← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 75

Sashe 67

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu Mami ta yi ta ce za ta koma ba ta zo da Faruk ba yana gida tare da Daddy, sai ta ce a ba ta Banafsha ta tafi da ita ta yaye ta a can tunda nan in ta ga Ummu Salma tana rigiman nono, Ammah ta ce a barta ta yi wata goma sha biyar sai a yayeta, Mami ta ce aa gwara a yayeta yanzu tunda shekararta É—aya har da wata biyu, kuma lafiyanta lau ba abin da ba ta ci, babu matsala in an yayeta a yanzu.
Received at 08:04Reactions: ❤ 14, 👍 1
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma ta ce bari ta kira Hamma Lamiɗo ta faɗa masa, ta kira shi bai ɗauka ba sai ta tura masa saƙo amma har dare bai kira ba sannan bai ba da amsa ba. Da ta hau whatsApp ta yi masa mgana ta ga ya duba saƙon ta amma bai ce komai ba sai ta yi masa uziri.

Amma har dare shuru kuma washegari Mami za ta koma Kaduna.
Tana É—akin ta na cikin bangaren Ammah Mami ta shigo tana tambayanta yadda suka yi da LamiÉ—on.

"Mami bai kira ni ba, na yi masa saƙo nan ma shuru."

"To ni bari na kira shi na faÉ—a masa."

Mamin ta faɗa tana barin ɗakin, Ummu Salma barci ta yi domin cikin nan cutar barci ya saka mata, ta yi da rana ta yi da safe daran ma ana mangariba za ta fara jin barci sai ta yi da gaske take zama sai ta yi sallar isha'i, ko gajiya da barcin ma ba ta yi amma ta farka sau nawa cikin dare in yunwa ta ƙwaƙuleta.

Yanzu ma sallar ta idar ta ci abinci ta bi lafiyan gado su Hanan suna can bangaren Baɗɗo can suke yi mata hiran, sun yi ma waya da Shamsiya da safe tana tunanin gobe za ta roƙi Hamma Saddam ya kai Hanan gidan babanta ta yi kwana biyu kafin su koma, ba saboda Habib ba ne saboda Shamsiya ce da take son Hanan tana yi mata so kamar ɗiyar cikinta watakila don ba ta samu haihuwa ba ne.

Ba ta san ko Mami sun yi wayar da Hamma LamiÉ—o ba, sai da safe ta ga tana shiri ta ce a haÉ—a mata kayan Banafsha tare za su tafi, sai ta tambayi Mami ko sun yi waya da LamiÉ—o sai ta amsa mata da sun yi magana.
Ba ta kawo tunanin wani abu ba, domin a mganarta ba ta yi tunanin ta yi laifi ba.

A ranar Mami ta koma Kaduna tare da Banafsha, ita murna take yi ba ta yi tunanin in ta tafi ba yanzu za ta dawo ba sannan Ummu Salma ba ta fito ba yaran ma aka hana su, domin kar ta gansu ta yi rigima. Bayan sun tafi itama Hanan Hamma Saddam ya kai ta gidan su Habib tare da su Sultan suka je tunda a mota ne, Hanan ta ce ita kwana É—aya za ta yi gobe a zo a É—auketa Hamma Saddam ya dawo yana faÉ—a ma su Ammah.

"Yarinya ta gaji da zuwa wannan gidan ta ce Uncle ni gobe ka zo ka É—auke ni "

Ya gama faÉ—a yana ta dariya Ammah ma sai da ta yi mirmishi.

"Saboda su Sultan ne, ba ta son barin su ne."

Ammah ta faɗa Amma sai Hamma Saddam ya hau cewa ba saboda haka ba ne, wannan gidan ai suna fama da rayuwa shi bai ma ga amfanin kai Hanan wajen su ba, uban fa ya ce ba ya son cikin me ya sa yanzu kuma zai karɓa.

"Ai ba a canza ma tuwo suna Saddam, Habib shi ne uban Hannatu, kuma in ta je ba laifi ba ne ai ba wajen su take zaune ba, kuma ban da abin ka ma suna komawa kafin su dawo an É—auki lokaci."

Suna cikin maganar ne Ummu Salma ta fito ta tashi daga barcin tana jin yunwa ta zauna a gefen Hamma Saddam tana tambayan Harira.

"Suna can bangaren Aisha."

Wayarta ta koma É—aki ta dauko ta kira BaÉ—É—o tana tambayanta abin da ta dafa, ta ce tuwo ne miyar zogale.

"Bana jin ci, ki ce kawai Harira ta zo ta dafa mini wani abu."

BaÉ—É—o ke faÉ—in me take so sai ta dafa mata anan sai ta ce ta bari kawai Hariran ta yi bayan sun gama waya Ammah ke faÉ—in ga tuwon ma nan da BaÉ—É—o ta kawo da yawa ta É—iba ta ci mana.

"Ammah ni ba tuwo nake so ba."

Ammah ta kalleta amma ba ta yi magana ba.

"Girman ki ne Sarauniyar Daurama, ko talo talo kika ce za ki ci sai a nemo miki."

Ya gama faÉ—a yana dariya Ummu Salma ta daki kafaÉ—an shi tana hararan shi, Ammah na zaune kanzil ba ta sake cewa ba sai da Saddam ke ba da labarin sun yi waya da Hamma LamiÉ—o akan aikinsa ya ce ya jira shi soon, lokacin da ya tura masa VC É—in sa ya ce ya tura Mai martaba mai murabus a wancan lokacin sai jikinsa ya tashi shi yasa aka samu tsaiko amma yanzu za a neme shi in sha Allahu.

"Allah ya amsa Amin."

Ammah ta faÉ—a Ummu Salma da Saddam suka sake amsawa da Amin a tare.
Harira ce ta shigo ɗauke da Junior ta miƙa ma Ammah shi ta yi saurin karɓan shi, tana masa wasa tana kiran shi da maigida na, Saddam na gefe ya ce Ammah yanzu kamar Junior ne ya kwace son da kike yi ma Baffa mu ai ba ma kya maganar mu."
Received at 08:04
12 people reacted with ❤
[6/26, 10:33 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta harare shi ba ta yi magana ba ya koma yana dariya. Ummu Salma na taya shi, kuma gaskiya ya faÉ—a Ammah yadda take son Junior kuma nunawa take kowa na gani ba kunya ba kamar sauran jikokinta da take nuna musu halin ko in kula, amma wannan har goya shi take yi ya yini a wajenta in ba nono zai sha ba, da yake ma ba shi da rigima sosai.

Suna ta gulmanta ƙasa ƙasa ba ta ma san suna yi ba tana ta yi masa wasa, yana bangala dariyansu na yara, Harira kuma ta tafi kitchen Ummu Salma ta ce ta dafa mata indomie ta saka kayan miya amma kar ya yi yaji. Mintina kaɗan ta gama ta kawo mata ba ta ci ita kaɗai ba Beena ta zo ta zauna ta ce za ta ci Sultan kuma ba shi da wannan yana da kamewa kamar baban shi. Beena ce kamar ba ɗiyar Lamiɗo da Bilkisu ba, kamar ɗiyar Ummu Salma shegen surutu da ƙiriniya irin ta irin Hanan shi yasa ta so ta zo ɗaya yanzu ɗin ma tambaya take yi yaushe Hanan za ta dawo Ummu Salma ta ce gobe.

"Mahma ni dai zan je wajen Hanan."

Beena ta faÉ—a tana kallon Ummu Salma.

"Aa ki bari za ta dawo."

"No ni ina so na je za mu yi wasa."

"Ke wannan gidan ai ba za su iya É—aukan nauyinku ke da Hanan ba, madaran da kuke shan tea da ita ma ba za su iya siya ba."

Hamma Saddam ya faÉ—a yana dariya Ammah ta yi masa dakuwa tana ba zai daina ba ko?
"Na daina Amnah in sha Allahu "

"Ba ka dariyan kaddaran wani domin kai ma ba ka san mai gobe za ta haifar ba."

"Haka ne, amma mu dai ba mu cuci kowa ba Ammah, in sha Allahu rayuwarmu za ta cigaba da kyau har ƙarshe."

Ta amsa da Allah ya sa, rigimar Beena na sai ta je wajen Hanan Saddam ne ya É—auke ta suka fita ta girma shekaran ta Bakwai da wattani Hanan ce biyar Sultan kuma yana cikin shekarunsa na goma sha ne shekara mai zai gama primary, Hanan na primary 1 Beena kuma 3.
Da yake yaran yan hutu ne suna cikin daula girman jikinsu ya ɗara shekarunsu ga wayau da iya mgana turanci da labarci kan ya zauna a bakinsu sosai a dangi ma yaran abin sha'awa ne kowa kallon su yake yi, mate ɗin ta ma da suka haɗu wajen renioun ma ta ga suna saka su a status har tambayanta suke yi wai yara nan nata wata makaranta suka yi ne? Ta ce a can Lagos ne, mamakin ƙoƙarin yaran suke gani.

Kowa yanzu neman ta yake yi a rana ba ta san adadin wayar da take amsawa ba, sai dai ta ji ana cewa wane ne kaza na makarantarku ana roƙonta don Allah ta yi saving lamba matan kuma suna ta kamun kafa suna kawo matsalolinsu da cewa in ta fara taimako ta saka sunan su ta ce ba matsala za a yi komai cikin tsari za kuma a ba da tallafin ga waɗanda suka cancanta ne.

Hanan washegari ƙanin Habib ya dawo da ita, sai bayan tafiyan shi ne Shamsiya ta kira ta tana magana dakyar ta ce ba ta da lafiya shi ya sa ba ta zo ba. Ga Hanan nan sun gode sosai. Ummu Salma ta ce ba komai, ta ga an dawo da ita da tsaraban bickit da su minti tana can falo tare da yan'uwanta.
Ta yi mata sannu da jiki, Shamsiyar na tambayar yaushe za su koma!? Ta ce ba ta saka rana ba amma a cikin satin da zai shiga saboda makarantar yara.

"Allah ya maida ke lafiya."

Ummu Salma ta amsa mata da Amin suka yi shuru na wani lokaci.

"Ummu Salma."

Ta kira sunanta ta amsa tana sauraranta.

"Don Allah ki yi haƙuri."

"Ba komai ai na faÉ—a miki ya wuce."

"Habib..'

Ta yi shuru ta kasa faÉ—in maganar da take son faÉ—a.
Ita ko Ummu Salma tuni ta haɗe fuska kamar Shamsiya na ganinta. Ita fa tsanar da ta yi ma Habib ko sunan shi ta ji an kira sai ranta ya ɓaci.

"Ki yafe masa, don Allah."

"Na ce na yafe ba wani abu."

Ta faÉ—a cikin kosawa tana son katse wayar ne ta gaji da jin mgana É—aya.

"To in haka ne ga shi ku gaisa."
Chapter 67 · 0% Book details