← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 75

Sashe 23

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummu Salma ta ce za ta yi, Shamsiya ta yi mata sallama da cewa za ta tafi Habib na can kofar gida yana jiran ta.

"Ki gaida gida."

Kawai Ummu Salma ta iya cewa.
Sai Shamsiya ta É—an waiwaya tana kallonta.

"Habib ya ce na sake ba ki haƙuru."

"Ya wuce"

"Mun gode sosai."

Har ta juya za ta fita Ummu Salma ta kira sunanta.
Ta juyo tana amsawa.

"Ke ma Allah ya ba ki haihuwa"

"Amin na gode sosai."
Ta amsa hawaye na kace mata. Da a ce baya za ta dawo da watakila suna nan da ƙawancen su da Ummu Salama amma yanzu abubuwa sun sauya har abada ba za su taɓa komawa kamar baya ba

Haka ta fita falo ta yi ma su Ammah Sallama a tsakar gida ta ga Hanan ta yi mata Bye bye ta ga Harira sai ba ta damu da Shamsiyar don za ta tafi ba haka ta fita tana waigen Hanan kamar ta sake É—aukanta su koma tare

A ƙofar gida ta ga Habib jikin get ɗin in da ta bar shi yana jiran ta.

"Na fito"
Received at 11:37
8 people reacted with ❤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta faÉ—a tana yin gaba ba ta so ya ga tana kuka shi kuma ya riga ya gani.
Bayanta kawai ya bi, shima yana ji kamar ya koma ya É—auko Hanan amma babu daman haka, kwaannta bakwai tare da su amma kamar shekaru haka yake kallon kwanki nan. Kwana bakwai kawai ta shiga ransa yarinyar nan da zai iya ba da komai saboda ya kasance da ita rayuwarsa a cikin kwana bakwai ta yi sauyi mai yawa a cikin kwana bakwai kawai ya tsinci kansa cikin tsananin farinciki.

Hanan ga hira sannan Bakuntar kwana ɗaya zuwa biyu ta yi musu daga nan ta saki jikinta. Shamsiya tana son Hanan ta shiga ranta sai ya ji da yana da iko da ya ba ta rijon Hanan na har abada amma ina ya rasa wannan damar na shi a matsayin shi na uba tun lokacin da ya furta baya son cikin nan yanzu kuma bayan an haifi ciki ba shi hurumin yanke wani hukunci sun gode ma da aka ba su damar sanin akwai Hanan da ba su damar zaman da ta yi da su har na tsawon kwana bakwai amma ji yake yi kamar jiya ne ta zo yau za ta koma ƙunci yake ji a zuciyarsa na kewar Hanan
Haka ma Shamsiya, har suka hau adaidaita ba ta daina kuka ba

Bai ce mata komai ba sai da suka koma gida ta shiga É—aki ta kwanta a saman gado tana ta kuka.

"Cewa suka yi ba za su sake kawo mana ita ba?

"Aa Ammah ta ce in dai suka samu hutu suka zo garin za su kawo ta."

Ta faÉ—a tana share hawayenta.

"To kuma mene ne na kuka? Hakuri za mu yi gabaÉ—aya."

Ya faÉ—a yana zama a gefen gadon.

"Kukan nadama nake yi, da a ce ban ci amanar ƙawata ba da kaddaran rayuwata bai fara ba. Da kana tare da matarka da Hanan har ma da wasu yaran cikin farin ciki. Nima da watakila na yi aurena ina tare da mijina da ya'yana cikin farinciki."

Sai ta ba shi tausayi ya dafa hannunta yana faÉ—in.
"Haka Allah ya so, sai mu yi hakuri mu ce mun gode."

Hawayenta sun ƙi tsayawa shi ke share mata yana lallashinta.
Ce mata yake yi ai mun tuba, tubar mu zai saka Ubangiji ya ba mu abin da muke so
Hanan kuma tana tare damu har abada.

*Janafty*
Received at 11:37Reactions: ❤ 5, 👍 2
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
BaÉ—É—o ma ta daÉ—e ba ta yi fushin ba itama ba ta ga laifin da ta yi mata ba, akan gaskiyanta take ai ta san fushi ta yi domin tun ranar ba ta dawo kuma ba ta kira ta a waya ba, itama ba ta kira ta ba.

Tunda Baffa ya rasu ta rasa jarrinta taurin zuciyarta ya karu ba ta jin taushi taushi, ta san tana da taurin kai a baya amma yanzu ya yi ƙamari tana ji ko za a yi tashin ƙiyama ne ba ta yarda a ce ita ce ke da laifi ba shi ya sa ko kaɗan zuciyarta ba ta rusuna ba.
Wanda zai yi fushi da ita ya daÉ—e bai yi ba.

Tafiyar Hamma Jibo da iyalansa sai gida ya yi shuru.
Hamma Abdullahi daga kai su filin jirgi ma bai dawo ba, Saddam kuma ya fita Hamma Abdulrahim ne kawai muka yana bangaren su.

Harira ta shigo ta gaisheta tana tambayanta ko akwai abin da za ta yi mata, yan zannuwanta da take sawa da dogayen riguna ta ce ta kwashe ta É—an wanke mata. Bayan fitan Hariran ne Mami ta shigo É—akin ta ba ta waya Daddy ne ya yi mata ya jiki suka gaisa shi yake faÉ—a mata ba zai samu zuwa ba tafiya ta kama shi zuwa Lagos amma gobe Mami da su Islam za su bi jirgi su koma Kaduna tunda duk sun koma makaranta.

Bayan sun gama wayar ne ta miƙa ma Mami wayarta.
Ta karɓa tana kallon ta kur kamar tana nazarinta, ita kuma tana kwance ne daman lokacin da Mami ta shigo sai ta ɗan zauna a saman gadon ta cire hijabin jikinta doguwar rigar atamfar dake jikinta ta bayyana kanta akwai hula amma ana ganin gashin ta, a tsefe yake ta so ne in suka zo nan a yi mata kitso to ba kwanciyar hankali, ga rasuwar Baffa ga abin da ya same ta, gashin duk ya yi biji biji.

Mami ta faÉ—a mata cutar da ya kamata, har goggle ta yi na cutar ta yi daga nan ta san tana da sauran kwana a gaba ne, amma cutar tana da hatsari ga mata masu ciki.

"Yaushe ne za ki koma ganin likita?

Mami ta katse shurun da ya gifta a tsakanin su, itama yanzu Ummu Salma ba ta mata hira in ba ita ce ta tsare ta da magana ba.

"Ranar monday ne jibi."

"Kuma ga shi gobe za mu tafi, ke da wa za ku je?

"Ni kaÉ—ai, Harira za ta raka ni."

"BaÉ—É—o fa ko kuma Umma Balki ta raka ki."

Mami ta faÉ—a tana kallonta.

"To."

Kawai ta ce tana kauda kanta.
Ba haushin Mami take ji ba kawai itama ta san tana bayan masu cewa ba ta kyauta ba. E ta san maganganun da ta faɗa ma Ammah ba ta kyauta ba, wannan ta yarda ta kuma karɓi kuskuranta amma a kan maganar Lamiɗo tana da ja akan masu cewa ita ce ta yi masa laifi.

"Ummu Salma."

Mami ta kira sunan ta lokaci ɗaya tana matsawa kusa da ita har tana riƙo hannuwanta.

"ÆŠago ki kalle ni nan."

Ta É—ago idanuwanta tana mai kallon Mami.

"Ki yi haƙuri ki daina damuwa. Baffa addu'a za mu yi ta masa, maganar Hanan kuma ki kwantar da hankali babu wanda ya isa ya karɓe ta daga hannun ki."

Idanuwan Umma Salma suka kawo ƙwalla suka kece mata a saman kumatunta.

"Mami yau kwana huÉ—u amma ba su dawo da Hanan ba."

"Za su dawo da ita, in ma ba su dawo da ita za a je a É—auko ta."

Mami ke share mata hawaye da tafin hannunta.

"Ke da za ku koma Lagos da zaran Muhammadu ya dawo, tare da É—iyar ku za ku koma in sha Allahu.'"

Hankalinta ya É—an kwanta ta tabbata koma me zai faru Mami tana tare da ita.

Ba za ta koma Lagos ba sai Hamma LamiÉ—o ya janye kalamansa in kuma bai janye ba ta rantse da wanda ranta ke hannun shi ba za ta bi shi ta koma ba.
Mami ta sake lallashinta da cewa ta sake zuwa ta samu Ammah ta sake ba ta haƙuri.

"Ko É—azu da safe ma na shiga na gaisheta dakyar ta amsa gaisuwa ta Mami."

"Ki sake zuwa ki ba ta haƙuri abin ne ya dame ta."

"Mami nima fa ba a kyauta mini ba."

"An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya."

Sai kawai ta yi shuru.

"Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne."

"Haka ne."

"To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri."
Ta amsa da to za ta je.

"Shi LamiÉ—on kin kira shi?

"E bai É—auka ba."

Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba.
Kawai sai Mami ta É—au wayarta tana cewa bari ta kira shi.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
*FJ littafin kuɗi ne 1k a manhajar Telegram tura kuɗin karatu ta wannan acct ɗin 9069067488 Opay Jamila Umar shaidar biya ko tuntuɓa ta waɗannan lambobin.*
08032773332
09069067488.

Tunda Hanan ta dawo ranar cikin salama da aminci Ummu Salma ta yi barci har da makara.
Tashin hankalinta daman a ce yau za a raba ta da Hanan amma tunda ta dawo gare ta, sai fargabanta ya ragu abin da ke gabanta kawai Hamma Lamiɗo ya dawo su yi ta ta ƙare.

Ba ta ma san a ranar za su dawo ba sai da suka yi waya da Fulani ta kira ta, domin ta gaisheta da jiki daman lokaci bayan lokaci tana kiran ta a waya. Ita ke faɗa mata Hamma Lamiɗon da Bilkisu suna tafe yau, bayan kuma sun gama wayar wajen bayan azahar Hamma Abdullahi ya zo ya karɓi key din bangaren Bilkisu a hannun Ammah ya ce Lamiɗo ya ce ya karɓi yana jin a gida za su fara sauka.

Tana falo ne a lokacin ta zo É—aukan ruwa ta ji Hamma Abdullahin ya shigo suna magana da Ammah
ÆŠaki ta koma abin ta, gwara ya dawo domin ta san matsayin ta.
Chapter 23 · 0% Book details