← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 75

Sashe 3

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saddam ya faɗa yana fatan Ammah ta amsa da cewa zazzaɓin ne ya yi zafi Baffa ya rufa har saman kanshi amma abin da bai gane ba akwai bargo me ya sa Baffa zai rufa da zani?

Abdulrahim ko ƙura ma Baffa idanuwana ya yi Baffa ba ya motsi, kirjinsa ya doka a rikice ya kalli Ammah.

"Ammah Baf..f"

Sai ya kasa ƙarisawa, domin da gudu Saddam ya durƙusa ya yaye zanin Baffa ga shi nan kwance idanuwansa a rufe daga sama har ƙasa suka sauke ganinsu a ƙafafunsa in da Ammah ta haɗa ta ɗaure.

A tare kirjinsu ya doka, Abdulrahim shima ya yi ƙasa ya durkushe yana ganin duruduru. Ammah suka kalla da ta koma ta jingina da bango tana maimaita salati a cikin zuciyarta.

"Baffa ya tafi ya bar mu, jiya ƙarfe uku na dare Ubangiji ya karɓi Baffa."

Ammah ta sanar da su cikin wani irin murya.
Saddam ya faÉ—a jikin Baffa kamar ba namjji ba ya wage murya yana kuka yana kiran sunan Baffa

Shi ko Abdulrahim bakin shi ya danne da hannu bibbiyu kuka na son ƙwace masa da rarrafe ya fita daga ɗakin ya koma ƙofar ɗakin Baffa yana hawaye, hawaye masu ɗaci da zafi.

Jiya fa har É—aya saura na dare suna tare da Baffa suna hira ashe ciwon kan da ya ce yana ji na ajali ne.

"Innalillahi wa'inna inna ilaihirraju'un."

Haka Abdulrahim ya ke maimaita yana kuka mara sauti hawaye na zuba wasu na koran wasu
Saddam daga cikin É—akin Baffa ana jiyo kukansa.

"Baffa "

Haka yake kiran sunan shi yana kuka har da shessheƙa.
Ammah ce ta yi ƙarfin halin daka masa tsawa.

"Meye haka? Kai da za ka yi masa addu'a shi ne za ka tasa shi kana yi masa kukan wofi?

"In kuka zaka yi, ka fita waje."

Ta faÉ—a tana buÉ—e murya.
Tashi ya yi da gudu ya fito waje, ya kusa ture Abdulrahim dake zaune dirshan a ƙofar ɗakin Baffa yana kuka.
A tsakar gida shima ya baje yana kuka da duka muryansa.

Hamma Abdullahi ya fara isowa gidan.
Sun yi waya da Abdulrahim ya faÉ—a masa Ammah ta ce su zo gida shima ya ce ya ga kiranta hankalinshi tashe ya ce wani abu mara daÉ—i na faruwa duka sun ji a jikinsu.

A waje Abdullahi ya yi parking É—in motarsa
Da sauri ya shigo gidan sai dai kukan da ya ji ne ya sa ya faÉ—o gidan da gudu jallabiyan jikinsa ma a bai bai ya saka ta saboda sauri.

Ganin Saddam baje a tsakar gida yana kuka mai sauti ga Abdulrahim a ƙofar ɗakin Baffa yana hawaye tare da salati.

"Me ya faru?

Ya tambaya muryansa a buÉ—e.
Ganin sa ya sa Saddam ya sake rushewa dakuka.

"Hamma Baffa."

Ya faÉ—a shessheka na hanasa magana.

Abdullahi ya zaro idanuwana.

"Me ya faru da Baffan?

Zuciyarsa ne ta nemi tsayawa cak lokacin da Saddam cikin kuka yake faÉ—a masa Babu Baffa, Baffa ya tafi ya barsu.
Abdullahi ya yu wurgi da takalmin kafarsa ya rumtuma É—akin Baffa yana fatan ya ga ba gaskiya ba ne yana fatan ya ga Baffa zaune.
Sai dai abin da Saddam ya faÉ—a masa gaskiya ne.
Ya iske Baffa na kwance babu rai a jikinsa ga Ammah zaune a gefe tana jan carbi ko bai tambaya ba yasan yau sun wayi gari cikin wata jarabawa.

Allahu akbar, duk cikin su yafi shaƙuwa da Baffa saboda tare suke kasuwanci daga shi sai Saddam da Abdulrahim tunda kodayaushe suna gida tare da shi.

Ya durƙushe a gaban Baffa ya dafe kanshi hawaye suna shatata masa.

A jere yake sauke numfashi na kukan zucci.

"Ku daina masa kuka Baba, Baffa addu'an mu yake buƙata a yanzu."

Ammah ta faÉ—a muryanta ta karye amma ta kasa kuka.
Abdullahi ya juya yana hawaye yana kallon Ammah.

"Ammah."

Ya kirata muryansa na rawa bakinsa na rawa duk a lokaci É—aya.

"Baffa ne ya tafi ya bar mu?

Ya faɗa kuka na taso mata, ya kwantar da kanshi a kirjin Baffa yana rera kukan zucci yana sharɓe majina.

"Baffa Allah ya gafarta maka."

"Ubangiji ya sadaka da rahamarsa."

A lokacin Abdulrahaman ya shigo gidan shima ganin su Saddam a tsakar gida cikin wani yanayi, ga shi suna ta kuka kamar ba maza ba.
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Bai tsaya tambaya ba ya faɗa dakin Baffa shi ne kaɗai bai gani ba jikinsa ya ba shi wani abu ne ya faru da Baffa amma bai taɓa kawo ma Baffa mutuwa ba.

Ko bai tambaya ba, ya san amsar. Ga Abdullahi durƙushe a gaban Baffa yana kuka.
Ammah na gefe da Hijabi da casbaha ta sunkuyar da kanta.

Tabbas Baffa ya amsa kiran mahallicinsa ashe zaman hiran da suka yi jiya na bakwana ne Baffa lokaci ya yi. Shima gefen Abdullahi ya duka shima yana kallon Baffa amma shi bai yi kuka ba zuciya ce ke suya kawai.

Ya fara yi masa addu'a daga karshe ya ce" Allah ya gafarta maka Baffa"

Shi ya janyo zanin ya sake rufe shi sannan ya tashi ya zo gaban Ammah ya duka yana kallonta.

"Ammah ya haƙurin mu?

"Mun gode ma Allah Abdulrrahaman."

"Allah ya jiƙan Baffa, Ubangiji ya ba mu haƙurin rashin sa."

Ta amsa da Amin kallon ta yake yi ba ta yi kuka ba amma Allah kaÉ—ai ya san suyan dake cikin zuciyarta.

"Rasuwar dare ce?

"Ƙarfe uku na dare da wani abu ya cika."

Ya jinjina kai cikin sanyin jiki da na zuciya.

"Allahu akbar Ubangiji ya karɓi bakuncin Baffa."

Ta amsa da Amin Amin

"Ka kira sauran yan'uwanka, sannan ku sanar da Baffa Umaru."

Ya miƙe yana amsa mata.
Ya kalli Abdullahi ganin yadda yake hawaye da kuka har yana sauti.
Ga su Saddam can a tsakar gida suna ta hawaye suma
Kamo Abdullahin ya yi ya miƙar da shi

"Haƙuri za mu yi Abdullahi. Lokacin Baffa ne ya yi ba mu da yadda za mu yi."

Ya faÉ—a yana dafa kafaÉ—an shi alamun lallashi.
Suka fita tsakar gida shima Abdullahi a yarin su Saddam ya bi ya yi zaman dirshan a tsakar gida yana dafe kansa lokaci É—aya yana hawaye.

Ya rasa ma wanda zai fara kira wayarsa ya zaro a cikin aljihu ya ga Ummu Sulaim ta kira shi ganin yadda ya fita hankali tashe shi ya sa ta damu.

Bai kira ta ba, sai da ya kira wayar Baffa Umaru bai same shi ba sai ya kira na Baffa Salihu shi ya sama bayan sun gaisa tun kafin ma ya sanar da shi abin da ke faruwa ya ce ba lafiya tunda ya ga kiran shi da sassafe haka nan ya sanar da shi Baffa lokaci ya yi.

Baffa Salihu ya ja salati ya dire.

"Hadi ya rasu Abdulrrahaman?

"Wallahi Baffa sa'i ya yi."

"Allahu akbar., ciwo ya yi ne ba mu sani ba?

"Ba ciwo Lafiyan shi kalau jiya har sha biyun dare muna tare da shi. Lokaci ne kawai ya yi "

"Allahu akbar. Allah ya jikan Hadi Allah ya yi masa rahama."

Ya amsa da Amin yana faÉ—a masa ya kira wayar Baffa Umaru bai same shi ba ya sanar da su Baffa lokaci ya yi Baffa Salihu ya ce yanzu kuwa tunda kuma rasuwar ta dare ce sai yanzu kowa zai sani a sanya jana'izar zuwa sha É—aya na safe haka kafin nan kowa ya iso Hamma Abdurrahama ya amsa masa da to.
Suna ma cikin wayar Ummu Sulain na ta sake kiran shi.

Sai da suka gama wayar ya kira ta tana tambayan shi me ya faru ya ce kawai ta rufe gida ta É—auko yara su samu adaidaita su taho gida.

"Me ya faru?

"Baffa ne Allah ya yi ma rasuwa.'

Ta ja salati bai bari ta ƙarisa ba ya kashe wayarsa.
Ya juya yana yi ma su Abdullahi nasihan su daina kuka addu'a kawai Baffa ke bukata.

"Abdullahi ka yi haƙuri, yanzu mu tsara yadda za mu isar da Baffa gidansa na gaskiya."

Cewa ya yi Abdulrahim ya je ya faÉ—a ma limamin masallacin da su Baffa ke salla nan kusa da su ne, ya tashi yana goge hawayensa ya zura takalmin shi ya fita Saddam dai ko motsi.
Dakin Baffa suka koma dukkansu biyu suka durƙusa gaban Ammah.
Abdulrahaman na faÉ—a mata ya samu Baffa Salihu a waya ya faÉ—a musu ya ce suna tafe yanzu.

"Ku kira Fatima, kar ku faÉ—a mata kai tsaye ku yi magana da mijinta."

Hamma Abdullahi ya ce bari ya kira Daddy.

"Abdulrahaman ki kira su Balki ku faÉ—a musu, sannan ka kira LamiÉ—o."

Ta yi shuru tana saukar da numfashi.

"Kar ku faÉ—a ma Auta tana da juna biyu, za ta iya shiga hatsari ku kira su Jibo su sanar da su, su taho da wuri a sallaci Baffa a sada shi da gidan shi na gaskiya"

Ya amsa mata da to, tsakar gida ya fita ya fara kiran Hamma Jibo.
Shi kuma Hamma Abdullahi ya kira Daddy ya sanar da shi ya ce yana Abuja amma zai kira Mami ya sa ta samu jirgin da za ta taho Adamawa cikin dubara ba tare da ta san abin da ya faru ba.
Received at 09:09Reactions:
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Cikin lokaci kaÉ—an labarin rasuwar Baba ta zagaya kunnuwan dangi na kusa da na nesa.
Ammah da kanta ta kira Ummin ikki ta faÉ—a mata Baffa lokaci ya yi.
Su Adda Suwaiba ne kaÉ—ai suka riga ta zuwa sai liman sai gata tare da su BaÉ—É—o da babansu.

Ammah falonta ta koma aka bar ma mazan nan É—akin Baffa. Su Hamma Jibo haka suka ji mutuwar Baffa kamar saukan aradu kowa ma sai ya ce wai ya yi ciwo ne.? A ce ba ciwo ajali ne ya yi kira.
Chapter 3 · 0% Book details