← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 75

Sashe 47

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yake yanzu zamani ya kawo mu komai ta waya ake yi, ta email Lamiɗo ya yi magana da asibitin tun bayan da ya yi bincike kan asibitin kuɗi mai kyau a ƙasar in da Ummu Salma za ta haihu da ikon Allah da kuma ƙwarewarsu. Ta Email ɗin ya tura musu duka bayanan Ummu Salma sannan suka ba shi lambar da zai dinga magana da su. hatta booking ɗin komai an gama jiran su kawai ake yi, shi ya tura musu sakon ticket ɗin su da lokacin da za su ta so da kintatan lokacin da za su sauka shi ne kafin su saukan ma suna filin jirgi suna jiran su.

Tun a filin jirgin LamiÉ—o ya tabbatar da Ummu Salma za ta samu kulawa na musamman. Sun taho da gadon marasa lafiya ga wheelchair bayan an É—aura ta daga bakin jirgi zuwa motar asibitin su kuma suka bi su a motar haya har zuwa asibitin.

Garin daman na larabawa ne asibitin ma yawaanci duk labarawan ne duk da akwai turawa asibitin ya haÉ—u haÉ—uwarsa ya wuce a zauna ana rubutawa
Harira baki kawai take saki tana yi ma Allah kirari.

Mami kuma daman ta saba zuwa ta san Egpyt sosai suna yawan zuwa da Daddy sannan lokacin da ta haifi Islam sai da ta yi kusan wattani biyu kafin ta koma Nigeria so Egypt ba baƙo ne ba ne a wajenta.
Lamiɗo ma da bai taɓa zuwa ƙasar ba shi dai daga ƙasar Malaysia sai Saudia Arabia ya taɓa zuwa haka na musamman Malaysia saboda can ya kwashe shekaru sama da huɗu yana karatu, Saudiya kuma ya je sauke farali da Umra bai san sau adadi ba. Sauran ƙasashen kuma aiki ke kai shi daga ruwa sai ruwa ba yawo suke yi a cikin gari ba amma duk da haka ba za ka gan shi ka ce masa baƙo a ƙasar ba saboda iliminsa da wayewa.

Ummu Salma ma wannan ne karon ta na farko. Ita daman Umra kawai ta taɓa zuwa sanadin Daddy da Mami tana da burin zuwa Saudia ta sauke farali tun a baya ballatana yanzu da take son ta je ta roƙa ma Baffa gafara da rahama a wajen Allah. Tabbas Hajji kiran Allah ne ba rashin kuɗi ba ne ya hana ta zuwa Allah ne bai kirata ba.

Suna zuwa asibitin wasu takardu ne kawai Lamiɗo ya cike maganar payment daman tun a Nigeria ya tura musu kuɗaɗen da suka caje su a ƙiyasi dai Ummu Salma za ta iya yin wata ɗaya ƙarƙashin kulawarsu tunda EDD ɗinta tara ga watan November ne sun kuma sauka a asibitin 31 ga watan actober.

A wani ƙayattacen ɗaki na musamman aka ware ma Ummu Salma ga girma ga shi abu abin da babu a cikin ɗakin nan kamar irin ta zo shaƙawata ba haihuwa ba. Babu abin da za ta nema ta rasa. Sannan kafin a shigar da ita sai da suka sanya mata kayan su na asibitin wani fari mai layi layin baƙi, riga da wando masu sakewa ba su kama ta ba, har da irin hulan su na asibitin da takalminsu ga blanket komai anan suka samu
Kuma ba su buƙatar masu jinya su kwana su za su dinga kula da majinyaci sai dai daga safiya zuwa yamma.

Har sun fara duba lafiyarta an yi ma gwaje gwaje domin a fahimci matakin da take har scan na cikin ta sun sake yi mata duk da an turo bayanan ta suna bukatar ganin komai da kansu sun yi tsarin cewa har abincinta su za su tsara da lokacin cin ta lokacin da za yi dinga barci saboda jininta ya yi sama akwai buƙatar ya sauka kafin haihuwar ta zo. Daga ganin wannan asibitin za ka san naira ce ta yi kuka naira mai suna naira miliyoyi da ba za su ƙirgi ba.

LamiÉ—o da Mami har da Harira suna asibitin sai gabda azahar suka tafi Hotel É—in dake kusa da asibitin mai suna NADA HOTEL 3star hotel ne mai kyau hadaÉ—É—e mai hawa hawa ba iyaka.

LamiÉ—o ya yi musu booking É—in É—akuna nan za su zauna sai dai za su dinga zuwa lokacin da asibitin da tsara suna duba Ummu Salma shi yana gama abubuwan da zai yi yana so ya koma saboda ranar friday zai koma bakin aikin shi.
Received at 18:55
Rabi'atu reacted with ❤
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ko da suka baro sun ba ta abinci sun yi mata allura ta fara barci. Akwai wayarta a hannunta za ta dinga amfani da ita amma sun ce ba za su bari ana damunta da hayaniya ba a takaice dai tana under control É—in su ne. Suma an kawo musu abinci mai rai da lafiya bayan sun yi wanka sun yi salla suka ci suka kwanta suna barcin da ba su samu damar yi a jirgi ba.

LamiÉ—o ya so ya kama ma Mami É—akin ta ita kaÉ—ai amma ta ce ba ta son zama ita kaÉ—ai ya kama musu ita da Harira shi kuma umarninta saman muradinsa ne sai ya yi mata yadda take so.

Mai martaba ya daɗe yana faɗa masa Mami ta fi kowa son shi ba ta dai nunawa ne sannan wani lokacin in suna hira da Ummu Salama in ya ce Mami ta fi son ta sai ta ce kara take yi maka. In ya ce Ammah ta fi son shi sai Ummu Salama ta ce kara take yi maka amma ba wacce za ta fi uwa son abin da ta haifa. Ya tabbatar da haka yanzu da suke samun kusanci ya ɗauka a baya duk wani abu da ya shafe sa ne ba ta so har da shi ma sai daga baya ya fahinci tabbas kara take yi ma Ammah da Baffa sai wata darajarta da ƙimarta suka ƙaru wajensa sannan kwanaki ya ji wani wa'azi malamin ya ce ko a bakin kura kake to wajibi ne ka yi ma mahaifiyarka biyayya sai ya zauna ya yi tunanin tun tasowar sa wani biyayya ya yi ma Mami a matsayinta na uwa a gare shi? Ya kasa tunawa shi ya sa yanzu ya gyara biyayya yake yi mata duk da ko a baya yana yi mata biyayya shaƙuwa ce dai a tsakanin su sannan ba sa shiga rayuwar juna amma dalilin Ummu Salma ya sa yanzu zai iya doguwar magana da Mami bai sani ba itama za ta zauna ta yi masa mganganu ba ta sani ba, a hankali dai tazaran rashin shaƙuwar dake tsakaninsu tana ta haɗewa ba tare da sani ba.

Ba za su koma asibiti ba sai da yamma. Yanzu ɗin ma Mami ce ta baro ɗakin su zuwa na shi ta ce ta gaji da kwanciya. Shi kuma daman bai iya barcin ba yana dai kwance yana hutawa bayan ya gama waya da Bilkisu ya sanar da ita sun sauka tunda suna sauka ƙasar ya siya sabon layi ya fara amfani da shi.

Mamin ce ma ta tuna masa ya kira su Ammah ya faɗa musu sun sauka sai ya kira har ya ba ma Mami suka yi magana tana faɗa mata asibitin suna da ƙwarewa da ikon Allah Ummu Salma wannan karon za ta haihu da kanta.

Bayan sun gama waya da Ammah sun jima suna hira da Mami tana faÉ—a masa yadda yanayin asibitin da ya nema sun birge ta kuma daga gani za a samu abin da ake so. Tana faÉ—a masa itama asibitin da ta haifi Islam mai kyau ne sosai sun kula da ita sosai nan take ta shiga nuna masa hotunan a wayan ta, ga lokacin da suka yi hotuna da likitocin larabawa ga Islam tana jaririya gwanin sha'awa Mami ba ruwanta duk hiran da ta zo bakin ta faÉ—a masa take yi, har tana ce masa ta sha wahala an har kusa yi mata C.S Allah ya taimaka ta haihu da kanta. Shekaru sama da ashirin kafin ta haifi Islam dole ta ji jiki.

Wani maganarta na ta ya yi ɗan mirmishi wani kuma ya jinjina kai. Shi dai ba hira yake yi mata ba domin bai iya ba ita ce ke hiranta yana amsa mata in buƙatar hakan ya ta so, to sanin halin shi itama ba ta damu ba. In hira ta yi mata daɗi har dafa kafaɗan shi take yi.
Akwai wani suna da take kiran shi yana yi masa daÉ—i sosai.

Muhammadu ta ke ce masa, ta kan jima ba ta kira shi da LamiÉ—o ba. Ko ta ce ÆŠan Ammah amma in ta kira shi Muhammadu sai zuciyarsa ta yi masa É—umi.

Lokacin salla la'asar ne ya yi, ya sa hiran ta su ta katse. Ta koma É—aki shi kuma ya shirya ya fita masallaci akwai masallaci a cikin hotel É—in tunda duk musulmai ne.
Sai dare suka koma asibiti suka sake duba Ummu Salma ba su daÉ—e ba mintina talatin ne kawai suka ba su, suka ce za ta ci abinci ta kwanta.
Tana ji tana gani suka tafi suka barta har kuka sai da ta yi. Kewa duk ya ishe ta ga kaßaici ita kaɗai ba wanda ta sani sai baƙin fuskokin Nurses da likitoci larabawa.
Ga shi duk a tsorace take gani take yi kamar wannan karon ma haihuwa za ta zo da targaÉ—a kamar ta baya. Sannan ba ta so a sake yankata ta fi so ta haihu da kanta wannan karon yawan yin C.S ga mace na rage mata karfin jiki.
Received at 18:55
[6/26, 10:32 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
lokacin ma ya san Yariman ya zo garin ko shi Mai martaba bai yi zencen da shi ba Fulani ce kawai ta sani kuma ba ta faÉ—a ma kowa ba.

Sannan a daran ya sake haɗa musu wata ganawar ta sirri da malamai da masu iko a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba. Suma tattaunawar ta su ta ɗau tsawon awanni huɗu kafin Mai martaba ya sallame su.

Washegari kuma Mai martaba ya karbi baƙuncin Baban Alkalin kotun musulunci na jihar Katsina Qadi, shima ɗin tattaunawa ce ta sirri, bayan tafiyar shi ya gana da Limamin jumma'a na masallacin cikin fada a daran kuma ya gana da sauran hakimai da dattawan fada.
Chapter 47 · 0% Book details