← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 75

Sashe 22

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

An yi mata cheekup, babu wata matsala mikin ta ma yana warkewa B.P É—inta ne dai ya yi sama likita na ba ta shawaran ta daina tunani sannan ta dinga samun ishashen barci, kuma da gaske ne a kwanakin ba ta samun barci sosai ya sake rubuta wasu magungunar suka siya a cikin asibitin kafin su tafi, da ATM É—in ta, ta yi amfani na Hamma Lamido ba ta taho da shi ba, ba shi kan shi ba duk abin da ya danganceta haushin shi take ji.

Daga asibitin ma tasha Saddam ya wuce suka karɓo saƙo kaya ne mai yawa har na mota Mami ta biya. Baiwar Allah tana son ta, so mara algus Ubangiji ne kawai zai saka mata.
Sai da suka koma gida ta kira Mami a waya ta faɗa mata saƙon ya iso.

"To sai ki fara amfani da shi ai na san jinin ya É—auke ko?
Mamin ta san jinin ya É—auke tun sati biyu da haihuwar, amma take sake tambayata ta ji kunya ta kasa amsa mata.

"Kina da lambar mai mganin ko? Ki yi mata bayanin ke ce mai wannan saƙon ta yi miki bayanin yadda zaki yi amfanin da komai."
Received at 11:37Reactions: ❤ 6, 👍 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta amsa da to, domin ba za ta yi gaddama ba.
Amma yadda Harira ta shigo da ledan ta tura ta can bayan gado ba ta ƙara ma kallon su ba, ballatana ta yi tunanin cire su daga cikin ledan.
Ita abin da ke gabanta ta ga É—iyarta ta dawo ga shi yau sati amma shuru har wajen yamma ba su dawo da ita ba.

*

Ta damu matuƙa ta ga kuma ba wanda ya damu a gidan
Ammah ce da Umma Balki ta san tana yi musu magana sai faɗa ya dawo sabo daman daƙyar ta samu Ammah ta fara amsa gaisuwanta cikin sakewa.
Bayan ta sake ba ta haƙuri ta nuna nadamarta.

Itama dai daga karshe cewa ta yi ta kira ɗan gold ta ba shi haƙuri ta yanka ƙarya ta ce tuni sun yi magana ma an wuce wajen ahalin tunda ya kira ta ba ta ɗauka ba. Bai sake kiran wayarta ba, itama daman ba niyar nemansa a zuciyarta

Har bayan mangariba shuru haƙurinta ya gama ƙarewa za ta fita ta je har gidan su Habib ai ta san gidan a anguwan Doubeli ne, ko mai zai faru in dai ta dawo da Hanan sai ya faru daga baya.

Ta yi tunanin tafiya ita kaÉ—ai sai ta ga ba mafita ba ne. Ta kira BaÉ—É—o ita ta ma manta wai suna fushi da juna ne, kamar BaÉ—É—o ma ba za ta amsa wayar ba sai da ta kusa katsewa sannan ta É—aga wayar tana amsa mata magana a ciki a ciki.

Tana kan darduma ne daman bayan ta idar da sallar mangariba

"BaÉ—É—o za ki iya zuwa gida yanzu?

"Me zan yi miki?
Ta amsa mata a yangance

"Raka ni za ki yi wani waje."

"Ina kenan?

"Gidan su Habib, zan je na dawo da Hanan ne yau sati É—aya ba su dawo da ita ba kuma na ga ba wanda ya damu ballanta ya yi magana."

"Mtsewww
Ba zan je ba, ki je ke kaÉ—ai."

Daga haka BaÉ—É—o ta katse wayar ta bar Ummu Salma bakinta a buÉ—e sai a lokacin ta tuna sun rabu ba daÉ—i yau sati É—aya kenan, idanuwanta ya rufe ta ma manta da wannan da ta tuna ba za ta kira ta ba

"Ai zan iya zuwa ni kaÉ—ai."

Ta faɗa a fili tana mikewa tsaye darduman da ta yi salla ta ninke, ta ɗau karamar jakarta a saman madubi ta ɗauki kuɗi duk wanda ya tambayeta za ta faɗa masa in da za ta je ba amfanin kuma ɓoye ɓoye.

Hijabin jikinta take sauyawa, ta É—auko gogagge a cikin wardrope.
Ta ji ana amsa gaisuwa a falo kamar wasa ta ji Ammah na kira sunan Hanan itama ta ji karaÉ—in muryanta.

Da sauri ta nufi falon, tana zuwa ko ta ga Hanan a jikin Ammah sanye da doguwar riga na atamfa ba ma cikin kayanta ba ne har sabon kitso an yi mata ga wata leda a hannunta sannan ga wata teedy na wasa a É—ayan hannun nata.
Umma Balki na ta cewa maraba da Hannatu.
Shamsiya na zaune a ƙasa da hijabi a jikinta gabanta kuma jakar kayan Hanan ɗin ne da suka tafi da ita.

"Hanan. "

Ta kira sunan ta da wani irin farinciki, a muryanta.

Hanan ta juya ganin uwarta, da gudu ta tashi daga jikin Ammah ta nufe ta, da murnan ganinta.
Tana zuwa Ummu Salma ta duka ta É—aga ta sama.

"Hanan sai yau?

Ummu Salma ta tambayeta tana dariyan farinciki dariyan da tun tafiyan Hanan ba ta yi irin shi ba.
Ammah da Umma Balki na bin ta da kallo har da Shamsiya dake ta mirmishi.

"Mahma Anty ta kai ni kiso "

Ta ke faÉ—a tana nuna mata kanta, ta sha cuko duk an bishi da duwatsun yara.

"Abba ya siya mini Baby."

Ta sake faÉ—a tana mata Teddy dake hannunta.

"Anty ta siya mini sweet."

Wannan karon sai da ta nuna Shamsiya sannan ta ciro sweet da yawa daga cikin ledan hannunta. Haushi ya kama Ummu Salma Anty, Shamsiyar ce Anty kenan Habib Abba. Takaici ne kawai ke murkurkusanta amma ganin Hanan sai kamar ana rage mata zafin zuciya.

Cewa kawai ta yi ta gani da fatan ta ce musu ta gode ta É—aga kanta.
Sauketa ta yi ta nufi Ammah tana nuna mata sweet É—in hannunta ta ba ta, Umma Balki ta ce itama a ba ta nata sai ta É—ibo biyu ta ba ta.

"Son kai, na kakarki ya fi nawa yawa."

Ta faɗa tana dungure ma Hanan din kai ta ko maƙale kafaɗa kamar ta san abin da ake yi.
Ammah na mirmishi, Umma Balki na fadin yarinyar nan akwai wayau.

"Sosai kowa fa mamakin wayaun ta yake yi ga zence a bakinta haka Babanta ya ce wayanta ya girmi shekarunta."

Shamsiya ta amsa tana mirmishi.
Ammah ta amsa da cewa Hannan ai akwai magana.

Ummu Salma na tsaye tana jin Shamsiya na ba da haƙurin ba su dawo da Hanan da wuri ba
Received at 11:37
4 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
"A yi haƙuri babanta ne ya ce a ɗan tsaya ya samu kuɗi ya yi mata y'an siyayya."

Kallon ta kawai Umma Salma ke yi in ta ce babanta sai ta ji zuciyarta ta yunkuro.

"Ba komai, ai da yake ma baban nata na nan bai dawo ba. Sai ya dawo ne za su tafi."

Umma Balki ce ke bayar da amsa. Shamsiya ta ce sun gode sosai Habib ya na kofar gida ya ce a miƙa masa godiyar sosai.
Ammah da Umma Balki suka ce ba komai

"Da yake a can Lagos É—in take makaranta amma in sun samu hutu su ka zo za a dinga kawo ta in sha Allahu."

Bakin Shamsiyar har kunne tana ta godiya.
Hanan kuma har ta fita tsakar gida in da Harira ke zaune a saman tabarma.

Ummu Salma ta juya za ta shiga ciki sai Shamsiya ta miƙe ta ce tana son za ta yi magana da ita.
Ko amsa ta ba ta yi ba, ta wuce ciki yanzu kam hankalinta ya kwanta magana kuma babu sauran wata magana a tsakaninsu a yanzu.

"Bita ciki mana."

Umma Balki ta yi ma Shamsiya magana sai ta ɗaga kafa ta bi bayan Ummu Salma har zuwa cikin ɗakin da ta san na Umma Salma ne tun tana budurwa ɗakin da ta kan zo su yini suna hira. Amma yau ɗakin ya zama baƙon ta.

Lokacin da ta shiga Ummu Salma na tsaye a gaban madubi kuÉ—i ta mayar a cikin jakarta sannan ta koma ta zauna a gefen gado ko kallon Shamsiya ba ta yi ba.

Ita kuma a ɗarare take, ta kasa zama tana tsaye daga jikin ƙofar ɗakin.

"Umma Salma."

Ta kira sunanta a sanyaye.

Ta kalleta amma ba ta amsa ba.

"Daman ina so na sake ba ki haƙuri kan abubuwan da suka faru a baya ne."

Sai ta É—an dakata ta jan fasali tare da kallon yanayin Ummu Salman.

"Don Allah ki yi haƙuri ki manta baya, Hanan ta riga ta haɗa mu ba yadda muka iya."

Wani kallo Ummu Salma ta watsa mata amma ba ta yi magana ba.

"Ba don ni ba don Allah, ki yi ma Hanan kara ki ba ni lambar wayarki "

"Saboda mene? Na ce na yafe ba buƙatar haka."

Ummu Salma ta faÉ—a tana kallon ta.

"Akwai bukata mana, saboda mu dinga gaisuwa da ke da Hanan gabaÉ—aya."

"Don Allah."

Yadda take yi mata magiya ya sa taka sa musa mata.
Ta fara karanto mata lambar Shamsiya na lodawa a cikin wayarta.

"Na gode sosai."

Ta faÉ—a hawaye na taruwa a cikin kwarmin idanuwanta.

"Ko da ba za mu koma da amintar mu ba. Don Allah ki daina jin haushina."

Ta kalleta amma ba ta yi magana ba.

"Zaman Hanan tare da mu na kwana bakwai kamar shekara bakwai ne a wajen mu, ta wanzar mana da farinciki sosai yan'uwa sun ganta kowa ya yi murna. Habib na son yara an jarabesa nima ina son na haihu ga shi da kamar wuya tunda ko na samu cikin baya kai labari yake ɓarewa."

Ta gama faÉ—a tana sharan kwalla.

"Don girma Allah kar ki yi mana katanga tsakanimmu da Hanan, har abada taki ce ba wanda zai raba ki da ita. Amma muma ki yi mana alfarman aron ta na wani lokaci duk sadda damar haka ya zo"

Ummu Salma ta kalleta yadda take hawaye sai ta ba ta tausayi.
Ta san ya zafin ka É—auki ciki ka rasa shi yake.

"Ba damuwa."

Yadda Shamsiya ke yi mata godiya kamar ta ba ta duniya.
Nan take ta kira ta a waya sai ga lambar Shamsiyar ta fito ita ce dai lambarta tun na baya tana ganin lambobin ta gane sun yi amimta har ya sa ta haddace lambar Shamsiyar a lokacin baya.

"Ga lambata nan ki yi saving don Allah."
Chapter 22 · 0% Book details