Sashe 11
Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannan ko Mami da Baɗɗo da suke kwana da ita ba su taɓa mata maganar abin da ke cikin ta ba. Ita ba yarinya ba ce in abin da ke cikinta na da rai ai za ta gan shi amma tunda ta ji shuru ta saka ma zuciyarta cewa koma me ta haifa shima babu shi kamar Baffa ba ta yi kuka ba amma kuma raɗaɗin dake zuciyarta bawa bai isa ya kwantanta ba.
Sannan ana gobe bakwai É—in rasuwar Baffa ranar da aka buÉ—e wajen da aka yi mata C.S aka yi dressing É—in wajen ba daÉ—ewa LamiÉ—o ya zo shi ya haÉ—a ta da Fulani a waya ta gaisheta.
Ta yi ta tambayanta ba wata matsala dai ko? Ta ce babu sai ɗan abin da ba za a rasa ba. Asibitin babban asibiti ne tunda kuma asibitin kuɗi ne akwai ƙwarrarun ma'aikata suna kula da majiyantan su sosai tun ballatana ita da take matsayin VIP.
Ta faÉ—a ma Fulani kawai yanzu rashin karfin jiki ne sai kuma rashin daÉ—in bakinta an fara ba ta abinci amma ba ta jin taste É—in komai.
Sai kuma sai yawn ciwon kan da ta ke fama da shi ga ciwon mara, ga zafi daga in da aka yanka ta, ta yi ma likitan magana ya ce a hankali komai zai bari saboda C.S É—in da aka yi mata ne. Ita a lokacin haihuwar Hanan an yi mata C.S amma duk ba ta fuskanci wannan matsalolin ba sai yanzu.
Fulani ta yi ta lallashinta da kalamai masu daɗi da nuna mata komai ta ga ya faru da bawa mukaddari ne. Ta yi haƙuri Allah zai ba su wani rayayye tun kafin ta ji daga bakin kowa ta san shima mai sunan Baffa bai zo da rai ba, kuma duk da cikin wattaninsa bakwai ko da ana haihuwar bakwaini su rayu amma ƙarancin hakan ya fi yawa.
Ta amsa ma da Fulani da cewa ba komai haka Allah ya so. Ita kuma Fulani ba ta san ma ba a faÉ—a ma Ummu Salman ba sai da LamiÉ—o ya karbi wayar ya fita daga É—akin yake faÉ—a mata ba su riga sun sanar da ita ba.
"LamiÉ—o Ummu Salma ta san cikin ta bai rayu ba. Ka faÉ—a mata ba domin ba ta sani ba sai domin ka lallasheta."
Shi yana tamtama a ina ta ji? Tunda ba wanda ya faÉ—a mata.
"Uwa ce fa, in da abin da ke cikinta na da rai da ta gan shi zuwa yanzu."
Sai ya aminta da maganar Fulani bayan sun gama waya ya koma É—akin sai ya ga Mami na zaune gefenta tana yi mata magana sannan ga wayar Mamin a hannunta alamun cewa hoton jaririn ta nuna mata
Mami na ganin ya shigo ta mike tana faÉ—in"Na faÉ—a mata, ka zauna ka sake ba ta baki."
Tana gama faɗin haka ta fice, Baɗɗo ta je gida ta dawo daga can za ta ɗauko ma Ummu Salma wasu kayan sawa duk da ba ta fara wanka ba sai dai su goge mata jiki tare da gasawa saboda ba a son ruwa ya taɓa wajen aikin kafin a kwance.
In BaÉ—É—o ta dawo ita Mamin za ta koma gida ta yi wanka, Daddy ya koma Kaduna sai gobe addu'an bakwai zai dawo Hajiya Falmata ma kwanan ta biyu ta koma Kaduna. Su Gimbiya Shahida ma ana yin uku suka koma Daura.
Bayan fitan Mami in da ta tashi ya koma ya zauna wata farar kujera dake gaban gadon da Ummu Salma ke kwance. Ya ƙura mata idanuwana yana so ya fahimci yanayinta.
Hannunta da ba karin ruwa ta riƙe wayar da shi wayar ta ƙura ma idanuwa Lamiɗo ya kasa gane yanayin da ta ke ciki bai ga hawaye ba sannan bai ga tana kuka ba.
Ɗayan hannunta ya kalla na dama in da ake yi mata karin ruwa. Ya ɗan kumbura domin akai akai ake zuwa duba ta tare da kayadde lokacin da za su yi mata allurai da saka mata ƙarin ruwa. Sannan sun fara ba ta kwayoyin maganin tunda ta fara cin abinci. Sannan suna yawan yi mata awon B.P jini akai akai da kuma awon fitsari tunda tana da B.P Sannan ga Eclampsian da ta yi fama da shi lokacin da aka kawo ta.
Miƙa masa wayar ta yi ya karɓa yana kallon ta.
"Kin gan shi?
Ya tambayeta lokaci ɗaya yana ɗan rike hannunta mai ƙarin ruwan
Received at 10:00
13 people reacted with â¤
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ta juyo ta kalle shi ta ɗan gyada masa kai, tunda ta farfaɗo ba ta cika yawan magana ba zai gaisheta za ta amsa amma kuma babu wata doguwar hira a tsakaninsu bai damu ya ɗauka shock ɗin abin da ya faru da ita ne ga kuma rasuwar Baffa a tunanin shi nan gaba kaɗan za ta warware. Abin da bai sani ba Ummu Salma komai na duniyar ne ya daina birgeta har shi kan shi ya daina birgeta yanzu gata nan ne kawai tana raye amma kamar ta mutu. Radaɗin dake zuciyarta kawai zai iya barazanar kashe ta a kwance a in da take. Sannan tunda ta farka take ganin duniyar ba daidai ba, ɗakin ma ganin shi take yi wani lokaci ƙarami, wani lokacin babba, daga nesa in ta ga abu sai ta ga ya canza mata gata nan ne kawai yanayinta gabaɗaya ya canza.
"Ya zo da rai ya kwana É—aya ya rasu."
Ya faÉ—a yana sake kallon hoton daga wayar Mami.
Hamma Kabiru ne ya É—au hoton ranar da suka koma gida yana tunanin shi ya tura ma Mami.
"Allah ya kaddara mai sunan Baffa shima zai zo kuma zai tafi ya bar mu kamar Baffa"
Ya faɗa cikin sanyin murya amma a ƙasan zuciyarsa wani abu ke yi masa motsi rashin wannan jaririn ya dake shi, ba shi kaɗai ba da dukkan dangin su ba wanda bai ji ba daɗi ba.
"Allah ya jikan su. Shi kuma Allah ya sa ya cece mu."
Ummu Salma ta faÉ—a tana É—an kauda kai.
"Amin."
Yana so su haÉ—a idanuwana amma ta ki ba shi damar haka.
"I'm sorry."
Ya gama faÉ—a yana matsa kafafunta da duka hannuwansa duka biyu.
"Allah zai ba mu wani mai sunan baffa in sha Allahu."
Kanta na can gefen ba ta yi magana ba shima shurun kawai ya yi yana É—an matsa mata kafafuwa
Kiran wayarsa ya katse sa daga abin da yake yi, sai ya ga Bilkisu ce ya ɗauka suka gaisa ƙasa ƙasa tana Abuja ranar kwana huɗu da rasuwar Baffa suka tafi tare da yara da su Hidaya amma kafin tafiyarta ta zo har asibiti ta duba Umma Salama lokacin tana barci.
Yanzu ma cewa ta yi ya jikin Ummu Salma ya ce da sauƙi ga shi ma tare da ita.
"How is she? Kun faÉ—a mata?
"Ta sani."
"How is she?
"She is fine, ba ta tada hankalinta kamar yadda na yi tunani ba."
"Allah ya ba ta lafiya."
Bilkisu ta faÉ—a cikin wani yanayi, ba ta son ta amma ta ji tausayinta cutar Eclampsia tana da hatsari sannan ga shi ta rasa jaririnta ga shi ta rasa uba duk a lokaci É—aya in dai kai musulmi ne za ka ji tausayi ko kaÉ—an ne.
Wayar ta ce ya ba ma Ummu Salma ta gaishe ta.
Sai ya miƙe ya isa ta wajen kunnenta ya ƙara mata a kunne yana faɗa mata Bilkisu za ta gaisheta.
Ya riga ya saka mata wayar a kunne ta ji Bilkisu na yi mata sannu ta amsa a sanyaye
"Babu wata matsala ko?
Ta amsa mata da cewa babu
"So ki cire damuwa a ranki, ana so jinin ki ya yi ƙasa sosai in kina so a sallameki ki koma gida"
Ta ce mata toh kawai sannan ta ce Allah ya ƙara mata lafiya ta amsa da Amin
Sultan da Beena suna kusa suna ta cewa a basu wayar sai ta ba su É—aya bayan É—aya suka gaishe da Ummu Salma sai a lokacin ta É—an yi mirmishi kaÉ—an
Bayan ta gama wayar shi ya karɓi wayar yana magana da yaran sai ga likita da wasu nurses sun zo duba ta sai ya fita waje ya ba su wuri suka fara checking ɗinta kamar yadda suka saba a koda yaushe.
A wajen ɗakin ya samu Mami zaune saman wasu kujeren zama dake wajen, sai da suka yi sallama da Bilkisu sannan ya ƙarisa in da Mami ke zaune amma har ya zauna gefenta ba ta sani ba ta zurfafa a tunani.
Sai da ya kira sunan ta sannan ta san da shi a gefenta.
"Ya take? Ina fatan ba ta yi kuka ba?
Wayarta ya miƙa mata ta karɓa.
"Ba ta yi ba."
Shuru suka yi dukkansu na wani lokaci.
"Ka yi haƙuri kai ma. Allah zai ba ku wani in sha Allahu."
Jinjina kai alamun gamsuwa.
"Allah ya sa."
Shuru ya sake wanzuwa a tsakanin su Mami ta kalle shi duk ya rame sai sumar fuska da ya tara daga gani ba shi da natsuwa sai ta dafa kafaÉ—an shi ya juyo yana kallon ta.
"Kana cin abincin kuwa Muhammadu?
"Ina ci."
"Ka kwantar da hankalin ka, Ummu Salma za ta warke ku koma gidanku ku zauna, Allah zai sake ba ku wani rabon da ikon Allah sai kun haifi mai sunan Baffa"
"In sha Allah."
Received at 10:01Reactions: ⤠8, 👠1

Ya amsa mata cikin yaƙini da tabbatarwa. Suna cikin haka ne sai ga Baɗɗo ta dawo tare da Umma Balki.
Zuwan su ya sa Mami ta bi LamiÉ—o zuwa gida su kuma suka zauna a asibitin tare da Ummu Salma wacce ta koma barci.
Haka aka yi addu'ar rasuwar Baffa kwana bakwai Ummu Salma na asibiti. A ranar kwananta biyar kenan a asibiti. Kuma ba su da niyar sallamanta domin a washegari mutanen Mubi da za su koma duk sun zo asibtin duba ta, da su Baffa Salihu shi Baffa Umaru sai an yi sati biyu.