwa ta kira ta ce in sun gama a kai su É—akinsu a yi musu shirin kwanciya.

Tana cikin wannan fargaban ne sai ga kiran Lamiɗo ya ce ta zo, jikinta ya kama rawa ta riga ta yi ɓaramɓarama, ta furta abin da ke cikin zuciyarta.

Jikinta a sanyaye ta tafi bangaren shi. Ta same shi tsaye hannayensa harÉ—e a bayan shi.
Tana shigowa ya juyo yana kallon ta.

"Ranka ya daÉ—e."

Ta faÉ—a tana kakaro mirmishi.
Lokaci É—aya tana gyara zaman rigar barcin dake jikinta.

Hannayenta ta É—ora a saman kafaÉ—an shi sannan ta sumbaci bakin shi.
Bai mayar mata da martani ba sai sunanta da ya kira.

Tana jin yanayin kiran sunan jikinta ya sake saki.
Kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa
Maganganunta ya sa ya fahimci bincike ta yi masa a waya ta karanta saƙonnin Ummu Salama, ya goge ma dukasaƙo sannan ya yi abin da bai saba ba ya saka ma wayarsa password.

Bilkisu tana da wani hali da ya fahimta, son shiga rayuwar shi da Umma Salama ahalin ita Umma Salama ba ruwanta da wannan. Yana so ya ce ta bari ba ya so sai kuma kawai ya ƙyaleta. Tambayarta ba ta bukatar amsa tunda ga Umma Salma har da ciki
Cikinta ya É—uri ruwa ta É—auka zai yi mata fada ne sai ta ji shuru.

Cikin farinciki ma suka kwana. Washegari asabar yana gida bai fita ba yara kuma sun tafi makaranta. Ummu Salma ta fara rigiman ita fa a samo mata ƙasa James ya yi magana ya ce ya shiga cikin gari ya diɓo kasa kala kala ya kawo masa.

An kawo mata duk wanda ta shinshina sai ta ce ba ta ƙamshi James wajen sau uku yana fita.
Shi kan shi mamaki ya kama shi mai oga zai yi da ƙasa? Bilkisu na bangarenta ba ta san ma abin da ke faruwa ba tunda yau tana gida ba ta je aiki ba. Ba ta son ma fitowa ballatana su haɗu da Umma Salma itama Umman Salman ko fitowa ba ta yi daga bangarenta ba tun jiya.

Ƙasa dai karshen ta na wajen flowers na cikin gida aka samo mata tace tana so yana ƙamshi. Saboda da safe lokacin da James ke ba ma wajen ruwa ta ji ƙamshin ƙasar.

Harira ta samo mata wata roba mai murfi ta jiƙa mata sannan ta kara jiƙa mata da ruwa. Sai goro da ta ce tana so ya hana ta tashin zuciya shima James aka tura kasuwa ya siyo mata.

Abinci kuma Harira ta yi mata irin tuwonta da miya daga kuka sai gishiri da farin maggi ba wanda ya sani tunda a kitchen É—in bangaren Ummu Salma ta yi girki.

Sai litini da safe Ummu Salma da Bilkisu suka haÉ—u a main falo.
Lokacin da za su yi ma LamiÉ—o rakiya zai koma wajen aikinsa.
Chapter 37 · 0% Book details