← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 75

Sashe 4

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Umma Balki suma hankalinsu a tashe suka ce yanzu za su kamo hanya.
LamiÉ—o kuma Abdullahi ya kira shi bai same shi ba sai ya tura masa sako
Kafin ya ga sakon Hamma Kabiru da ya ji labari ya kira shi shidda da mintina Hamsin na safe ya faÉ—a masa
A lokacin ya dawo daga masallaci kenan ya kwanta gefen Ummu Salma da yake yau an yi wa'azi a masallacin ya tsaya ya saurara.
Lokacin da Hamma Kabiru ke faÉ—a masa Babu Baffa sai da ya ji jiri ya kwashe shi.
Tsam ya tashi daga kan gadon ya mike ya fita falo.

Mutuwan ta girgiza shi Baffan da suka yi magana da shi jiya lafiyan shi ƙalau. Ammah kawai yake tunawa daga ita sai Ummu Salama sai Mami waɗanan ukun ya za su ji yau in suka tabbatar da Babu Baffa.

Tashin hankalin shi yadda zai faÉ—a ma Ummu Salma babu Baffa. Ga ta da ciki tana da B.P.
Kansa ya dafe yana kiran sunan Allah.
Wayarsa ya shiga ya nema musu jirgi, har ya amince ma Ummu Salma za su fara biyawa ta Abuja kafin su sauka Adamawa.

Sai ga shi komai ya sauya daman bai nema musu ticket ba. Nan take ya shiga ya nema musu jirgi kuma an yi sa'a akwai wanda zai tashi zuwa Adamawa takwas na safe

Sai bayan ya yi booking sannan ya kira wayar Mai martaba bugu É—aya ana biyu ya É—auka bayan gaisuwa ya shaida masa halin da ake ciki.

"Allahu Akbar."

Mai martaba ya ja kabbara sau uku.

"Allah ya jiƙan Hadi. Ubangiji ya kyautata makwancinsa."

Tambaya ya yi ƙarfe nawa ne za a yi janaizar?

Ya ce sai ya kira ya tabbatar zai faÉ—a masa.
Mai martaba ya ce to ya kira shi ya faÉ—a masa yanzu zai sa a shirya tagawa za su taho in sha Allahu.

Mai martaba ne ya kira Fulani a waya ya sanar da ita tana ta salati nan ma Masarautar tuni labari ya kai ma kowa, Saleem kuma ya shiga group ɗinsu na iyalan Mai martaba ya sanar cewa kawun Yarima Yayar mahaifiyarsa kuma mariƙinsa sannan uban matarsa Allah ya yi masa rasuwa jiya da daddare.
Gimbiya Hadiza ta fara kiran Bilkisu ta faÉ—a mata rasuwan Baffa ta ji mutuwan nan sosai domin wani abu bai taba shiga tsakaninta da Baffa ba sai alherinsa.

Da ta kira Lamiɗo yana waya lokacin da Abdullahi yana jin lokacin da za a yi Jana'iza ya ce sun saka sha ɗaya na safe. Saboda yan nesa su ƙariso, ya ce Ummu Salma ta yi nesa da wayarta tunda duk sun fitar da sanarwan a kafafen sada zumunta Lamiɗo ya ba shi tabbacin zai hana ta ɗaukan wayarta har sai sun iso.

Sai da suka gama waya ne ya kira Bilkisu
Ta tambaye shi ya tabbatar mata.
Nan take ta ce za ta nema musu ticket ita da yara itama za ta taho ya ce suma yanzu shiri za su yi jana'izar ƙarfe sha ɗaya na safe.

"Ciwo ya yi ne Ranka ya daÉ—e?

"Lafiyan ƙalau jiya ma mun yi magana da shi."

"Allah ya jiƙan shi."
Ya amsa da Amin suka yi shuru.

"Ummu Salma ta sani?

"Ban faÉ—a mata ba."

"Kar ka faÉ—a mata akwai hatsari."

Ya amsa da toh, ta na faÉ—a masa ya bari in sun je can kawai ya ce haka yake tunani.
Ba su daÉ—e suna wayar ba suka yi sallama da cewa sai sun haÉ—u a can duk da ba ta son Ummu Salma amma Baffa bai yi mata komai ba ta ji mutuwarsa sannan ta tausaya ma Umma Salma ta san yadda take son Baffan nan na ta sosai.

Mami kuma tana cikin barci wayar Daddy ya tashe ta.
Tunda ta ji ya fara cewa za ta je Adamawa a yau yau É—in nan da safe nan ta watsake.
Ta san ba lafiya ta ce koma me ya faru kawai ya faÉ—a mata ita ba yarinya ba ce za ta iya kula da kanta.

Lokacin da ya faɗa mata Baffa ne ya rasu ya yi mamakin ƙarfin halinta Mami ta yi shuru kamar a mafarki.

"Allah ya jiƙan Baffa. Allah ya yi masa rahama."

Tausayinta ya kama shi ya ji takaicin ba ya kusa. Nan take ya ce ta nemi mota su taho Abuja ya duba babu jirgin da zai taho Abuja zai nema musu jirgin da za su tafi Adamawa daga can Abujan.
Ta ce shike nan bari su shirya.
Received
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Zama ta yi a É—aki ta sha kukanta tun shekaranjiya take jin jikinta ba daÉ—i ashe maraniya za ta zama jiya ne kawai ba su yi magana da Baffa a waya ba. Lafiyan shi lau bai yi ciwo ba amma ajali ya kira shi.

Data ta buÉ—e tana ganin hotunan Baffa da R.I.P a jiki sai ta ji kawai ta sake fashewa da kuka.
Status É—in Hamma Abdulrrahaman ya fi karya mata zuciya.

"Allah ya yi ma mahaifina Alhaji Hadi Baba Rasuwa a jiya da daddare za a yi jana'izar sa yau da misalin sha É—aya na safiyar ranar talata a gidansa dake anguwan Zone3 a garin Jimeta Adamawa."

"Ku yi masa addu'a. Ku nema ma mahaifina gafara."

Ba hoto ya saka ba rubutu ne amma gabaÉ—aya jikinta ya saki. Tana kuka ta fita ta yi magana da Barira.
Tare za su tafi tunda ba ta san yaushe za su dawo ba lokacin da Barira ta ji Baffa ne ya rasu itama ta yi kuka sosai, Islaam ma kuka share shere Faruk har yana birgima ko wanka ba su tsaya sun yi ba, ballatana maganar abinci.
Mami ta kira Hajiya Falmata a waya ta faÉ—a mata.
Ta tausaya mata domin ta san a duniya Mami ba ta da kowa sama da Baffa nan ta yi mata gaisuwa ta ce kafin a yi uku za ta taho.

Rufe gidan suka yi karfe bakwai da wasu mintina Hamisu ya kwashe su a baƙar pradon ɗin Dadduy suka ɗau hanyar Abuja.
Mami tana idanuwanta sun tasa muryanta har ta dishe ta umarci Hamisu da ya yi gudu sosai shi yasa cikin awa biyu da wani abu suka isa Abuja.

Har suka isa Abuja Mami kuka take yi, a filin jirgin suka haÉ—u da Daddy ashe jirgi É—aya za su hau zuwa Adamawa tare da Hamma Jibo da iyalansa.

Jirgin karfe goma ne, A Airport Daddy ya rumgume Mami tana ta kuka yana lallashinta Hamma Jibo bai yi kuka ba amma duk ya yi zururu.

Adda Nauwara ma da su Saudat É—in kukan suke yi
Allahu akbar rai baƙon duniya.
Sai da jirginsu ya É—aga sannan Hamisu ya baro Airport É—in ya kama hanyar komawa Kaduna.

*

Ƙarfe goma da mintina arba'in da takwas su Mami suka iso Adamawa.
Tashar Napep biyu suka yi zuwa gida.

Tun daga farkon layin motoci ne sun cika ga jama'a.
Mai martaba ya iso tun wajen goma tare da Tawagan wakilan Fada, da Saleem da Fulani tare kuma da Gimbiya Shahida da Gimbiya Amratu.

Bilkisu ma ta iso tare da su Sultan da su Sabuwa.
Hamma Mustpha ya iso haka ma Hamma Kabiru.
Mutanen Mubi motoci uku sun iso, daman su Mami ne sai su LamiÉ—o ba su taho ba.
Tuni har an yi ma Baffa wanka an haÉ—a shi sannan an je makabarta an yi hakan kabari
Baffa Umaru ne da su Hamma Mustapha da Hamma Abdulrrahanman da Abudullahi suka yi masa wanka.

Cikin gida tun daga haraba har cikin É—akuna cike yake da jama'a kama daga yan'uwa da mutanen anguwa. Ammah na zaune a falonta da Hijabi Ummin ikki na gefenta tare da su Umma Balki. Kowa da Hijabi a jikinsu masu kuka na yi masu share hawaye na yi.
Zuwan Mami ya rikita falon domin zubewa ta yi a jikin Ammah tana gunjin kuka su Umma Balki ne ke ba ta baki.

"Baffa ya tafi ya bar ni, ni ba marainiya ba ce a baya amma yanzu na zama marainiya."

Har tsakar gida ana jin ihunta. Mai Martaba na cikin É—akin Baffa tare da su Baffa Umaru da su Hamma Mustapha.
Yau ga Mai martaba ga Batula sun haɗu bayan shafe shekaru sama da talatin amma haɗuwar ba ta zama mai daɗi ba. Yana kallonta cikin rawaninsa cikin tausayinta lokacin da ya yi mata gani na ƙarshe tana kuka yanzu ma da ya sake haɗuwa da ita cikin kuka ne
Ƙirjinsa ya dinga suya, yana so ya lallasheta amma kuma ba shi da wannan hurumin yana gani Daddy ya riƙe mata kafaɗu yana lallashinta wanda suka shigo ɗakin tare da su Hamma Jibo.

GabaÉ—ayansu sun zagaye gawan Baffa suna ta yi masa addu'a da fatan dacewa
Allahu akbar ga Baffa kwance ba ya motsi. Jiya fa lafiyan shi ƙalau amma yau ba ya raye. Duniya zencen banza Ubangiji ya sa mu gama lafiya.

Hamma Lamiɗo ake jira da Ummu Salma su kuma sun samu tsaikon jirgi ne sai ƙarfe goma sauran jirgin su ya tashi.
Duk da Umma Salma ba ta sani ba. Amma ta ji a jikinta wani abu mara daÉ—i na faruwa tun da tashi da safe take jin ta wani iri kamar mara lafiya sukuku ba ta da kuzari.
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Barcin da ta koma bayan sallar asuba ta yi wani mafarki ta ga gidansu cike da jama'a ta ga kowa da kowa har mutanen Mubi amma ba ta ga Baffa ba kuma ta kasa faÉ—a ma LamiÉ—o mafarkin da ta yi amma tunda ta farka zuciyarta duk ba daÉ—i hankalinta duk ya koma gida.

LamiÉ—o ya yi dubaran ya É—auke wayarta ya kashe ba tare da ta sani ba, halin da take ciki ne ya sa ba ta ma nemi wayar ba, ba ta cikin yanayi mai daÉ—i
Ko karyawa ba su tsaya sun yi ba ya ce in suka isa can za su karya.

Da shi da Ummu Salma da Hanan da Harira.
James da Baban Adila ya sallame su, rufe gidan za su yi suma su tafi garuruwansu hutun kirisimeti da sabuwar shekara.
Chapter 4 · 0% Book details