← Book details Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 75

Sashe 21

Fargar Jaji Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mami nima fa ba a kyauta mini ba."

"An ji ke ma ba a kyauta miki ba, amma ke ce ƙarama ke ce ba ki da gaskiya."

Sai kawai ta yi shuru.

"Uwa ce ita, duk wanda zai so ki da cigaban ki bayan ita ne."

"Haka ne."

"To ki sake zuwa ki same ta daga ke sai ita, ki sake ba ta haƙuri."
Ta amsa da to za ta je.

"Shi LamiÉ—on kin kira shi?

"E bai É—auka ba."

Ta yi ma Mamin ƙarya domin ita dai ba za ta kira ba.
Kawai sai Mami ta É—au wayarta tana cewa bari ta kira shi.
Received at 11:37Reactions: ❤ 4, 👍 1, 🔥 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Ummu Salma na zaune ko fargaba ba ta yi domin ta san halin shi ba zai taɓa cewa ba ta kira shi ba a e ɗin shima zai tafi.
Wayar a amsa kuwwa Mami ta saka tana fara ringing ya danna mata busy har tana tunanin ko yana cikin mutane ne sai ga kiran shi ya shigo ta É—aga.

Muryan shi tarai, muryan da kan sanya Ummu Salama kasala da shauƙi a baya ban da yanzu.

Suka gaisa da Mami da tambayan mutanen gida.

"Yaushe za ka dawo?

"Da zarar Mai martaba ya ta shi zuwa London'

Ya amsa mata cikin yanayin maganarsa. Mami ta tambaya da cewa daman bai tafi ba? Sai ya ce sun samu tsaikon Visa ne ta yi fatan alheri.

Suka yi shuru dukkansu ba wanda ya yi magana.
Shi da man ba gwanin É—ago magana ba ne ko da akwai maganganun a bakin shi.

"ÆŠiyata ta ce ta kira ka, ba ka É—auka ba?

Sai ya yi shuru kamar bai ji ba sai da Mami ta sake maimaitawa.

"Ban lura da kiran na ta ba Mami."

Ya amsa kai tsaye amma a ƙasan zuciyarsa yana tunanin ko lokacin haihuwar nan Ummu Salama ta samu natsala ne? Shi dai yana ganin she is not okay.

"To ta kira ka ne ta ba ka hakuri kowa a gida ya ce ba ta kyauta ba. Amma kai ma ba zan fasa faɗa maka ba ka kyauta ba koma me ya faru ai ka duba yanayinta lallashi take buƙata ba faɗa ba."

"Mami."

Ya kira sunanta ta amsa.

"Ni cikin ɓacin rai na yi maganar da na yi, amma Mami Ummu Salama ta kyauta mganganun da ta faɗa ma Ammah? Ta kyauta abin da ta yi?

Ya faɗa a jere daga ji yana ƙokarin sarrafa fushinsa ne

"Ba ta kyauta ba, kowa ma ya faɗa mata kuma ta karɓi laifinta kuma har ta ba ta hakuri ma."

Ya yi shuru kawai bai yi magana ba.

"Kai ma sai ka yi haƙuri, kai ne babba. Ka lallasheta domin tana bukatar hakan."

"I will."

"Amma ni ma mganganun da ta faÉ—a mini ta kyauta?

"Ba ta kyauta ba, za ta ba ka hakuri."

"Better."

Ummu Salma na zaune haushi duk ya isheta har wani better ya ke faɗi tunda an ce za ta ba shi haƙuri to ya cigaba da jira.
Maganar komawarta asibiti Mami ta yi masa ya ce zai kira Ummu Salman za su yi magana ya tambayi ko an dawo da Hanan?

"Ba su dawo da ita ba, in ba su dawo ba za a je a karɓota ai kana dawowa za ku koma Lagos ɗin ko?

Ya amsa da in sha Alllahu ya kara da cewa shima hutunsa ya kare ga yara ma sun koma makaranta.

"Bilkisun fa?

"Tana nan tare da ni."

Ya amsa ma Mami, sannan ya cigaba da faÉ—a mata daman bayan sun gama biki a garin Abuja Kano ta koma, daga Kanon ne jiya ta zo Daura ta same shi gabaÉ—ayansu tare za su taho nan Adamawa.

Yanzu akwai sakin jiki tsakanin LamiÉ—o da Mami, sai su É—au lokaci suna magana a waya ma ba su sani ba.
Ummu Salma kuma haushi ya turniƙeta, wato ma matarshi na can tare da shi, ita ce ya gasa ma maganganu ya yi tafiyarsa.

Ta ɗauka Mami za ta yanke wayarta ne amma kawai sai ta ga ta miƙa mata tana ce masa ga Ummu Salma ma su yi magana ta karɓa saboda Mami ce, a gabanta ta yi masa sallama ya amsa a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba.

Allah ya taimaketa Mami ta ba su waje, tana fita ko ta yi zaraf ta kashe wayar, saboda ma an ce za ta ba shi hakuri dakyar yake amsa sallamanta.
Ya sake kiran wayar Mami ta ƙi ɗauka baya nan itama ya kirata sau biyu a wayarta ma ba ta ɗauka ba sai hararan wayar take yi tana sakin tsaki ita kaɗai.

Can ba jimawa sai ga saƙon shi.

"Umma Salama."

"Pick the Call."

Ko buɗe sakon ba ta yi ba ta sreen ɗin wayarta ta hango shi kuma ba ta ɗauka ba ko da ya sake kira sau ɗaya daga nan kuma bai ƙara kira ba.

Mami na dawowa ta miƙa mata wayarta ta yi mata ya ce zai kira wayarta su yi magana.

"Yauwa ko ke fa, yanzu maganar kayan gyara za mu yi bari na kira Hajiya Falmata na ji yadda za mu yi"

Da za ta iya da ta ce ma Mami kar ta ba kanta wahala. Ita ta daina yi ma namiji wannan rawan jikin duk ba yan goyo ba ne halin su saya. Nan jaririn Hamma Lamiɗo ne a cikinta wajen haihuwansa ta kusa mutuwa amma bai damu da ita ba har a yanayin yake cewa zai sake ta maza yan kutumar uba ne, ta yadda da maganar hausawa da suke cewa namiji ƙañin ajali. Namiji hankaka gabansa fari bayansa baki, namiji dafin shi ya fi dafin kunama namiji kuma ba ɗan goyo ba ne.
Received at 11:37Reactions: ❤ 7, 👎 1, 👏 1
[6/26, 10:31 AM] +234 706 064 8502: Janaftybaby
Lokacin da ta auri Habib tana ganin za ta goya namiji, sai ga shi da ta goyasa ga tozarcin da ya biyo baya, a lokacin tana ganin ta gama bama wani namiji yarda amma Hamma Lamiɗo ya mantar da ita wannan har take ganin namiji ɗan goyo ne sai da ya yi mata wannan abin ta fahimci shegu duk halin su ɗaya ta ɗauko ko a cikin maye ba zai iya cewa zai sake ta ba. Kalamansa sun munana a wajenta, tunda kuma ya furta an ce magana zarar buni ce ta fita ba halin ta koma. Tunda maganar nan ta fito daga bakinsa shike nan take ganin baƙin sa.

Tana jin Mami ta kira Hajiya Falmata suka gama magana.
Tana faÉ—a mata za ta siya mata babban package na maganin sanyi, da na haÉ—in maijgo a wajen Surayya Halin yau 080322773332
Bojuwa zuwa jibi sako zai iso ta fara amfani da shi kafin su koma Lagos, ta cinye kaza da ciccibinta anan da kayan sanyi, na garin kuma ta tafi da su.

Ta amsa da to kawai, amma a zuciyarta ta ce ba za ta ci ba ko da an kawo. Domin ita a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya yin wani abu da sunan wani gyara ba. Lafiyanta take nema da tunanin ma za ta sake É—aukan cikin? Ko kuma a wannan karon za ta haihuwa lafiya?ga shi dai an yankata sau biyu a waje É—aya bawa bai isa ya guje ma kaddaransa ba.

Tana tunanin haka sai wata zuciyar ta ce kin manta kin ce ba za ki koma ba? Sai kuma ta amsa ma da kanta za ta koma in dai ya fara yin nadaman kalamansa ya bata haƙuri kuma ya janye su za ta iya yi masa afuwa ta bi shi su koma tare amma in dai bai yi haka ba sai dai kowa ya ga baƙinta ba za ta koma ba.

Ba ta furta ma kowa abin da ke zuciyarta ba. Amma za ta aiwatar da kudrinta sai dai a kore ta a gidan tunda ta fahimci kowa Hamma LamiÉ—o yake goyon baya.

Washegari ma kafin tafiyarsu Mami haka ta yi ta mata faÉ—a, ta daina damuwa saboda halin da take ciki ta ce za ta daina.

Tafiyar Mami sai ya kara sa gidan ya zama shuru ba Faruk ba Islam.
Duk da Mamin ta ce za ta dawo nan ba da jimawa ba.

Mami na tafiya ko sauka ma ba su yi baa direba ya kirata tana da saƙo daga Kano. Ta san saƙon maganin nan ne sai kawai ta tura masa lambar Saddam, ta ce Direban ya kira shi zai karban mata saƙon in sun shigo gari.

Da yamma da Saddam ya shigo gidan yake tambayanta tana da sako ne daga Kano am kira shi ta ce e na ta ne.
Gida ya yi tsit Allahu Akbar babu Baffa ba ta ma san fita tsakar gida saboda sai ta ga kamar za ta gan shi ya fito daga cikin ɗakin shi, ɗakin ma yana kulle ne Ammah ma ba ta son shiga, wataƙila yana tuna mata da Baffa ne.

Ba su da matsalan komai, kayan abinci a store sai ya shekara, kafin tafiyan su Hamma sun ajiye komai, ko ruwa katan katan ne ba adadi ga lemu, sun yi cefane ga kudi masu yawa da suka bari har gobe ma kuɗin da Masarautar Daura ta ba da ko rabi ba a taɓa ba

Daddy ma ya ba da kuÉ—i mai yawa, haka ma Mami da za ta tafi. Baffa ne kaÉ—ai suka yi rashi amma komai na rayuwa babu abin da babu shi a gidan nan amma gidan kowa ka gani babu karsashi.
Harira ita ke taimaka ma Umma Balki da wasu ayyuka tunda tana da ƙokari sosai.

Ranar monday da safe ita da Harira suka tafi asibiti. Hamma Saddam ya kai su, Hamma Abdulrahim ya tafi wajen aiki.
Chapter 21 · 0% Book details